Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wasa Da Azzakari Har Ya Kai Ga Fitar Da Maniyyi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Menene Hukuncin Wasa Da Azzakari Harya Kai Ga Fitar Da Maniyyi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

الحمد لله

Wannan al'ada ita ce malamai suke kira istimna'i wato mutum yaiwasa da gabansa har maniyyi yafita mace ko namiji.

Wanda haramunne a alqur'ani da hadisi

Ibnu kaseer rahimahullah yace : Imamu shafi'i da wadanda suka goyi bayansa yakafa hujja da haramcin wasa da gaba da faɗin Allah madaukakin sarki

وَالَّذِينَ هُمْ لِفُرُوجِهِمْ حَافِظُونَ ٥۝ إِلَّا عَلَىٰ أَزْوَاجِهِمْ أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُمْ فَإِنَّهُمْ غَيْرُ مَلُومِينَ ٦۝ فَمَنِ ابْتَغَىٰ وَرَاءَ ذَٰلِكَ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الْعَادُونَ ٧۝

Bayin Allah nagari Sune waɗanda dangane da farjinsu suke kiyayeshi. Face a kan matan aurensu, ko kuwa abin da hannayen damansu suka mallaka (kuyanginsu) to lalle su ba waɗanda ake zargi ba ne. Saboda haka wanda ya nemi abin da ke bayan wancan, to, waɗancan su ne masu ƙetarewar haddi. (Suratul Muminun 5-7)

Imamu shafi'i acikin littafin Aure yace sai ya kasance Allah yabayyana kiyaye farjinsu saifa akan matayensu ko abinda damarsu tamallaka, sai yazama haramun idan ba matarka bace ko kuyangarka sai Allah ya karfafi maganar dacewa " wanda ya nemi koma bayan hakan yana cikin masu taka dokokin Allah"

Bai halatta amfani da azzakari ba sai akan matarka ko baiwarka, bai halatta jin-daɗi dashi da hannu ba wallahu A'alamu kitabul ummu na imamu shafi'i.

Wasu malaman sun kafa hujja taharamcin istimna'i da faɗin Allah madaukakin sarki

وَلْيَسْتَعْفِفِ الَّذِينَ لَا يَجِدُونَ نِكَاحًا حَتَّىٰ يُغْنِيَهُمُ اللَّهُ مِن فَضْلِهِ

Wadanda ba su samu damar aure ba sukame har sai Allah ya wadata su daka falalarsa. (Suratul Nur aya 33)

Sukace: umarni da kamewa yana nuna hakuri da rashin samun yin auren ko kuyangar.

A sunnah kuwa sunkafa hujja da hadisin Abdullahi dan mas'ud Yardar Allah takara tabbata a gareshi ya ce: Mun kasance tare da Annabi sallallahu Alaihi wasallam muna samari bamu samu komai ba sai Annabi sallallahu Alaihi wasallam yace damu "ya ku taran samari duk wanda yasamu halin daukar dawainiyar iyali yayi aure, domin yanasa kamewa daka gani, yana kuma tsare farji, wanda kuma bai samu dama ba to nahore shi dayin azumi domin azumi yana kariya daka fadawa haram. Bukhari 5066.

Sai shari'a ta shiryar lokacin da mutum ya gajiya wajen yin aure sai ya dunga azumi tare da wahalarsa, shari'a bata shiryar zuwa wasa da farji ba, tare da saukinsa akan azumi tare da haka ba'a halatta shiba.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments