Ticker

6/recent/ticker-posts

Wakar Garin Kwaki: Bage Dansala (Daga Ratayen Littafin Cimakar Hausawa)

Gindin Waƙa: A ci dai ba don a ƙoshi ba,

            Garin kwaki ya yi taimaka.

 

Jagora: ƙul ya ayul lazi amamata,

Yara: In don hadi kai kazalika.

 

Jagora: ƙul ya ayul lazi amamata,

Yara: In don hadi kai kazalika.

Bakandamiya ga abin ta hwaɗi,

Yara: Shi na yaz zaka babu gardama.

 

Jagora: Akwai wata rana nan tana zuwa,

Yara: Mai rai kan tuna radda zai mutu.

 

Jagora: Yunwar Ɗankurjan da taz zaka,

Yara: Hat ta hurce ba a yin jiƙo.

 

Jagora: Yunwar Shago,

Yara: Ta taho kuma,

            Hat ta hurce ba a yin jiƙo.

 

Jagora: Ham magabata,

Yara: Sun yi sun wuce,

            Sun gama yayi ba su yin jiƙo,

            A ci dai ba don a ƙoshi ba,

            Garin kwaki ya yi taimaka.

 

Jagora: Can da ban ce ma ga yanzu ba,

Yara: Garin kwaki ba ya yi Kabi,

            Dag ga Nuhwawa si Bayarrabe.

 

Jagora: Bara ga rani na ga al’ajab,

Yara: Ka ga abin da ka ba ka hirgita.

Jagora: Sai ka ji mata tai kira miji,

Yara: Ta ce wane abin da kaj jiƙa,

            Ya taso daidai a yi ta ci,

            A ci dai ba don a ƙoshi ba,

            Garin kwaki ya yi taimaka.

Jagora: Kuma sai ka ga ɗa na wa uwa tai kukam

            Wai shi ba shi yin jiƙo.

Yara: Ta ce mai koma ka dangana,

            Ba a tuwo yau taiba za a ci,

            A ci dai ba don a ƙoshi ba,

            Garin kwaki ya yi taimaka.

 

Jagora: Ga wata taikiri yara kun jiya,

            An bugo talho an yi min waya,

            An ce min gari shi na zuwa.

Yara: Amma na ce kay ya zo bana,

            Ban hwatat in koma yin jiƙo.

 

Jagora: Hudowar gari maso jiƙo,

            Sannan nis san kabu-kabu nan,

Yara: Garin kwaki shi da kanta-kalaje,

            Da ɗa wa na da ɗan ƙane.

 

Jagora: Tare suke,

            A ci dai ba don a ƙoshi ba,

            Garin kwaki ya yi taimaka.

 

Jagora: Garin kwaki wai hushi shi kai,

            Don na zo roƙon shi gahwara,

Yara: Sai yac ce min Bage Ɗansala,

            Ai ko can na san tana haka,

            A ci dai ba don a ƙoshi ba,

            Garin kwaki ya yi taimaka.

 

Jagora: Hucewa dai ɗan kwarakkwado,

            Tubashin dambu maso jiƙo.

Yara: Ɗan rogo huta da lafiya,

            Mun gode kakan kwarakkwado,

            A ci dai ba don a ƙoshi ba,

            Garin kwaki ya yi taimaka.

Jagora: Dole wuya ba ci da man iri,

            An ce buzu inda dus shike,

            Yay yi naɗi bai walwale shi ba,

Yara: Ran nan bara da za mu Yawuri,

            Ni ishe buzu za ya yi jiƙo,

            Dur rawani nai ya zube ƙasa,

            A ci dai ba don a ƙoshi ba,

            Garin kwaki ya yi taimaka.

 

Jagora: Garin kwaki ba ni ram maka,

            Na gode ma ka yi taimako,

Yara: In ban cin gari Najeriya,

            Da halaka ta hwarma ɗan Adam.

 

Jagora: Garin kwaki ba ni ram maka,

            Na gode ma ka yi tai taimako.

Yara: In bancin gari Najeriya,

            Da halaka ta hwar ma ɗan Adam.

 

Jagora: Kulum buta ag garan ɗaka,

            Shi nika ci in sha in a jiko,

Yara: Na mai she shi kamah hura ɗaka,

            Han na saba ba ni shaƙƙuwa,

            A ci dai ba don a ƙoshi ba,

            Garin kwaki ya yi taimaka.

