Ticker

6/recent/ticker-posts

Ya Yaga Takardar Saki Kafin Matarsa Ta Gani

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Malam Shin Idan mutum ya rubuta takardar saki sai ya yaga takardar sakin kafin matarsa ta gani, shin matar ta shi ta saku?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam To malam matukar ya rubuta da niyya kuma yana cikin hayyacinsa ba takura masa aka yi ba, to ta saku, saboda faɗin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: "Allah ya yafewa al'umata abin da ta riya a zuciyarta, mutukar bata fada ba, ko ta aikata" ka ga kuma rubutu aiki ne.

Kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana zartar da abubuwa da yawa ta hanyar rubutu, ka ga ya zama hujja ke nan.

Wannan shi ne mazahar Abu-hanifa da Malik kuma shi ne zancen Shafi'i mafi inganci. Duba Al-mugni: 7\486

Allah ne mafi sani

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments