Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wanda Yayi Sallah Ba Zuwa Ga Alqibla Ba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Meye hukuncin mutumin da yayi sallah, sai bayan ya gama sannan ya fahimci cewa wannan sallah da yayi ba Alqibla ya fuskanta ba?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Yana daga cikin sharadin sallah mutum ya fuskanci Alqibla matukar ba wata matsala aka samu ba wadda zata hanashi hakan, inhar ko mutum yaki fuskantar Alqibla alhalin yana da dama toh sallarsa batacciya ce, sabida Allah yace

قَدْ نَرَىٰ تَقَلُّبَ وَجْهِكَ فِي السَّمَاءِ ۖ فَلَنُوَلِّيَنَّكَ قِبْلَةً تَرْضَاهَا ۚ فَوَلِّ وَجْهَكَ شَطْرَ الْمَسْجِدِ الْحَرَامِ ۚ وَحَيْثُ مَا كُنْتُمْ فَوَلُّوا وُجُوهَكُمْ شَطْرَهُ ۗ وَإِنَّ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ لَيَعْلَمُونَ أَنَّهُ الْحَقُّ مِنْ رَبِّهِمْ ۗ وَمَا اللَّهُ بِغَافِلٍ عَمَّا يَعْمَلُونَ

Lalle ne, Muna ganin jujjuyawar fuskarka a cikin sama. To, lalle ne, Mu juyar da kai ga Alƙibla wadda kake yarda da ita. Sai ka juyar da fuskarka wajen Masallaci Tsararre, kuma inda duk kuka kasance, to, ku juyar da fuskokinku jiharsa. Kuma lalle ne waɗanda aka bai wa Littafi, haƙiƙa su, suna sanin lalle ne, shi ne gaskiya, daga Ubangijinka. Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga abin da suke aikatawa. (Baqara 144).

Da umarnin da annabi (Sallallahu alaihi wasallam) yayi yace “Sannan ka fuskanci alQibla kayi kabbara) Bukhari 6667.

Maluman sun tafi akan cewa wanda yayi sallah ba zuwa ga Alqibla ba da gangan ko a halin mantuwa zai sake, sabida bai cika sharadinta ba.

An tambayi maluman ‘Lajnatudda’imah’ kan hukuncin matafiyi da ya isa gari, yayi sallah ba zuwa ga alqibla ba, kuma bai tambaya ba, baiyi bincike ba, suka ba da amsar cewa zai sake wannan sallar, sabida rashin bincike da baiyi ba, ko kokari wurin gano alqiblar, (Lajnatudda’imah Majmu’ah ta biyu 5/294).

Dan haka, ya wajaba akan wanda yayi sallah ba zuwa ga Alqibla ba yana mai mantuwa ya sake sallansa, amma in ya rasa gane Alqibla sabida rashin wanda zai tambaya, ko kuma wasu dalilai, toh mafi yawan Malamai suna akan bazai sake ba. kuma hakan shi ne daidai….

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Du5LNx31U9hDi6RQbbrzgW

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments