Jagora :
Yayyi mutun mai ƙoƙari,
Sannan yayyi mutun mai kyawo,
Kuma yayyi mutun mummuna,
Sannan yayyi mutun mai haske,
Kuma yayyi mutun mai dauni,
Sannan yayyi mutun mai samu,
Kuma yayyi mutun busasshe,
Sai yayyi mutun É—an Sarki,
Kuma ya aza bawan Sarki,
Sannan yayyi mutun mai iko,
Y/Amshi :
Albarkan Nana Uwad Daje,
Bamu Mato Muhamman Sarkin Kudu,
Albarkan Nana Uwad Daje,
Bani Mato Muhamman Sarkin Kudu,
Jagora :
Laihin yaro shi yi ƙuiya,
Laihin babba shi yi rowa,
Ina ƙamnak ka Muhammadu,
Na tabbatak' ƙamna ta ka kai,
Ko kai niyya bamu Dawakuna,
Samnan Bahwade sara ya kai,
Ya ce ko ka bamu Dawakuna,
Randa Sallah ka tashi ƙaura mukai,
Ya ce ko ka bamu Dawakuna,
Randa Sallah ka tashi ƙaura mukai,
Jagora :
Mamman haraka sai yaj jiya,
Yac ce kai ko ƙarya kakai,
Ƙaura da Gusau da Kwatarkwashi,
ÆŠangulbi da BunguÉ—u ham Maru,
Dud É—ai na ga Mamman Sarkin Kudu,
ÆŠan Dikko ya na can yaj jiya,
Wannan magana ta tabbata,
Daa inda rana ka fita gabas,
Har inda rana taka faÉ—uwa,
Dud É—ai na ga jikan ÆŠanhodiyo,
Babu wurin da mulki nai yatc tcaya,
Y/Amshi :
Dud É—ai na ga jikan ÆŠanhodiyo,
Babu wurin da mulki nai yatc tcaya,
Kana shire Baban Yan Ruwa,
Na Bello jikan ÆŠanfodiyo,
Jagora :
Maganag ga da zani hwaÉ—a maka,
Y/Amshi :
Gagarau É—an Alu kai min gahwara,
Jagora :
Maganag ga da zani hwaÉ—a maka,
Y/Amshi :
Gagarau É—an Alu kai man gahwara,
Wada dud aka gado É—aukaka,
Wada dud aka gado ƙasura,
Wada dud aka gadon ci gaba,
Mamman ka gadi Abubakar,
Ko da sayen halin nan akai,
Baba halin da kakai kuÉ—É—i shi kai,
Jagora :
Ko da sayen halin..
Y/Amshi :
Halin nan akai,
Baba halin da kakai kuÉ—É—i shi kai,
Jagora :
Ko ni MakiÉ—inka Uban Zagi,
Y/Amshi :
Don na gadi a bamu garuruwa,
Jagora :
Ko ni MakiÉ—in Uban Zagi,
Y/Amshi :
Don na gadi a bamu garuruwa,
Na gadi a bamu jukunkuna,
Na gadi a bamu Dawakuna,
Mamman in Allah yai nuhi,
Bamu gari da mutane nai duka,
Jagora :
Mamman in...
Y/Amshi :
Allah yai nuhi bamu gari da mutane nai duka,
Jagora :
Babban daji kake É—an Abu,
Y/Amshi :
Ko icce ko namun dawa,
Jagora :
Babban daji kake É—an Abu,
Y/Amshi :
Ko icce ko namun dawa,
Ko manya ko yan ƙank'ane,
Da mutun da dabba da itatuwa,
Kowa ƙamnam Mamman ya kai,
Mamman jikan Attafiru,
Baba na Sidi,
Mamman gwarzon Cika,
Jagora :
Mamman...
Y/Amshi :
Mamman jikan Attafiru,
Baba na Sidi,
Mamman gwarzon Cika,
Kana tsaye Baban Yan Ruwa,
Na Bello jikan ÆŠanhodiyo,
Jagora :
Halin ga da Bubakar yar riƙa,
Y/Amshi :
MacciÉ—o kai ka shirin gado haka,
Jagora :
Halin ga da Bubakar yar riƙa,
Y/Amshi :
MacciÉ—o kai ka shirin gado haka,
Jagora :
Gurbin Giwa....
Y/Amshi :
Sai É—an ta,
Daudu zaman gurbi sai É—an Kada,
Jagora :
Gurbin Giwa...
Y/Amshi :
Sai É—an ta,
Zomo an ka aza yab bag gida,
Kana shire Baban Yan Ruwa,
Na Bello jikan ÆŠanhodiyo,
Jagora :
Tafiyag ga da kayyi da bani nan,
Jagora /Y/Amshi :
Nib bika ina gudu gani nan,
Jagora :
Tafiyag ga da kayyi da bani nan,
Y/Amshi :
Sai nib bi Gusau sai niw wuce,
Sai nib bi Kwatarkwashi niw wuce,
Kuma nib bi ta Tcahe ina gudu,
Can na kusa kaiwa Zariya,
Dan nan Daudu niko sai nitc tcaya,
Jagora :
Haka nan fa,
Y/Amshi :
Sai S/Zazzau nig gani,
Yac ce man Muhamman
ya tai Haji,
Jagora :
Ya tai Haji Mu'azu..
Y/Amshi :
Sai nis saki hanya nii gabas,
Can na taɓa yat tafiya kaɗan,
Sai nii ishe Suda ta na kiyo,
Ta na ta Waƙas S/Kudu,
Rai nai ya daÉ—e S/Kudu,
Alisabinanin É—an Amadu,
Allah shi ƙara mai nasara,
Nic ce Suda Waƙa akai,
Tac ce lalle Waƙa nikai
Waƙam Muhamman S/Kudu,
Waƙan nan da Ɗan Umma yay mashi,
Ban cin uwats Tsuntsaye nike,
Inda kamam milki na nikai,
Da na mai wasik'a yay man KiÉ—i,
Jagora :
Faru ba..
Y/Amshi :
Dan nan nikau sai niw wuce,
Can na taɓa yat tafiya kaɗan,
Sai nii ishe Burtu na kiyo,
Shi na ta Waƙas S/Kudu,
Rai nai ya daÉ—e S/Kudu,
Alisabinanin É—an Amadu
Allah shi ƙara mai nasara,
Jagora :
Amin...
Y/Amshi :
Nic ce Burtu Waƙa akai,
Yac ce lalle Waƙa nikai,
Waƙam Muhamman S/Kudu,
In nayi ta zani wurin kiyo,
In niz zo abinci sai ije,
Jagora :
Ihmmm!
Y/Amshi :
Dan nan niko sai niw wuce,
Can na taɓa yar tafiya kaɗan,
Na kai bakin Bahar Maliya,
Sai nii ishe Larabawa wurin,
Suna ta Waƙas S/Kudu
Rai nai ya daÉ—e S/Kudu,
Alisabinanin É—an Amadu,
Allah shi ƙara mai nasara,
ÆŠan mai darajja S/Kudu
Jikan mai darajja É—an Amadu,
Sannan mai darajja shi yayyi shi,
Shi na gida zanne a Sakkwato,
In yay Sallah yay casbaha,
Hasken nashi han nan kallo mukai...
Turken Waƙa:
Kana shire Baban Yan Ruwa,
Na Bello jikan ÆŠanfodiyo.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.