Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Mai Azumi Zai Iya Sumbaci (Kissing) Matarsa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam dan Alllah idan miji ya sumbaci matar sa da azumi shin haka zai iya ɓata azumin su ko ba zai iyaba. Na gode

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Zance mafi inganci shi ne ya halatta ga mai azumi ya sumbaci (kissing) ɗin matarsa, amma da sharaɗin idan za su iya control ɗin sha'awarsu ta yadda hakan ba ze sa su yi jima'i ba ko maniyyi ya fita.

An karbo hadisi daga Aisha (r.a) ta ce: “Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya kasance yana sumbanta alhali yana azumi, kuma yana runguma alhali yana azumi, amma shi ya fi ku mallakan sha'awarsa”. Bukhary da Muslim.

Wannan hadisin na nuna mana: Halas ne mutum ya rungumi ko sumbanci (kissing) ɗin iyalinsa a cikin watan Ramadan matukar zai iya kare kansa daga jima'i ko fitar da maniyyi.

Runguma da sumbanta ya halatta, amma ba jima'i ba.

Wanda ya sumbanci matarsa kuma maniyyinsa ya fita, to azuminsa ya lalace, kuma zai kame bakinsa daga ci da sha har sai rana ta faɗi, kuma zai rama azumin, bayan ya nemi gafarar Allah da tuba zuwa gare Shi.

Amma idan madziyyi ne kawai ya fita, to azuminsa bai lalace ba kamar yadda mafi yawan malamai suka yi bayani.

Don haka, sumbanta na iya karya azumin mutum matukar maniyyinsa ya fita.

WALLAHU A'ALAM.

🏿Ayyoub Mouser Giwa.ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments