Ticker

6/recent/ticker-posts

Ta Haihu Kafin Ta Cika Wata Bakwai Da Aure

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Malam yarinya ne aka aurar da ita batayi wata bakwai ba 7 ta haihu cikakkiyar yarinya yar wata tara (9) to malam meye hukuncin auren kuma ya hallaccin jaririyar a musulunci?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikum salam, In har an San tanada ciki aka yi auran wannan hukuncinsa a fili yake, kuma auran bai inganta ba a zance mafi inganci, amma in haihuwa ta yi bayan wata bakwai, kuma ba'a santa da ciki ba to Ɗansa ne, saboda ayar suratu Lukman da tá suratul Ahkafi sun nuna cewa ana iya haife ciki a watanni shida.

Auran da aka yi da cikin shege ba tare da an sani ba ya inganta, saidai ba za a danganta cikin zuwa mijin ba, tunda ba shi ya yi ba.

In har ya san tana da ciki bayan sun yi aure bai halatta ya take ta ba har saí ta haihu, saboda fadin Annabi Sallallahu alaihi Wasallam "Duk wanda ya yi imani dá Allah da ranar Lahira to kar ya shayar da ruwansa ga shukar waninsa" kamar yadda Abu-dawud ya rawaito.

In ta haihu za su iya cigaba dá mu'amalarsu ta aure, musamman in bai sani ba saí da aka daura auren.

Allah ne mafi sani.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/DIcJIQrWyLP0oBOMSnDi5P

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments