Gindin Waƙa: Ya yi halin maza ko da rani bai sake ba,
Sabka lahiya mai batun yaƙi da sabra.
Jagora: Kada ruwa su ci mai hito,
Yara: Tun da bami bai iya ba. ×2
Jagora: Kada ruwa su ci mai hito,
Yara: Tun da bami bai iya ba,
Ya yi halin maza,
Ko da rani bai sake ba,
Sabka lahiya mai batun yaƙi da sabra.
Jagora:Kada ruwa su ci mai hito,
Yara: Tun da bami bai iya ba.
Jagora: Ran da bami ya iya,
Yara: Shi gwani ya gwanshi kai nai. ×3
Jagora: Ana ruwa Ɗan Namudi,
Yara: Mijin Hana ceci gayya. ×2
Jagora: Ana ruwa roƙi Allah,
Ya bar ma masu son ka,
Yara: Ɗiyan
maƙiyanka su ko,
Su hude ciki da barho.
Jagora: Ana ruwa roƙi Allah,
Ya bar ma masu son ka,
Yara: Ɗiyan
maƙiyanka su ko,
Su hude ciki da barho.
Ya yi halin maza ko da rani bai sake ba,
Sabka lahiya mai batun yaƙi da sabra.
Jagora: Sarki ya yi doka a bar waƙar manoma,
In ba mu garza su ba aiki sukai ba,
Yara: Dan nan am mahwarin hatci,
Ya katce ma gwarza,
Ya yi halin maza ko da rani bai sake ba,
Sabka lahiya mai batun yaƙi da sabra.
Jagora: Ga wasu na hwarin ciki an dwaɗikke roƙo,
Wannan mai hwarin ciki komi bai daɗa ba,
Wasu na baƙin
ciki roƙo ba a yi nai,
Yara: Wannan mai baƙin ciki ba rowa ya kai ba,
Ya yi halin maza ko da rani bai sake ba,
Sauka lahiya mai batun yaƙi da sabra.
Jagora: Ga sadda ana kiɗi ba ni kwana ba ta gari,
Yara: Da anka ruhe kiɗi ko kumallo ban ƙarawa,
Ya yi halin maza ko da rani bai sake ba,
Sabka lahiya mai batun yaƙi da sabra.
Jagora: Garba ga ni tsakag gida,
Yara: Ga takaici na ta cin ka.
Jagora: Sana ga ni cikin gida,
Yara: Ga takaici na cin ka.
Jagora: Labbo ga ni cikin gida,
Yara: Ga takaici na cin ka.
Jagora: Ga ni ba kuɗɗin awo,
Yara: Ga ka ba tsabad dakawa. ×2
Jagora: Tun da gero ya ɓace,
Yara: Dole sai mu gama da gari,
Ya yi halin maza ko da rani bai sake ba,
Sabka lahiya mai batun yaƙi da sabra.
Jagroa: Mu zo mu ga mai
jiƙo,
Yara: Alhajin jama’a Arewa. ×2
Jagora: A kai ni ga mai jiƙo,
Yara: Alhajin jama’a Arwa.
Jagora: Gari ya hito daz Zanhwara,
Ya dubi Gobir,
Garo ya buga gabas,
Ya kuma ma yamma,
Na yi abin wata ina taɓa
yawon ƙasaisai,
Ina saitin gidaje ina ta awon manoma,
Yara: Yau duk inda nib biya gari na rigya na,
Ya yi halin maza ko da rani bai sake ba,
Sabka lahiya mai batun yaƙi da sabra.
Jagora: Yau duk ina nib biya,
Yara: Gari na rigya na,
Ya yi halin maza ko da rani bai sake ba,
Sabka lahiya mai batun yaƙi da sabra.
Jagora: Kun gani yunwag ga,
Na sa mutum ya yi zamne
jangwam,
Yara: Yana magana cikin zuciya tai,
Ba a sani ba.
Jagora: Sai ka ji zuciya,
Tanai mai ebe-ebe,
Yara: Ya yi halin maza ko da rani bai sake
ba,
Sauka lahiya mai batun yaƙi da sabra.
Jagora: Ashe yunwag na sa mutum ya gaza da
mata,
Yara: Ya sa a yi mai jiƙo,
Ba ya ce mata tashi gashi,
Ya yi halin maza ko da rani bai sake ba,
Sabka lahiya mai batun yaƙi da sabra.
Jagora: Ka ga yunwag ga na iske ɗan gaye ta shuwai,
Yara: Ta ce mai tashi zaune.
Jagora: Ashe yunwag ga na iske ɗan gaye ta marai,
Yara: Ta ce mai ya hakan ga,
Ya yi halin maza ko da rani bai sake ba,
Sabka lahiya mai batun yaƙi da sabra.
Jagora: Na ga ɗan
gaye da gayan tuwo ya sa ga baki,
Kuɗɗin sabulu masu gari anka ba su,
Yara: ‘Yan kuɗɗin
ɓula masu bakuru nar riƙe su,
Ya yi halin maza ko da rani bai sake ba,
Sabka lahiya mai batun yaƙi da sabra.
Jagora: Wanga irin baƙin zamani Allah kiyaye,
Wasu na ta tashi suna tahiyas su Gwambe,
Mu kam mun tsaya nan muna gyaran gidaje,
In mun cimman gyaranta ba tashi mukai ba.
Yara: In ta ɓaci
ko Singa ba ta rigam mu bi ma,
Ya yi halin maza ko da rani bai sake ba,
Sabka lahiya mai batun yaƙi da sabra.
Jagora: Shekarun dandi ne,
Yara: Ba gudun kunya akai ba. ×2
Jagora: Yanzu karuwa tai yawa,
Yara: Ga su nan hab ba iyaka.
Jagora: Kuma ga ƙattan
da an nasu,
Ba aiki sukai ba. ×2
Jagora: Masu noma ‘yan kaɗan,
Yara: Masu ci nai ba iyaka.
Jagora: Karuwa ke baro uwaye ke zaɓi dandi,
Yara: Wagga ɗiya
uwayenki na da baƙin cikinki,
Ya yi halin maza ko da rani bai sake ba,
Sabka lahiya mai batun yaƙi da sabra.
Jagora: Tashi ba ki da gaskiya,
Yara: Ke baro ɗakin mijinki. ×2
Jagora: A a daw wata gaskiya?
Yara: Sai da aure za a yinta.
Jagora: Da duk ba a gyara aure ba,
Yara: Ke ma ba a yin ki.
Jagora: Dub ba a gyara aure,
Yara: Ke ma ba a yin ki.
Jagora: Ke an yo ki,
Yara: Ko ɗa
guda ba ki samu yi ba.
Jagora: In da kwana duniya ba a kwana lahira.
Yara: Ran da kwana nac cika,
Ban ga kwana duniya ba.
Jagora: A sai nono da mai,
Yara: In ji matan mai bisashe. ×2
Jagora: Ku sai tsabat tiya,
Yara: In ji mai mai ɗakin manomi. ×2
Jagora: Duk ku kawo in saye,
Yara: In ji matam mai sulalla,
Ya yi halin maza ko da rani bai sake ba,
Sabka lahiya mai batun yaƙi da sabta.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.