Gindin Waƙa: Riƙa da gaskiya,
Rana ba ƙoshi
takai ba,
Yari Ɗanbagge,
Noma ba ya saka rama.
Jagora:
Yari Danbaggi,
Rana ba ta sa ka rama,
Ku yi noma da gaskiya.
Yara: Don Allah ku hwanshi kanku,
Riƙa da gaskiya,
Rana ba ƙoshi takai ba,
Yari Ɗanbagge,
Noma ba ya saka rama.
Jagora: Yaro irin Amina Ɗan Maigujiya na sha ɗari,
Yara: Gyaɗo
mai kashin marake,
Riƙa da gaskiya,
Rana ba ƙoshi
takai ba,
Yari Ɗanbagge,
Noma ba ya saka rama.
Yaro: Don Ɗanbagge nit taho,
Yara: Don Ɗanbagge za ni wasa.
Jagora: Baicin ke Ɗanbagge,
Yara: Raggo ba ya shan duman ga,
Riƙa da gaskiya,
Rana ba ƙoshi
takai ba,
Yari Ɗanbagge,
Noma ba ya saka rama.
Jagora: Batun yau da nuj ji labarin ka arme
maza,
Yara: Ka tcere ma shaci tcimbo,
Riƙa
da gaskiya,
Rana ba ƙoshi
takai ba,
Yari Ɗanbagge,
Noma ba ya saka rama.
Jagora: Ku yi noma da gaskiya,
Yara: Don Allah ku hwanshi kanku,
Riƙa
da gaskiya,
Rana ba ƙoshi
takai ba,
Yari Ɗanbagge,
Noma ba ya saka rama.
Jagora: In dai ‘yab Buhari ta,
Yara: Kowa ba bari takai ba.
Jagora: In dai ‘yab Buhari ce,
Yara: Kowa ba bari takai ba.
Jagora: Yunwa ta taho da gorori ta iske maza,
Duk ƙaton
da taƙƙuma
ga wuya sai a shantale,
Yara: Shi ya hurce Kwantagora.
Jagora: Sannan ta waiwayo,
Yara: Ta ga ƙaton da bai ɗaga ba.
Jagora: In taƙƙumai
bugu,
Yara: Wajjen yamma za ya sauka,
Riƙa
da gaskiya,
Rana ba ƙoshi
takai ba,
Yari Ɗanbagge,
Noma ba ya saka rama.
Jagora: Sannan ta jirkito,
Yara: Ta ga ƙaton da bai ɗaga ba,
Riƙa
da gaskiya,
Rana ba ƙoshi
takai ba,
Yari Ɗanbagge,
Noma ba ya saka rama. ×2
Jagora: Sannan ta waiwayo,
Yara: Ta ga ƙaton da bai ɗaga ba.
Jagora: In taƙƙumai bugu,
Yara: Wajjen yamma za ya sauka.
Jagora: Ga hwa kudun ana tayi,
Yara: Amma ba a yin arewa. ×2
Jagora: Han na arwa sun biyo hanya sun ɓata ƙasam
Yara: Sai shayi sukai na gaske.
Jagora: Na arewa sun biyo hanya sun ɓata ƙasa,
Yara: Sai shayi sukai na gaske,
Riƙa
da gaskiya,
Rana ba ƙoshi
takai ba,
Yari Ɗanbagge,
Noma ba ya saka rama.
Jagora: Ni dai ban san na gaske ba,
Yara: Sai na sa dawo ga baki. ×2
Jagora: Kowac ce na gaske ne,
Yara: In dai ba dawo ba ƙyale. ×2
Riƙa
da gaskiya,
Rana ba ƙoshi
takai ba,
Yari Ɗanbagge,
Noma ba ya saka rama.
Jagora: Ko Guguwa a ad da ƙuli na ga ta sayas,
Yara: Ta bam mai na gaske zamne. ×2
Jagora: Ko Hadiza Amali na ga ta bugo hwanke,
Na ga ta sayas,
Yara: Ta bam mai na gaske zamne,
Riƙa
da gaskiya,
Rana ba ƙoshi
takai ba,
Yari Ɗanbagge,
Noma ba ya saka rama.
Jagora: Hashimu ya taho da rogo na iske ya sayas,
Yara: Ya bam mai na gaske na nan.
Jagora: Malam Abdu ya sayas,
Yara: Ya bam mai na gaske zamne,
Riƙa
da gaskiya,
Rana ba ƙoshi
takai ba,
Yari Ɗanbagge,
Noma ba ya saka rama.
Jagora: Kuma Mairamu ta sayas,
Yara: Ta bam mai na gaske zamne.
Jagora: To ƙarya ba na gaske na ba,
Yara: To ƙarya ba na gaske ne ba.
Jagora: Shi ya ce na gaske ne,
Yara: Kuma dai ya ƙi
sha ya ƙoshi,
Riƙa
da gaskiya,
Rana ba ƙoshi
takai ba,
Yari Ɗanbagge,
Noma ba ya saka rama.
Jagora: Rani wanga ya yi rani,
Ya sa maza lage,
Tahiwa wagga ta yi nisa,
Ta sa maza gaba,
Yunwa wagga ta yi yunwa,
Ta ba mu arkane,
Ga mata da ‘yan ɗoya,
Ka ji ƙatonta,
Ya yi lalata ya ɓata wuri,
Yara: Ya tcere yana ta kainai,
Riƙa
da gaskiya,
Rana ba ƙoshi
takai ba,
Yari Ɗanbagge,
Noma ba ya saka rama.
Jagora: In dai macce hat tana ɗiya,
Yara: Ta hi maigida sai in ranta bai gashe
ba.
Jagora: In ranta yai baƙi,
Yara: Ko yaƙi tana iyawa.
Jagora: In ranta yai baƙi,
Yara: Ko yaƙi tana iyawa,
Riƙa
da gaskiya,
Rana ba ƙoshi
takai ba,
Yari Ɗanbagge,
Noma ba ya saka rama.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.