𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Akramakallah shin akwai hadisin da ya tabbata daga manzon
Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) cewa yace '' man ra'ani fil manami
fasayarani fil yaqzwa'' wato wanda ya ganni a mafarki to tabbas zai ganni a
fili. To shin malam hakan tana yiwuwa, kuma har ma Annabin ya bada wata falala?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Ɗan'uwa wannan hadisi ne tabbatacce daga Annabi Sallallahu
alaihi Wasallam kamar yadda Bukhari ya rawaito shi a hadisi mai lamba ta: 6592
Saidai malamai sun yi saɓani
game da lafazin zai ganni a fili, wasu sun ce: ma'anarsa: zai gan shi ranar
alkiyama da sifa ta musamman , wasu kuma sun ce zai gan shi a duniya, saidai
wannan zancen yana da rauni sosai, tun da hadisi ya tabbata cewa Annabawa suna
cikin kabarinsu, wasu malaman kuma sun ce hadisin yana Magana ne akan wadanda
suka zo a zamaninnsa, ma'ana duk wanda ya gan shi a mafarki, to zai haɗu da shi.
Malamai suna cewa abin da ake nufi shi ne ka gan shi da
siffofinsa wadanda suka tabbata a hadisi, inda za ka gan shi bakikkirin ba
gemu, ko da mafarkin ya nuna maka Annabi ne to ba shi ba ne, tun da hakan ya saɓawa siffarsa a hadisi,
wannan ya sa idan mutum ya zo ya cewa: Muhammad dan Siirin (RA) ya ga Annabi
Sallallahu alaihi Wasallam a mafarki yakan ce masa siffanta min shi, in ya fadi
kamannin da suka saɓawa
hadisai, sai ya ce ba shi ka gani ba, an rawaito kwatankwacin haka daha Ibnu
Abbas.
Ba'a karɓar
wani hukunci ko wata falala daga Annabi Sallallahu alaihi Wasallam a cikin
mafarki, saboda hakan yana nuna tawayar addini, tare da cewa aya ta uku a cikin
suratul Ma'ida ta nuna cikar addini, tun fiye da shekara dubu
الْيَوْمَ
أَكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَأَتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ الْإِسْلَامَ
دِينًا
A yau Na kammala muku addininku, Kuma Na cika ni'imaTa a
kanku, Kuma Na yarda da Musulunci ya zama addini a gare ku. (Suratul Maida aya
3)
Don neman Karin bayani duba: Alminhaj na Nawawy 1/50 da kuma
Fathul-bary 12/386.
Allah ne mafi sani
Jamilu Zarewa
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/EbkKRXdFzNu4F8aQZbZ1Vx
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.