Dafa-Dukan Soyayyar Shinkafa
Kayan haÉ—in da za a tanada su ne:
i. Albasa
ii. Attarugu
iii. Gishiri
iv. Hanta ko ƙoda
v. Kabeji
vi. Karas
vii. Kori
viii. Magi
ix. Mai
x. Nama
xi. Ruwa
xii. Shinkafa
xiii. Tattasai (É—anye)
xiv. Wake (É—anye)
Ita ma za a yanka kayan lambu ƙanana-ƙanana, sannan a tafasa nama da hanta a yanka ƙanana-ƙanana a tafasa ruwa. Sai kuma a wanke shinkafa a zuba. Idan shinkafar ta fara alamar dahuwa,wato ta yi garas-garas sai a sauke a tace. Daga nan za a ɗora mai a wuta, idan ya yi zafi, sai a saka albasa tare da kayan lambun da aka yanka sala-sala. Za a yi ta juyawa, har lokacin da aka tabbatar sun fara laushi. Sai a zuba shinkafa da nama da magi da gishiri da kori a ci gaba da juyawa har sai shinkafar ta ƙarasa dafuwa tare da kayan lambun. Idan ta dafu, za a ga ta yi wara-wara ta sauya launi.
Dafa-Dukan Makaroni da Kabeji
Kayan haÉ—in da za a tanada su ne:
i. Albasa
ii. Gishiri
iii. Kabeji
iv. Karas
v. Kayan yaji
vi. Kori
vii. Kukumba
viii. Magi
ix. Mai
x. Makaroni
xi. Nama
xii. Ruwa
xiii. Tarugu
xiv. Tattasai
xv. Tumatur
Za a jajjaga tumatur da tarugu da albasa a saka kayan yaji a ciki. Sai a soya su, idan sun soyu, sai a yi sanwa tare da magi da gishiri da kori a ciki. Idan kayan sun tafasa, za a saka makaroni a goge karas a yanka a fere kukumba a saka. Za a iya tafasa nama a soya shi tare da tattasai a saka a ci tare da shi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.