TAMBAYA (83)❓
Aslm Allah ya kar6i aikin malam Dan Allah tambaya ta shine inada budurwa hartaki an kai ga samin Rana sai Na ga wata taburgeni shin zan iya zuwa zance wurinta kokuma saidai bayan bikin nawa ya halarta nasake kula wata
AMSA❗
Waalaikumussalam warahmatullahi
wabarakatuhum
Alhamdulillah
Idan na fahimce ka, kanada
ra'ayin auren mace sama da daya saboda wani dalili na kashin kanka. Hakan koyi
da Sunnah ne amman fa in kayi da kyakkyawar niyya sannan kuma idan kanada ikon
yin adalci garesu
Idan kyau ne silar da tasa ka
kula waccan sabuwar budurwar to ka sani a kullum za ka yi ta kule kulen yan
mata ne, domin kuwa kyawawa dai kam in har kullum zaka fita to sai ka gaji da
ganinsu
Hanzarin me kake. Ba kyau yin
gaggawa a cikin al'amura. Sannu sannu bata hana zuwa. Idan kanada ra'ayin auren
mata biyu a lokaci guda wannan ba laifi bane ba indai har kanada sana'ar da
zaka iya kulawa da su. To amman tunda an saka maka rana ka tsaya mana ka san
abinda ya kamata kayi wajen shirye shiryen ganin komai ya tafi yanda ya kamata
Sannan kuma yawan zuwa zance yana
iya bude kofar barna. Abinda yake a shari'ah shine: idan ka ga mace ta kwanta
maka a ranka. To kada ka bi son ranka, a'a, ka tattara al'amarin ka miqa shi
zuwa ga Allah Azzawajallah ta hanyar yin addu'ar da Annabi Sallallahu alaihi
wasallam ya koyar damu wato addu'ar Istikhara. Ka fara bawa Allah zabi tukunna.
Idan akwai alkhairi zaka gani akasin haka ma zaka gani. Sannan kuma sai ka
bincike halayenta da alaqar ta da iyayenta. Ka fara duba yaya halin mahaifiyar
ta yake, ya take biyayya ga mijinta. Saboda ai da na gaba ake gane zurfin ruwa.
Dabi'un mahaifiya suna da matuqar tasiri wajen gane halayen yayanta musamman
mata. Sannan sai ka tura waliyyanka suyi magana gemu da gemu. Kafin wani late
comer yazo ya kasa ka, azo ana ta dana sani, da hausawa kan kira ta da keya.
Daganan sai kuje asibiti ayi muku test saboda kada aje soyayya ta yi dadi azo
ace ai waninku yanada cuta iri kaza da kaza, maganin kar ayi kar a fara. To
ammanfa duk da haka kowacce cuta saidai Allah ash-Shafi' ya saukarda maganinta
tun ma kafin ya halicci cutar
Ka ci gaba da miqawa Allah
zabinSa akan neman auren ta farkon saboda kada kaje ka saki reshe ka kama
mujiya, aje ayi ba wan ba kanin, ma'ana garin neman gira ka rasa ido, kai baka
auri ta farkon ba kuma idan ta tabbatar da kana zuwa wajen wata zance, abinda
zai fara zuwa ran ta shine; zan auri miji mai yaudara, mai kule kulen yan mata
Wasu mazajen suna kafa hujja da
ai namiji mijin mace 4 ne, eh wannan haka yake amman indai zai iya adalci a
tsakaninsu ba (Kamar yanda hakan ya tabbata a cikin Qur'ani Mai girma)
Idan waccan baiwar Allah din ta
tabbatar da halinka na yawan kule-kulen yan mata to gaskiya kimar ka zata zube
a idanunta. To don gudun hakan ta faru, gwara ka riqe dahir ka saki gaibu
Wannan shine yar taqaitacciyar
shawarata a gareka. Sannan kuma a karshe zanso ka shiga makarantar koyar da
rayuwar auratayya a musulunci bisa koyarwar sunnar Annabi Sallallahu alaihi
wasallam. Karanta littafin "Guidelines To Intimacy in Islam" zai
taimaka matuqa da kuma littafin "Rijali Haular Rasul"
Ina roqon Allah ya yi maka zabin
alkhairi
Masu aure kuma, Allah ya basu
ikon cin jarabawar haqurin zamantakewa. Gwauraye kuma Allah ya kawo manema
nagari
Wallahu ta'ala a'alam
Amsawa:
Usman Danliti Mato
(Usmannoor_Assalafy
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.