TAMBAYA (55)❓
Please ina da tambaya
Akwai Ayoyin da ake karantawa jarirai daga AL-QUR'AN daze
tsaresu daga sharin fiyade,luwadi,da lesbian?
AMSA❗
A haqiqanin gaskiya babu wata sahihiyar addua da ta zo a
sunnah akan wannan matsalan
Kwana kwanannan an samu case din wani mara imani da yayiwa
wata yarinya wadda bata fi shekaru 5 ba fyade silar garzayawa da ita asibiti
akayi mata aiki. Wannan wacce irin lalacewa ce ? Amsar saidai muce hakan yana
da alaqa da alamomin tashin alqiyama domin kuwa muna ganin alamun akan idanunmu
Yin zina tsakanin saurayi da budurwa babban laifi ne a
shari'ar musulunci, kuma alamu ne na cewar akwai karancin ilimi da kuma
yalwataccen jahilci da son zuciya ga mazinatan, wanda kuma yayiwa karamar
yarinya fyade wannan kam ba shi da tausayi kuma da za'a tambayeshi zai so ayi
hakan ga yar sa zai ce a'a. Anan shaidan da biyewa sha'awarsa sun yi tasiri
akansa har ya manta da gargadin Allah Azzawajallah;
( وَلَا
تَقْرَبُوا الزِّنَا ۖ إِنَّهُ كَانَ فَاحِشَةً وَسَاءَ سَبِيلًا
)
الإسراء
(32) Al-Israa
Kuma kada ku kusanci zina. Lalle ne ita ta kasance alfãsha
ce kuma tã mũnãna ga zama hanya
A kokarin neman maganin faruwar hakanne wata mata ta je
wajen wani malami wanda ya bata ayar dake cikin Suratu Maryam, wai ta dinga
karantawa a al'aurar yar wai ta hakan
zai sa ta samu tsari daga sharrin fyade da sauransu
Dukkan wannan bai zo daga sunnah ba
Amman abinda ya tabbata shine; an rawaito cewar Annabi SAW
yana yiwa jikokinsa wato Hassan da Hussaini bin Ali (Allah ya kara musu yarda
baki daya) wadda ta tabbata a cikin sahihan hadisai, kamar yanda Shaikh Sa'id
Alqataani (Rahimahullah) ya kawo a cikin littafinsa na Hisnul Muslim (Asaka
mawallafin littafin a addu'a domin kuwa a watanni baya ya koma ga MahaliccinSa)
Inda yace: Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a
gare shi, ya kasance yana nema wa Hassan da Husain tsari da wannan addu'ar
(Harma yace babanku {Annabi Ibrahim AS} yana yiwa yayansa {Annabi Ismail da
Ishaq} ga addu'ar kamar haka
أُعِيذُكُمَا
بِكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّة، مِنْ كُلِّ شَيْطَانٍ وَهَامَّةٍ، وَمِنْ كُلِّ عَيْنٍ
لاَمَّةٍ.
"O'eezukuma bikalimatil-lahit-tammah, min kulli
shaytanin wahammah, wamin kulli 'aynin lammah"
Bi ma'ana: "Ina neman muku tsari da kalmomin Allah
cikakku daga dukkan shaidan da wata dabba mai dafi, da kuma dukkan wani mai
kambun baka, mai cutarwa"
(Duba Sahihul Bukhari hadisi mai lambata 3371)
Sannan kuma tun ran gini tun ran zance, akan yi tuya a manta
da albasa ma'ana mutane sukan manta da addu'ar da Annabi SAW ya koyar kafin
tarawa da iyali, wadda rashin yinta kan iya kawo yiwuwar a haifi yaro
kangararre ya zo ya dameku ya dami al'umma da shaidanci domin kuwa sakacin
rashin neman tsarin Allah ne daman yasa shaidan kan shafi abinda Allah ya
azurta ma'aurata tunma kafin a haifi yaron, addu'ar itace kamar haka
بِسْمِ
اللهِ اللّهُمَّ جَنِّبْنَا الشَّيْطَانَ، وَجَنِّبِ الشَّيْطَانَ مَا رَزَقْتَنَا.
"Bismil-lah, allahumma jannibnash-shaytan,
wajannibish-shaytana ma razaqtana"
Ma'anarta: "Da sunan Allah. Ya Allah! Ka nisantar da
shaidan daga garemu, kuma ka nisantar da shaidan daga abin da Ka azurta mu da
shi"
Addu'ar tana cikin Sahihul Bukhari tareda Fathul Bari 4/181,
harma Shaykh Pantami yace ba abin mamaki bane idan kaga shaidanin yaro a wannan
zamanin, kana bin salsala zakagano iyayensa basuyi waccan addu'ar bane
Don haka wadannan sune wasu daga cikin sahihan addu'u'o'in
da suka inganta daga Ma'aiki SAW
Saidai kuma abu ne mai kyau kuma ya halatta iyaye su dinga
yiwa yayansu addu'a ta musamman domin neman kariyar Allah Azzawajallah musamman
ma a wannan zamani da muka tsinci kanmu a ciki. Akwai wata addu'a ta musamman
da Shaikh Aminu Daurawa ya shawarci iyaye su dinga tashi kamar karfe 3 na dare
suna roqawa yayansu, munsan cewar Allah SWT yana sakkowa sama'ud dunya a
kowanne karshen dare, kuma addu'ar iyaye karbabbiyace, a cikin addu'ar ne yace;
"...Allahumma hassin furujahum, minazzina, walliwadi,
wassihaqi, wa kullal jara'im..."
Ma'ana: Ya Allah ka tsare min gaban yaya na, ka kare su daga
zina, da liwadi, da madigo da dukkan laifuffuka
Muna roqon Allah ya bamu ikon fahimtar addini dakuma aiwatar
dashi, ya Allah ka tabbatardamu bisa tafarkin magabata na qwarai (Salafus
salih)
Wallahu ta'ala aalam
Subhanakallahumma, wabi hamdika, ash-hadu anla'ilaha illa
anta, astaghfiruka, wa'atubi ilayk
Amsawa;
Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/G5NSbo2TyHMD6bcoEfds5E
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.