Ticker

6/recent/ticker-posts

Bajinin gidan Bello Mamman Na Yari Sarkin Kudu MacciDo ci maraya (Wakar Makada Sa'idu Faru)

Jagora:

Bajinin gidan Bello Mamman Na Yari,

S/Kudu Macciɗo ci maraya,


Y/Amshi :

Bajinin gidan Bello Mamman Na Yari,

S/Kudu Macciɗo ci maraya,

Jagora /Y/Amshi :

 Na Marafa D/baba

 mai tura haushi,

  Na S/Gabas duniya

   hori wawa,

 

Jagora: 

Na Marafa Ɗ/baba


Y/Amshi :

Mai tura haushi 

Na S/gabas duniya

hori wawa, 

Bajinin gidan Bello Mamman Na Yari, 

S/Kudu Macciɗo ci maraya, 


Jagora: 

Bai gadi sake ba 

Mamman Na Baura, 


Y/Amshi :

Toron Giwa Uban Bello 

Mato, 


Jagora :

Bai gadi sake ba Mamman 

na Baura, 


Y/Amshi :

Toron Giwa Uban Bello 

Mato, 

Duh Hausa ba mai irin hanƙuri nai, 


Jagora /Y/Amshi :

Toron Giwa Uban Bello Mato, 

Duh Hausa ba mai irin hanƙuri nai, 

Bajinin gidan Bello Mamman Na Yari, 

S/Kudu Macciɗo ci maraya, 


Jagora:

Na Marafa Ɗ/baba mai tura haushi, 

Na S/gabas duniya hori wawa, 


Jagora: 

Na Marafa Ɗ/baba, 


Y/Amshi :

Mai tura haushi, 

Na S/gabas duniya hori

wawa, 


Jagora:

Babban dutci a hange ka nesa, 


Y/Amshi :

A ishe ka tsoronka ya tcarma kowa, 


Jagora: 

Babban dutci a hange ka nesa, 


Y/Amshi :

A ishe ka tsoronka ya tcarma kowa, 

Da ɗai babu geben da yak kai ga gulbi, 

Ruwan Maliya sun wuce masu taru, 


Jagora/Y/Amshi :

Da ɗai babu geben da yak kai ga gulbi, 

Ruwan Maliya sun wuce masu taru, 

Bajinin gidan Bello Mamman Na Yari,

S/Kudu Macciɗo ci maraya, 


Jagora:

Na Magaji mai martabad'

ɗan Mu'azu 


Y/Amshi :

Irin assabab Bubakar baba yayyo


Jagora :

Na Magaji mai martabad' ɗan Mu'azu


Y/Amshi : 

Irin assabab Bubakar baba yayyo


Jagora :

Tsari gaskiya Bello kai Shefu yacce


Y/Amshi :

Bari masu son dus su mai sheka yaro


Jagora :

Tsari gaskiya Bello kai Shefu yacce


Y/Amshi :

Bari masu son dus su mai sheka yaro, 

Da kyauta da ilmi da neman dalili, 

Da gode ma Allah da

Istangafari, 

Da su Bello ɗan Shehu yatc tcarma kowa, 

Ka kai kam mab Bello, 

Ka gadi Moyi, 

Saura ka kai inda mai Hausa yak kai


Jagora :

Ka kai kamab Bello 


Y/Amshi :

Ka gadi Moyi, 

Saura ka kai inda mai Hausa yak kai,


Jagora:

Da mutun da dabba, 

Da tsuntsu da ƙwaro, 

Da mutun da dabba,

Da tsuntsu da ƙwaro, 

Da ƙasa da abin da duk ag ga bayanta, 

Komi duniya na Almusd'aha na,

Manzon Allah abin so gare mu, 

Garai Shefu yas samu girma da yarda, 

Komi na gun Shefu shi ag ga Bello, 

Komi na gun Bello shi ag ga Garba, 

Komi na gun Garba kai ad dashi Bello 


Jagora /Y/Amshi :

Ko lahira kau muna tak'ama tai

Bajinin gidan Bello Mamman Na Yari 

S/Kudu Macciɗo ci maraya, 


Jagora :

Bai gadi sake ba Mamman na Baura, 


Y/Amshi :

Toron Giwa Uban Bello Mato, 


Jagora:

Bai gadi sake ba Mamman na Baura, 


Y/Amshi :

Toron Giwa Uban Bello Mato, 

Duh Hausa ba mai irin hanƙuri nai,


Jagora: 

Toron Giwa Uban Bello Mato


Y/Amshi :

Duh Hausa ba mai irin hanƙuri nai 


Jagora:

Baba ya bamu bandur guda dun na lailai, 

Ya bamu bandur guda dun na yadi,

Ya bamu fam goma yace mu ɗunka,

Ga takalumma na fan shidda shidda, 

Hula kalabus guda goma yab ban, 

Doki da kaya da kuɗɗin ciyawa, 

Kyauta irin taka jikan Mu'azu, 

Don ba a cewa mutun ba kama tai,


Y/Amshi :

Sai Larabawan Masar masu girma


Jagora :

Don ba a cewa mutun ba kama tai 


Y/Amshi :

Sai Larabawa Masar masu girma, 


Jagora :

Da biskit da minti da taba sigari, 

Da biskit da minti da taba sigari, 

Da lemu da soda da kwalbas sitawut, 

Bai yarda aza su ko sau guda ba, 

Ya ɗau wasiccin da Usumanu yacce, 

Ya ce abincinsu ba namu ne,

Yawancin abincinsu daɗi gareshi, 

Kowam mami yay rashi ba ruwa nai, 


Y/Amshi :

Wancan naci an naci bai ci can ba, 

Bajinin gidan Bello Mamman Na Yari,

S/Kudu Macciɗo ci maraya, 


Jagora :

Muhamman dalilin ka nis san Talata, 


Y/ Amshi :

Muhamman dalilin ka niz zamni Hausa, 


Jagora :

Muhamman dalilin ka nis san Talata, 


Y/Amshi :

Muhamman dalilin ka niz zamni Hausa,

Kowas sammu gidan ga nan an ka sammu, 

Kuma ban wuce ba nan mun ka dage,

Ban zo gidan Ɗan bita niy yi roƙo ba, 

Ko ya raba lafiya ba ruwa na, 


Jagora/Y/Amshi :

Ban zo gidan Ɗan bita niyyi roƙo ba, 

Ko ya raba lafiya ba ruwa na, 

Bajinin gidan Bello Mamman Na Yari, 

S/Kudu Macciɗo ci maraya, 


Jagora:

Ginshinshimin Kanwuri ban ganai ba, 

Dunb'arumin Kanwuri ban ganai ba, 

Kama cikin ka tsohon bak'auye, 

Burtuttu mai kan bulon cin abinci, 

Ga ko wanakiri ya sha tumatur, 

Wai shi aka ba ragi yanzu garka, Jagora /Y/Amshi :

Allah shi dum mai da kowa ga gadonsu 

Da wane kunya tana yab'uwatai


Jagora: 

Allah shi dum mai da kowa ga gadonsu 


Y/Amshi :

Da wane kunya ta na yab'uwatai 

Daga Taskar:
Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

Post a Comment

0 Comments