Wani Lokaci Ne Ya Kamata Mace Tayi Sallar Azahar A Ranar Jumma'a?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Malam kamar da wanne lokaci ne ya kamata ace mace tayi sallar azuhur a ranar juma'a, shin za ta yi ne kafin ayi juma'a ko kuma sai bayan an idar da juma'a sannan za ta yi sallar azuhur din?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Shi dai lokacin sallar azuhur yana shiga ne daga lokacin da rana tayi zawali (ta karkace daga tsakiyar sama) to amma mutanen da sallar juma'a ba ta wajaba a kansu ba kamar irin su: matafiyi, Bawa, mace, maras lafiya, da dai sauran ma'abota uzuri, shin wai za su yi sallarsu ne da zarar lokaci ya shiga ko kuma dole za su jira har sai an dawo daga juma'a?

    Maganar da take tabbatacciya a shari'ance kawai za su yi sallarsu a duk lokacin da sukaga dama, ko dai suyi azuhur dinsu tun kafin ayi juma'a, ko su yi ta a lokacin da a ke yin sallar juma'ar, ko kuma suyi sallarsu bayan an taso daga juma'a, duk hukuncin daya ne ba wani bambanci, amma yin sallah a farkon lokaci yafi lada.

    Sannan kuma ya halatta mace ta halarci sallar juma'a tare da liman sai dai in ana jin tsoron faruwar wata fitina a dalilin zuwanta din, to sai tayi sallar azuhur dinta a gida kawai

    ​​шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'α'α'αʟα

               Mυѕтαρнα Uѕмαn

                  08032531505

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.