Ticker

6/recent/ticker-posts

Yunwa Na Nan: Birgima Tsakanin Harshe, Adabi Da Kuma Al'ada

 Takardar ƙara wa juna sani da aka gabatar a ajin ALH 400: Seminars, a Sashen Nazarin Harsuna Da Aladu, Jamiar Tarayya Gusau, Nijeriya, (2022/2023 Academic Session).

Federal University Gusau (FUG) Nigeria

Yunwa Na Nan: Birgima Tsakanin Harshe, Adabi Da Kuma Al'ada

SUNA: Muhammad Shayau

LAMBAR WAYA: +2348167271109

ƘIBƊAU: shayau2004@gmail.com

 Tsakure

Wannan muƙala na bayyana yadda samarin da ‘yan mata da matasan garin Gusau, ke amfani da wata sabuwar kalma da suka ƙirƙira wajen nuni ko ishara zuwa ga shuwagabanni da masu hannu da shuni, game da halin da al'ummar garin ta tsinci kanta na yunwa da ƙangin talauci.

 Fitilun Kalmomi

● Yunwa:- A mahangar ilimi da mu'amala, yunwa na nufin wani yanayi da mutum yake da rauni a zahiri, ta sanadiyyar rashin abin masarufi a hannunsa, da rashin samun abin da zai ci domin ya rayu. Ita kalmar yunwa ba kawai tana nufin buƙatuwar abinci ba kamar yadda kowane mutum ya sani, har ila yau tana bayanin kwaɗayi ko muradin abinci. Matakin yunwa na ƙarshe shi ne matsanancin da ke haifar da yaɗuwar rashin sinadarai da abinci ke ɗauke da su a jikin ɗan Adam wanda a sanadiyyar hakan ake mutuwa.

● Matasa:- Matasa gungu ne ko dandazon wasu mutane da shekarunsu ba su gaza 20 zuwa 25 ba. Yawanci shekarun sukan fara ne daga 15 zuwa 20, 25 har zuwa 30 kuma jinsi ne na maza (lafiyayyunsu da marasa lafiyarsu).

‘Yan mata:- ‘Yan mata su ma kamar matasa ne amma a tsara, jinsinsu mata ne zalla ba najimi haka kuma, masu ƙananan shekaru waɗanda ba su yi aure ba. Shekarunsu na fara daga 15, 17, har zuwa 25.

● Gusau:- Garin Gusau gari ne da ke Arewa maso yammacin Najeriya kuma, shi ne babban birnin jihar Zamfara. Garin Gusau yana da faɗin ƙafa 3,364Km da kuma jama'ar da yawansu ya kai kimanin mutum 383,562.

● Shuwagabanni:- Shuwagabanni waɗansu mutane ne ‘yan tsiraru da a kan zaɓa ko jagorantarwa don cika muradin al'ummar da suka zaɓe su ko suka shugabantar da su, don tabbatar musu da doka da tsari bisa shugabanci na adalci.

1.1 Dalilin Bincike

Kowane bincike da aka gudanar ko ake gudanarwa na ilimi ko na wani abu a duniya, to lallai za a samu yana da dalilin gudanar da ya haifar da gudanar da shi. Hakan take a wannan binciken da aka gudanar, shi ma yana ɗauke da dalilan da suka sa aka gudanar da shi kamar haka:-

 1. Domin gano dalilin samuwar jimlar “yunwa na nan” da gano alfanu ko tasirin samuwarta a cikin al’umma.
 2. Domin feɗe kalmar da kuma gano ma’anarta ta asali da dalilin ƙirƙirarta.
 3. Domin nuna irin tasirin da ta yi akan ‘yan siyasa da masu hannu da shuni da ma al'umma gaba ɗaya.

1.2 Manufar Bincike

Wannan bincike da aka gudanar yana da wata manufa ta musamman ga ‘yan siyasa da mawadata da kuma sauran al'umma kan halin da mutanen garin Gusau suka tsinci kansu na yunwa da talauci. Haka kuma, don ƙara fito da maanar jumlar da zaƙulo fassararta ta asali saɓanin yadda wasu mutane ke kallon ta da wata manufa ta daban. Yin sharhi na gaba ɗaya da kuma tsefe jumlar don kawo ma’anar abin da take nufi a fili.

1.3 Maƙasudin Bincike

Maƙasudin wannan bincike shi ne nuna wa duniya illar da yunwa take da ita da kuma tasirin ƙirƙira da muryar matasa a cikin alumma. Sannan kuma yin hannunka mai sanda ga ‘yan siyasa da masu hannu da shuni akan mutanen da amanarsu take hannunsu.

1.4 Tambayoyin Bincike

       Yunwa na nan” ƙoshi ko kukan yunwa?

       “Yunwa na nan” wahala ko kukan daɗi?

       “Yunwa na nan” talauci ko raha?

       “Yunwa na nan” tsanani ko wadata?

       “Yunwa na nan” gyara ko ɓarna?

       “Yunwa na nan”?

1.5 Muhimmancin Bincike

Babban muhimmancin wannan bincike shi ne

 1. Domin gano ma’anar jumlar
 2. Domin fahimtar me take nufi
 3. Domin sanin ga wa take komawa
 4. Domin fahimtar tasirinta ga al’umma

1.6 Kadadar Bincike

Wannan bincike yana da faɗi sosai sai dai, yana da kadadar da take nuna inda ya tsaya. Binciken namu ya ja birkinsa a iya garin Gusau da matasa da ‘yan mata da kuma samarin garin.

1.7 Kalmomin Fannu

Yunwa na nan: ƙirƙirarriyar sabuwar jumla ce wacce samarin garin Gusau suka ƙirƙira, da take ɗauke da dunƙulallen saƙo ga shuwagabanni don ankarar da su halin da al'ummar wannan garin suka tsinci kansu na halin yunwa da ƙangin talauci.

 Dabarun Gudanar da Bincike

Farfajiyar wannan bincike na taƙaita ne ga kimiyyar harshen Hausa ga ƙirƙirar sabuwar jumlar ishara ko nuni ga wani ko ga waɗansu tsirarun mutane. An yi la’akari da sabuntar wannan jumlar wato irinta ta farko yayin gudanar da wannan bincike, wajen tuntuɓar samari da matasa ta hanyar tuntuɓarsu da kuma tattaunawa da su.

Kasancewar binciken bai fita daga cikin farfajiyar fahimtar Malam Bahaushe ba, an ɗora wannan aiki akan tunanin Bahaushe na; “da wasa ake faɗa wa wawa magana”. Ko da ma dai waɗansu daga cikin kalmomin barkwancin Hausawa faɗakarwa ce ake yi a fakaice. A bisa wannan fahimta, binciken na da hasashen cewa, ƙirƙirarrun kalmomin da ake ƙirƙira game da mutane, na mazaunin hannunka-mai-sanda. Suna iya faɗakarwa da ankararwa ga mutane.

Gundarin Aiki

Ma’anar Jumlar

“Yunwa na nan” na iya ɗaukar ma’anar zallar yunwa da ƙarancin abinci da rashin wadataccen kuɗin sayen abin masarufi. A ɗan ƙaramin binciken da muka gudanar mun gano cewa, jumlar yunwa na nan a tsakanin kowane lungu da saƙon da talakawan garin Gusau ke zaune a ciki. Wato a iya cewa hantsi leƙa gidan kowa yunwar ta yi wa lungunan masu ƙaramin ƙarfi a garin.

Ma’anar Jumlar a Tsakanin Al’umma

A tsakanin al’ummar garin Gusau kuwa, jumlar ta samu ma’anar ta kasu zuwa biyu, yayin da waɗansu ke furta jumlar a matsayin raha don tsokanar juna da wasa, a yayin da waɗansu kuwa ke furta ta don yin isgilanci ga waɗansu ko ga wani.

Ma’anarta ta raha kamar yadda bincikenmu ya gano ita ce: furta wa juna ko wani da wani jumlar don kawai a yi raha a yi dariya. Wani kan kalli wani ko waɗansu gungun mutane kawai ya ce “yunwa na nan” ba tare da sun harzuƙa ko sun ta da jijiyar wuya ba. Wannan yana faruwa a tsakanin samari, matasa da ‘yan mata.

Amma a ma’ana ta isgilanci kuwa, mutane kan furta wa wani ko waɗansu iyalai ko wasu mutane wannan jumlar da zimmar ci musu mutunci ko yin isgili a gare su. Bincikenmu ya gano hakan sakamakon nuna alama da jikinsu ya yi ko kasa aiwatar da wani abu da aka saba aiwatarwa. Idan mutum ya samu rama (ko da ta rashin lafiya ce) mutane kan yi amfani da wannan damar wajen furta masa wannan jumlar wato “yunwa na nan”.

Dalilin Samuwar Jumlar

A binciken da muka gudanar a tsakanin matasa da samari, mun gano cewa wannan jumlar ta samo asali ne daga halin yunwa da ƙangin talauci da alumma suka tsinci kansu a ciki. Wasu kuma suna da raayin cewa wannan kalmar an ƙirƙire ta ne don yin hannunka mai sanda ga jagorori da ‘yan siyasa masu riƙe da madafun iko da manyan masu kuɗi, don ankarar da su halin da talakawa suka tsinci kansu na matsanancin yunwa da ƙangin talauci.

Tasirin Jumlar a Tsakanin Al’umma

Wannan ƙirƙirarrar jumla ta yi matuƙar tasiri cikin abin da ka iya cewa tamkar wutar da daji haka ta riƙa yaɗuwa a tsakanin al’umma, mutane da yawa ne suke amfani da ita a tsakaninsu don raha ko isar da saƙo. Tasirinta ya yaɗu har a cikin mawaƙa da masu wasannin barkwanci an riƙa jiyo wannan jumlar.

Mallam Duro, wani mai wasan barkwanci ne kuma mawaƙin gidan rediyon Pride FM Gusau, shi ma ya rera wa tsohon gwamna wato Bello Muhammad (Matawallen Maradun) inda ya yi amfani da wannan jumlar a baiti na farko da yake cewa: Yunwa na nan sai bugu take,

 Ta hyaɗe maza mata suna gudu,

 Mulkin ceto in hakan yake,

 Mutanen Zamfara mun ga ƙaddara,

 Ya Allahu riƙa wa Matawalle yau,

 Talakawa shi muke jira ya zo

 Ya kawar mana gwamnatin ƙaya,

 Talauci na hyaɗar mutan jaha.”

Haka kuma, an samu wasu samari masu shirya wasan barkwanci a gidan talabijin na ‘Youtube’ masu suna Mr. Designer TV sun gudanar da wasan barkwancinsu inda suka yi amfani da wannan jumlar a cikin wasan nasu fa suke cewa

“Baba abun al’ajabi ɗazu mai unguwa ya canye rogon ɗari shidda, an yi magana yayyi gyatsa yacce wallahi marmari nai nikai. Ni ban ma san mi yammai da mu ba. Baba dun Allah ya za a yi ɗan Adam ya canye rogon ɗari shidda wai kuma marmari nai yakai, yunwa na nan!”

“Ina gaya ma yanzu rogo ai ya yi muƙami shi shi ma.

Haka kuma, na daga cikin tasirin da wannan jumlar ta yi shi ne faɗaɗuwarta har zuwa cikin manyan mutane da tsofaffi. Jumlar ta yi matuƙar tasiri inda ta riƙa yaɗuwa a tsakanin al’umma kamar wutar daji a ɗan ƙanƙanin lokaci.

Ƙara wa Jumalar Faɗi a Tsakanin Al’umma

A farkon al’amari kamar yadda bincikenmu ya gano, jumlar ba ta da wani ƙari sama da yunwa na nan amma, bayan ta yi yaɗo a tsakanin al’umma sai aka yi mata wasu ƙare-ƙare da ke nuna tasirinta a cikin alumma. Daga cikin ƙare-ƙaren da aka aka yi mata akwai faɗin

       “Yunwa na nan, garin kwaki ya bi jiki”

       “Yunwa na nan, rogo ya yi matsayi”

       “Yunwa na nan, muna ganinku masu kashin tafasa, ta safe ta game da ta rana.

Waɗannan ƙare-ƙaren da aka samu sun ƙara fito da jumlar, sun kuma ƙara fito da ainihin saƙon da take ɗauke da shi. Wannan ya sa mutane da dama suka ƙara mai da hankali akan manufarta.

Tasirin Muryar Samari da Matasa

Wannan ƙirƙira ta nuna irin ƙarfi da kuma tasirin da muryar matasa da samari ke da ita a tsakanin alummar da suke rayuwa a cikinta. Hakan ya nuna za a iya amfani da ƙirƙirarrun kalmomi (masu kyau) wajen isar da saƙo cikin gaggawa musamman ga shuwagabanni da makamantansu.

Zamanin Zuwan Jumlar

Wannan jumlar dai, an ƙirƙire ta ne a tsakanin watan Yuni zuwa watan Yulin shekarar 2023 kamar yadda wasu daga cikin matasan garin Gusau suka shaida mana. Kuma a zamanin mulkin shuga Bola Ahmed Tinubu shugaban ƙasar Najeriya, daidai da mulkin gwamna Dr. Dauda Lawal Dare Phd.

Amfanin Jumlar

Amfanin wannan jumlar a fili yake ƙarara tamfar rana a lokacin azahar. Kaɗan daga cikin jerin gwanon amfaninta sun haɗa da

1- Ta faɗakar

2- Ta nishaɗantar

3- Ta ankarar

4- Ta faɗaɗu zuwa wasu garuruwa

5- Ta isa inda ake so ta kai

6- Ta shiga jerin ƙirƙirarrun kalmomin Hausa

7- Ta yi tasiri

8- Ba batsa ba ce

9- Ta shiga bakin manya da ƙanana

10- An yi nazarinta.

Rashin Amfaninta

A ɗaya ɓangaren kuma muna ɗauke da rashin amfanin wannan jumla da za a iya cewa bai kai kaso ɗaya cikin ɗarin amfaninta ba. Rashin amfaninta bai wuce juyar da ma’anarta da wasu suke yi ba don cin mutuncin wasu ko nuna suna cikin yunwa bisa isgilanci.

Tsefe Jumlar

Ita dai wannan jumlar ta “yunwa na nan” kamar yadda bayanai suka gabata, jumla ce mai nuni da irin halin da wasu daga cikin mutanen garin Gusau suka tsinci kansu na rashin wadataccen abinci da sauran kayan masarufi kamar yadda bincikenmu ya gano. Harwayau, binciken namu ya gano cewa a da can baya, akwai kayan wadatar kayan abinci sosai a garin Gusau, don kuwa har laƙani aka yi musu da noma shi ne alfaharinmu amma daga baya kuma, sai ta rikiɗe ta zama cikin jerin gwanon jihohi masu fama da yunwa da matsanancin talauci.

Jumalar “yunwa na nan” saƙo ne dunƙulalle cikin hikima da dabarar isar da saƙo. Ba manufa ce ta nuna yunwa na nan tun tale-tale ba sai dai, yunwa na nan a zamani ko lokacin da aka ƙirƙiri jumlar kamar yadda bincikenmu ya gano. A wani binciken da muka gudanar a zantawarmu da wani matashi ɗan asalin garin na Gusau, ya shaida mana cewa ita wannan jumlar ba a ƙirƙire ta don wani saɓo ko ɓatanci ga wani ko wasu ba, sai dai don isar da saƙo da kuma bayyana halin da alumma suka tsinci kansu.

Sakamakon Bincike

Wannan bincike kusan za a iya kiransa da hanjin jimina, wato kome za a iya samu a cikinsa. Bayan nazari da kuma zurfafa wannan bincike, binciken namu ya gano abubuwa kamar haka

 1. Da yawan matsalolin da ake fama da su idan aka yi amfani da ƙirƙirarrun kalmomi ta hanyar amfani da muryar matasa da samari, za a iya shawo kan matsalar.
 2. Za a iya amfani da ƙirƙirarrun kalmomi wajen samar da nishaɗi a tsakanin al’umma.
 3. Ƙirƙirarrun kalmomi na iya haddasa sauyin yanayi a tsakanin alumma.
 4. Al’adun Hausawa ba su karo da ƙirƙirarrun kalmomi ba (musamman idan masu kyau ne).
 5. Kowane tsuntsu kukan gidansa yake yi. Mutanen garin sun yi amfani da ƙirƙirarrar jumla wajen sama wa kansu mafita.

Kammalawa

Samuwar wannan jumlar ya zo da juyin-juya-hali da kusan ya shafi kowane lungu da saƙo na jamaar garin Gusau, sakamakon tasirin da jumlar ta yi na kawo sauyi da kuma isar da saƙo cikin sauri tamkar haske! An kuma ga yadda mawaƙa masu wasan barkwanci suka riƙa tururuwa wajen yin amfani da wannan jumlar don ƙarfafa saƙonsu da na jumlar.

Post a Comment

0 Comments