𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum, miji ne ya je saduwa da matarsa sai ya
kuskure ya saka mata a dubura, shin menene hukuncinsa?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumus salam, in har da kuskure yayi hakan, sai yayi
sauri ya zare, mutukar ya cire daga zarar ya ji ba wurin bane Allah ba zai kama
shi da laifin hakan ba. A ƙarshen Suratul Bakara
رَبَّنَا
لَا تُؤَاخِذْنَا إِن نَّسِينَا أَوْ أَخْطَأْنَا
"Ya Ubangijinmu
kar ka kamamu in mun manta ko mun yi kuskure". Muslim ya rawaito hadisi
cewa: Allah ya zartar da hakan.
Ibnu-Maajah ya rawaito hadisi, Annabi (Sallallahu alaihi
Wasallam) yana cewa: "Allah ya yafewa al'ummata abinda suka aikata cikin kuskure".
Ci gaba da jin daɗi
a wurin bayan gano kuskuren, yana daga cikin zunubai.
Allah ne mafi sani.
Amsa daga Dr. Jamilu Yusuf Zarewa.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.