Ticker

6/recent/ticker-posts

Maganin Kara Kauri Da Tsawon Azzakari

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum, Malam. Wallahi, ni ne ranan muna tare da iyalina, sai ta ce min na sha maganin da zai ƙara min girman azzakari na da kuma tsayinta. Hakan ya sa ni na washe ta, kuma har na ce mata wannan zai iya saka na zarge ta, amma ta yaya ta san wannan maganar? Sai ta ce wai taji ana fada akwai maganin ne a radio. Gaskiya yanzu Malam na rasa yaya zan yi shiyasa na ce don Allah indai akwai yadda za'ayi azzakarina ta kara tsayi da girma ka taimaka min, domin ni bani da matsalan rashin karfin azzakari sai dai gaskiya azzakari na bai wuce 9 centimeter ko kuma ince tsayin ruler karami na cikin math-set. Saboda haka, don Allah, Malam akwai hanyan da zan yi azzakarina ta karu? Malam kuma wanne shawara zaka bani akan wannan maganan da ta gaya min domin har yanzu bana jin sha'awanta kaman da, thank you very much for your contribution. Malam don Allah ina bukatan amsar ka, domin nafi jin aminci tattare da maganganunka da hujjoji da kake bujirowa da su. Na gode. Allah ya ƙara maka imani.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh.

Gaskiya ɗan'uwa Ya kamata ka godewa Allah tunda ya baka cikakkiyar lafiya da ikon yin aure, sannan ya baka matar da ka aura, harma kuka samu daman biyan bukatunku na sha'awa. Idan ka duba zaka ga wasu da dama suna da lafiyar jiki, amma kuma mazakutarsu batta da

cikakkiyar lafiya. Wasu kuma suna da cikakkiyar lafiyar amma Allah bai basu ikon yin auren ba, har ranar mutuwarsu. Bai kamata ka ji haushin matarka saboda ta baka wannan shawarar ba. Watakila akwai dalilin da yasa ta baka shawarar. Watakila kana da wuƙa mai kaifi ne, amma baka san yadda zaka yi aiki da ita ba. Don haka ya kamata kayi tunani akan wasu halattattun hanyoyin da zaka bi domin gamsar da ita ayayin da kuke Jima'i.

Ka fara gabatar da wasanni, da kalamai na soyayya, da chanja position alokacin Jima'i. Duk waɗannan suna sanya ma'aurata su samu gamsuwa da junansu. Kodayake, Allah Ya halicci maza gwargwadon nau'in mazakutarsa kuma da hakan ne kowa zai iya biyan bukatar jima'i ga matarsa. Allahu Ya bambamta maza wajen halittar mazakuta haka kuma Ya bambamta mata wajen halittarsu. Saboda haka ne, bukatarsu ta bambamta ta fuskar jima'i, inda wasu matan ke son namiji mai girman azzakari ko kuma mai tsawo da zai cika su, ko kuma ya kai makurar farjinsu kafin su samu biyan bukata.

Masana sun ce, wasu matan Ubangiji Ya halicce su da zurfi ko fadin farji ta yadda idan azzakarin mutum gajere ne ko kuma ba shi da kauri to da wahala ya iya biya wa irin waɗannan mata bukata ta fuskar jima'i. Irin waɗannan mata kan samu gamsuwa ne kawai idan sun yi arangama da mai girman azzakari. Wannan dalili ya sa matarka ke son ka kara girman azzakari.

Masana a wannan fanni sun gudanar da bincike mai zurfi kuma sun samar da hanyoyi da yawan gaske da za a iya kara kauri da tsawon azzakari, amma mun zaɓi wasu hanyoyi guda biyu dangane da wannan makala. Mun zaɓi wadannan hanyoyi biyu ne saboda suna da saukin haɗawa, kuma kayan haɗin na samuwa a kowannne lokaci kuma ga su da araha. Sabosa haka kowa zai iya haɗawa a gida ba tare da wahala ba, kuma ya kara girman azzakarinsa. Maza da yawa sun jarraba su kuma sun samu biyan bukata.

1. Hanya Ta Farko: Ana haɗa wannan maganin karin kauri da tsawon azzakari ne da abubuwa biyu kacal: Su ne NAMA da kuma ZUMA.

Yadda zaka haɗa wannan magani shi ne; ka samu nama marar kitse ko kuma mu ce jan nama. Sannan ka tanadi zuma mai kyau marar haɗi. Bayan ka kammala takidar waɗannan kayan haɗin na ka, sai ka yanka naman nan yanka-yanka gwargwadon yadda mahauta ke yanka wa masu abinci naman sayarwa, amma zai yi kyau kar yankan ya kasance kanana sosai, sai ka soya naman, amma ka lura da kyau kar ya kone, don gudun kar a rasa wasu sanadarai masu muhimmanci.

Bayan ka kammala soya naman nan sai ka zuba shi cikin ruwan zumarka da ka tanada tun da farko, sai ka adana a mazubi mai kyau. Kullum da dare sai ka dinga cin naman nan yanka ɗaya. Da ikon Allah za ka sha mamaki. Wannan hadi an jarraba shi kuma an samu biyan bukata, don haka ka gwada zaka yi mana addu'ar alkhairi daga bisani, in sha Allahu. Wannan shi ne hanya ta farko yadda ake ƙara girman azzakari a saukake.

2. Hanya Ta Biyu. Ita ma wannan hanya ce mai sauki kwarai da gaske kuma kamar ta farkon ba ta da wahalar haɗawa. Hanya ce da mutum zai bi ya kara girman azzakarinsa, wato kara kauri da tsawon azzakarinsa. Abubuwan da mutum zai tanada sun haɗa da, ALBASA da ZUMA da GARIN HABBATUS SAUDAH da kuma GARIN FIJIL.

Yadda zaka haɗa shi ne, da farko zaka markada ALBASAR bayan ka gyara ta, sai ka zuba ta cikin ruwan ZUMA ka gauraya su, sannan sai ka ɗora a wuta ya dafasu, amma sama-sama, sai ka sauke.

Bayan ka sauke sai ka zuba GARIN HABBATUS SAUDA da na FIJIL cikin haɗin can na ALBASA da ZUMA ka gauraya su sosai, ka tabbatar sun gaurayu. Wannan haɗin za ka dinga sha babban cokali kullum da safe kafin ka karya kumullo. In sha Allahu zaka bamu labari, idan hakan bai samu ba, mu na fatan ka yi mana addu'a.

Mu na kira ga ma'aurata kan kar suyi sake wajen kula da lafiyarsu musamman ta fuskar jima'i saboda yadda ake samun korafe-korafe wajen mata game da matsalar rashin biyan bukata daga wajen maza. Kuma masana da yawa na danganta hakan ta fuskar raunin mazakuta. Don haka a yau mun kawo ma hanyoyi biyu, yadda za ka kara girman azzakarinka a saukake. Allah Ya sa mu dace, Ameen.

A karshe mu na kara kira ga mai karatu kan ya rarraba wannan makala a kafofin sada zumunta na zamani (social media) don wasu jama'ar su amfana. Amma Kuji tsoron ALLAH, kada ku kwafa (copy) ku goge wani abu daga ciki, koda Links ne. Ga wanda ya jarraba kuma ya dace, mu na barar addu'a ga iyayenmu da malamanmu. Mun gode. Allah ta'ala yasa mudace.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Za ku iya samun shafinmu ta wannan hanyar...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments