Ticker

6/recent/ticker-posts

Datun Hausawa a Zamanance, Kwadon Dambu Da Kabeji, Datun Garin Kwaki Da Ganye, Datun Salat, Gwaben Tumatur, Kwadon Kabeji

Gabatarwa

An gina babi na bakwai sukutum kan kwaɗo. A cikin ƙarƙashin 7.1 an kawo maanar kwaɗo. A ƙarƙashin 7.2 kuwa, an zayyano nauo’in kwaɗo na gargajiya da yadda ake sarrafa su. Wannan babi kuwa yana ɗauke ne da nau’o’in kwaɗon da suka samu a zamanance. Yana da kyau a fahimci cewa, kusan dukkanin nau’ukan kwaɗon da ake da su a gargajiyance akan same su a zamanance. Duk da haka akan samu ‘yan bambance-bambance ta ɓangaren sarrafawa, musamman da yake zamani ya zo da kayan haɗi iri-iri dangin ɗanɗano da ƙamshi.

Kwaɗon Dambu da Kabeji

Duk wani dambun da aka yi fari ba tare da haɗi ba, to za a iya kwaɗo da shi. Yayin samar da wannan kwaɗo, akan kwaɗanta dambun da kayan haɗi ne kai tsaye. Su kuwa kayan haɗin da ake amfani da su sun haɗa da:

Kayan haɗin da za a tanada su ne:

i. Albasa

ii. Dambu

iii. Gishiri

iv. Kabeji

v. Magi

vi. Mai

vii. Ƙuli

viii. Tarugu

Kwaɗon Garin Kwaki da Salat ko Zogale ko Tafasa ko Rama

Garin kwaki ma akan kwaɗanta shi da ɗaya daga cikin nau’o’in ganyaye da aka lissafa a sama. Da fari ana jiƙa garin ne. Bayan ya jiƙa sai a haɗa shi da kayan haɗi a gauraya kamar dai yadda ake sauran kwaɗo da aka yi bayani a sama. Kayan haɗin da ake amfani da su sun ƙunshi:

Kayan haɗin da za a tanada su ne:

i. Garin Kwaki

ii. Gishir

iii. Magi

iv. Mai

v. Ƙuli

vi. Ruwa

vii. Tumatur

viii. Tarugu

ix. Salat ko zogale ko tafasa ko rama

Kwaɗon Salat

Shi ma kansa ganyen salat ana iya kwaɗanta shi. Wato zai kasance an yayyanka salat ɗin ne sannan a sanya masa kayan haɗi (a maimakon a sanya shi cikin wani nau’in kwaɗo a matsayin kayan haɗi). Nau’o’in kayan haɗin da ake buƙata yayin kwaɗon salat sun haɗa da:

Kayan haɗin da za a tanada su ne:

i. Albasa

ii. Gishiri

iii. Magi

iv. Mai

v. Ƙuli

vi. Ruwa

vii. Salat

viii. Tarugu

ix. Tumatur

Kwaɗon Kabeji

Shi ma kabeji akan iya kwaɗanta shi a ci. Ana yin kwaɗon nasa ne kamar yadda ake na sauran ganyayen da Bahaushe yake kwaɗantawa, musamman salat. Kayan haɗin da ake amfani da su sun ƙunshi:

Kayan haɗin da za a tanada su ne:

i. Albasa

ii. Gishiri

iii. Kabeji

iv. Kukumba

v. Magi

vi. Mai

vii. Ƙuli

viii. Ruwa

ix. Tarugu

x. Tumatur

Kwaɗon Tumatur

Shi ma tumatur akan iya kwaɗanta shi. Yayin samar da wannan nau’in kwaɗo, akan samu tumatur masu kyau a yayyanka. An fi so a samu tumatur mai nama sosai (ma’ana wanda ruwan cikinsa kaɗan ne). Akan tanadi kayan haɗi kamar su:

Kayan haɗin da za a tanada su ne:

a. Albasa

b. Gishiri

c. Magi

d. Mai

e. Ƙuli

f. Ruwa

g. Tarugu

h. Tumatur

Kammalawa

Kamar dai yadda aka gani a sama, kwaɗo ya kasance nau’o’i daban-daban. Duk da cewa akan yi kwaɗo domin rashi ko toshe yunwa, sau da dama kwaɗo na kasancewa abin marmari, musamman yayin da aka sanya kayan haɗi sosai. Wani abin da ya sa ake son kwaɗo shi ne, sauƙin sarrafawa da kuma kasancewarsa abincin gaggawa. 

The book “Cimakar Bahaushe” (Diets of the Hausa People) is a collection of 293 traditional and modern diets of the Hausa people. Detailed explanations of the recipes and ingredients are provided. Comments are provided on the areas of the Hausa land where specific diets are mostly found, the age categories of people that usually use it, as well as the scientific impact of some of the diets to human biology.  Data is collected from interviews with different categories of people including:  i.                    Food sellers within the Hausa land: Mainly to have an idea of recipes on the diets.  ii.                  People of older age: Mainly to have insights on traditional diets of the Hausas.  iii.               Hausa scholars: Mainly to verify and justify the validity of the information obtained as well as provide further expert explanations on the diets.  Moreover, over two hundred (200) pieces of literature were reviewed to have better insight on the topic in question as well as get scientific and professional clarifications on some key concepts relevant to the research. The pieces of literature cover major relevant phenomena such as diet and hunger. Others are on the Hausa land and the Hausas.  The book contains thirty-three (33) chapters. Chapter one is the main introduction in which a concise explanation is provided on the Hausas, their history, their land, social life, and transformations due to globalization, acculturation, and modernity. Chapter two detailly discusses the concepts of diet and food from the Hausa point of view. That includes the meaning and the usage of diets in some Hausa works of literature both verbal and written (i.e. prose, poetry, proverbs, etc.).  Chapters three and four discuss the sources of Hausa diets and their forms accordingly. Chapters five to seventeen discuss some traditional Hausa diets including hard and soft ones. Chapter eighteen concentrates on the influence of modernity and globalization on Hausa diets. It has been discovered that there have been some significant changes in the Hausa diets ranging from recipes to kitchenettes.  Chapters nineteen to thirty-two discuss modern Hausa diets. Some traditional diets are still retained with little modifications, while on the other hand, there are a lot of new ones. Chapter thirty-three discusses “hunger” from the Hausa point of view. The relationship between hunger and food is examined. Additionally, the use of hunger in various Hausa literary works is studied. It is concluded that hunger is like a disease whereby its cure is food.  7th November 2022
Citation (Manazartar Littafin): Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

Get a copy:
To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
+2348133529736

You can also write an email to:

Post a Comment

0 Comments