Ticker

6/recent/ticker-posts

Wakar Marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau Ta Makada Musa Dankwairo

Wakar Marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau Ta Makada Musa Dankwairo
... Ya ja mani Rabbana Atiina,
Had da Ƙullan Yasibana yaj jaman...

Wani ɗan Waƙa a cikin Waƙar Marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau Suleja, Malam Ibrahim Dodo Musa wadda Makaɗa Musa Ɗanƙwairo Maradun ya rera masa mai amshi 'Mai Ƙasas Suleja ɗan Musa, ba a kai maka wargin banza'. 
Mai wannan hoton ne ya yi ƙarin wannan ɗan Waƙar a tsarinsu na karɓa - karɓa kuma shi ne Marigayi Alhaji Sani Musa Ɗanƙwairo Maradun(wanda ke saye da kaya kalar baƙi) da aka fi sani da laƙabin "Sani Zaƙin Murya" dake da muƙamin Marafan Kiɗi a Tawagar Kiɗa ta Marigayi Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun. Ya rasu a Shekarar 1988 sanadiyar hatsarin /haɗarin Motar da ya yi akan hanyar Gusau Zuwa Sakkwato kafin akai Garin Dange, Ƙaramar Hukumar Mulkin Dange /Shuni dake Jihar Sakkwato. Allah ya kyauta makwanci, amin.

Daga Taskar:
Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

Post a Comment

0 Comments