Ticker

6/recent/ticker-posts

Muhimman Sakonnin Zauren WhatsApp Na Taron Kara Wa Juna Sani Na Kasa Da Kasa Kan Makada Sa'idu Faru

Wannan shafi yana ɗauke ne da muhimman saƙonnin da ake turawa cikin zauren WhatsApp na Taron Ƙara Wa Juna Sani Na Ƙasa Da Ƙasa Kan Makaɗa Sa'idu Faru, shiryawar Sashen Nazarin Harsunan da Al'adu, Jami'ar Tarayya Gusau, Nijeriya.

Domin karanta cikakken bayani game da taron, a danna NAN.

To access these updates in English, click HERE.

Sanarwa ta 003

Muna farin cikin sanar da manyan malamanmu da sauran manazarta masu daraja cewa, nan ba da jimawa ba za mu turo jerin ƙananan batutuwan da za a iya rubutu a kansu dangane da wannan taro.

Domin ba da wa mambobin zauren damar karantawa, za mu ɗan kulle zauren na lokaci kaɗan (yadda ba za a iya turo saƙonni ba). Manufar hakan ita ce ta ba wa saƙon damar kasancewa na ƙarshe a cikin zauren. Hakan zai sa mutane da dama su samu damar karanta shi.

Kada a manta da cewa, a koyaushe za a iya karanta cikakken bayani game da taron a nan: https://www.amsoshi.com/2024/01/an-international-conference-on-life-and.html

Su kuwa muhimman bayanai da muke turowa cikin wannan zauren, za a iya karanta su a nan: https://www.amsoshi.com/2024/02/makaa-saidu-faru-conference-update-page.html

Kada kuma a manta da cewa, ana iya turo mana shawarwari da ƙorafi a keɓance ta;

📌Email: delac@fugusau.edu.ng

📌WhatsApp: +2347062052814

Mun gode matuƙa.

*****

Sanarwa ta 004: Jerin Batutuwa

Muna farin cikin sanar da malamanmu da sauran manazarta da abokan ha ɗin guiwa cewa, Kwamitin Lura da Fannin Ilimi na wannan taro ya fitar da jerin batutuwa da za a iya rubutu a kansu. An raba waɗannan batutuwa zuwa manyan rukunoni guda uku, wanda kowane rukuni yana tafe da ƙananan batutuwa a ƙarƙashinsa. Ga su kamar haka:

A. Makaɗa Sa’idu Faru

1. Ala’du a Makaɗa Sa’idu Faru

2. Gudummawar Makaɗa Sa’idu Faru ga ilimi

3. Gurbin Makaɗa Sa’idu Faru a fannin zaman lafiya da sasantawa

4. Ƙarangiya da gagara bami da ɓad da wawa a waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru

5. Makaɗa Sa’idu Faru da adabi

6. Makaɗa Sa’idu Faru da al’ummomi

7. Makaɗa Sa’idu Faru da cigaban al’umma

8. Makaɗa Sa’idu Faru da harshe

9. Makaɗa Sa’idu Faru da intanet

10. Makaɗa Sa’idu Faru da tattalin arziki

11. Makaɗa Sa’idu Faru da zamani da shirin game-duniya

12. Nazarin waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru

13. Tarihin Makaɗa Sa’idu Faru

B. Waƙoƙin Sarauta/Waƙoƙin Fada

1. Al’ada a waƙoƙin fada

2. Gurbin waƙoƙin fada a cikin adabi

3. Gurbin waƙoƙin fada a cikin ilimi

4. Gurbin waƙoƙin fada a duniya

5. Gurbin waƙoƙin fada ga tattalin arziki

6. Gurbin waƙoƙin fada ga zaman lafiya da sasantawa

7. Salo da zubi da tsarin waƙoƙin sarauta

8. Sauye-sauye a waƙoƙin fada

9. Tarihi a cikin waƙoƙin fada

10. Tarihin samuwar da bunƙasar waƙoƙin sarauta

11. Tasirin waƙoƙin sarauta

12. Tattarawa da kundace waƙoƙin sarauta

13. Waƙoƙin fada a farfajiyar Hausa da Hausawa

14. Waƙoƙin fada da al’ummomi

15. Waƙoƙin fada da cigaban al’umma

16. Waƙoƙin fada da duniyar intanet

17. Waƙoƙin fada da harshe

18. Waƙoƙin fada da zamani da shirin game-duniya

C. Adabin Baka

1. Adabin baka da al’ummomi

2. Adabin baka da kwamfuta da intanet

3. Adabin baka da zamani da shirin game-duniya

4. Dangantakar adabin baka da al’ada

5. Dangantakar adabin baka da harshe

6. Dangantakar adabin baka da tarihi

7. Dangantakar adabin baka da tattalin arziki

8. Gurbin adabin baka a ilimi

9. Gurbin adabin baka a zaman lafiya da sasantawa

10. Gurbin adabin baka ga cigaban al’umma

11. Sauye-sauye a duniyar adabin baka

12. Tattarawa da kundace adabin baka

Kada a manta da cewa, a koyaushe za a iya karanta cikakken bayani game da taron a nan: https://www.amsoshi.com/2024/01/an-international-conference-on-life-and.html

Su kuwa muhimman bayanai da muke turowa cikin wannan zauren, za a iya karanta su a nan: https://www.amsoshi.com/2024/02/makaa-saidu-faru-conference-update-page.html

Kada kuma a manta da cewa, ana iya turo mana shawarwari da ƙorafi a keɓance ta;

📌 Email: delac@fugusau.edu.ng

📌 WhatsApp: +2347062052814

Mun gode matuƙa.

Sanarwa Ta 005: Albishir (Sassauci Da Garaɓasa a Kuɗin Taro)

1. Muna farin cikin sanar da ku cewa, masu shirya wannan taro na bakin ƙoƙarinsu wajen ganin an sassauta matuƙa ga kuɗin gabatar da takardu. Wannan wani yunƙuri ne na ganin kuɗin taron bai hana waɗansu da ke da niyya halartarta ba. Muna kyautata zaton kuɗin da za a sanya ya kasance ɗaya daga cikin mafiya araha a duk tarukan ƙara wa juna sani na ƙasa da ƙasa da za a gabatar a shekarar 2024.

2. Ƙari bisa abin da aka ambata a sama (lamba 1) shi ne, masu gudanarwar sun fitar da wani tsari mai taken “Garaɓasa.” Wannan tsari ne da zai ba wa masu son halartar taron biyan kuɗi a hankali (sau biyu). Ma’ana, za su biya 50% a karon farko, sannan su biya sagowar 50% ɗin daga baya. An yi hakan ne la’akari da matsalolin tattalin arziki da ake fuskanta da kuma hauhawan farashin abubuwa.

Lura: Wani abin burgewa shi ne, duk waɗannan rahusa da garaɓasa ba za su rage komai daga inganci da aminci da kuma shagulgular da ake shirin gudanarwa ba a lokacin wannan taro. Ana fatan sai ma abin da ya ƙaru na ƙayatarwa da ilimantarwa da nishaɗantarwa.

Sanarwa Ta 006: Albishir (Bugu Takardu Kyauta!) 💃🕺

Muna ƙara godiya da ban-gajiya ga ɗaukacin malaharta wannan taron ƙara wa juna sani. Ƙoƙarin da aka yi baki ɗaya shi ya kai ga nasarar taron da izinin  Ubangiji.

Muna farin cikin sanar da ku cewa za a wallafa dukkannin takardun da suka cancanci wallafawa a kyauta, ba tare da ko sisi ba.

Ba za a karɓi kuɗin duba takardu ba (free vetting waiver).📌

Ba za a karɓi kuɗin wallafawa ba (publication fee waiver).📌

Wannan babbar garaɓasa ce ga dukkannin waɗanda ke da takarda. 

Kwamitin da ke jagorancin tantance takardu na ƙarfafa wa mutane guiwa da su hanzarta sanya shawarwari da gyararraki da aka musu yayin gabatar da takardun, tare da ƙara inganta takardun nasu kafin su turo. Nan da wani lokaci za a sanar da lokacin da za a fara karɓar takardu domin tura wa masu dubawa (vetters).

Mun gode.

Kada a manta da cewa, a koyaushe za a iya karanta cikakken bayani game da taron a nan: https://www.amsoshi.com/2024/01/an-international-conference-on-life-and.html

Su kuwa muhimman bayanai da muke turowa cikin wannan zauren, za a iya karanta su a nan: https://www.amsoshi.com/2024/02/makaa-saidu-faru-conference-update-page.html

Kada kuma a manta da cewa, ana iya turo mana shawarwari da ƙorafi a keɓance ta;

📌 Email: delac@fugusau.edu.ng
📌 WhatsApp: +2347062052814



Post a Comment

1 Comments

  1. Masha Allah! Gaskiya wannan ya ƙayatar da ni sosai. Ubangiji Allah Ya sa a yi wannan taro lafiya a gama lafiya.

    ReplyDelete

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.