 

Jagora: Yanzu in dai gari za ka yin jiƙo,

Yara: In nuna maka yadda za ka yi,

 

Jagora: Ga jiƙonshi ka ƙyale sa suga,

Yara: Sa mai bakuru ko hakin gwabe,

 

Jagora: Ga jiƙonshi ka ƙyale sa suga,

Yara: Sa mai bakuru ko hakin gwabe,

            A ci dai ba don a ƙoshi ba,

            Garin kwaki ya yi taimaka.

 

Jagora: Ga jiƙonshi ka ƙyale sa suga,

Yara: Sa mai bakuru ko hakin gwabe,

            A ci dai ba don a ƙoshi ba,

            Garin kwaki ya yi taimaka,

 

Jagora: Ban Yarbanci ba ni yin Ibo,

Yara: Ban iya taiba ba ba ni cin ɓula.

 

Jagora: Ban Yarbanci ba ni yin Ibo,

Yara: Ban iya taiba ba ba ni cin ɓula.

 

Jagora: Inyamurrai ran da ni ishe,

            Za su Hwatakot ta ƙule musu,

Yara: Sun ce min kedu-adumma,

            Ba su da kuɗɗi Bage Ɗansala.

 

Jagora: Zabarmawa da ne ishe masu,

            Sun yi Zabarmanci kala-kala,

Yara: Sun ce min hirkwaisu kai kasa,

            A ci dai ba don a ƙoshi ba,

            Garin kwaki ya yi taimaka.

 

Jagora: Hillani su ko da ni ishe,

            Hillanci ba mu san irinsa ba,

Yara: Sun ce min mindilli yamata,

            A ci dai ba don a ƙoshi ba,

            Garin kwaki ya yi taimaka.

 

Jagora: Nig ga Bashenge niy yi tambaya,

            Garin kwaki ko yana jiƙo,

Yara: Ya ce min aji tawo giwana,

            A ci dai ba don a ƙoshi ba,

            Garin kwaki ya yi taimako.

Jagora: Zuru da niz zo gun Badakkare,

            Nit tambai ko da yana jiƙo,

Yara: Ya ce ille burobo Ɗansala,

            A ci dai ba don a ƙoshi ba,

            Garin kwaki ya yi taimaka.

 

Jagora: Yara za ni ƙasar waje in kuna zuwa,

Yara: In ka tashi da mu muna zuwa.

 

Jagora: Yara za ni ƙasar waje in kuna zuwa,

Yara: In ka tashi da mu muna zuwa.

 

Jagora: Yara in na zo sai na yi tambaya,

            Turawa gari maso jiƙo,

Yara: Sun ce min til kom bakƊansala,

            Kad dawo zauna kana sani,

            A ci dai ba don a ƙoshi ba,

            Garin kwaki ya yi taimaka.

 

Jagora: Daɗa su ya kai gurbi ga tambaya,

            Ku Yarbawa na yi tambaya,

            Ku nis san kun gadi yin jiƙo,

            A a na aka yi shina yawa?

Yara: Sun ce min joko akai ma shi,

            Ba shi omi sosai shi kumbura.

 

Jagora: Ya hi yawa,

            A ci dai ba don a ƙoshi ba,

            Garin kwaki ya yi taimaka.

 

Jagora: Lale-lale Bage Ɗansala,

Yara: Baban Talle ɗan ƙanen Kulu,

            A ci dai ba don a ƙoshi ba,

            Garin wkaki ya yi taimaka.

 

Jagora: Ai akwai wata rana ran da za ni na,

            Nic ce ma shi ga ni na zaka,

            Tashi ka samu min abin daka,

Yara: Sai yac ce min Bage Ɗansala,

            Yaushe rabonmu da ko ganin dawo?

            A ci dai ba don a ƙoshi ba,

            Garin kwaki ya yi taimaka.

 

Jagora: Ran nan sai Bubuce niz zaka,

            Shi kuma Idi ni ishe ma shi,

            Sai nic ce ma shi ga ni na zaka,

            Idi ka samu min abin daka,

Yara: Sai yac ce min Bage Ɗansala,

            Duw wanda kay yi jiƙonshi mun jiƙa,

            A ci dai ba don a ƙoshi ba,

            Garin kwaki ya yi taimaka.

 

Jagora: Ran nan sai Bangara niz zaka,

            Na isa shi ko inda Hamidu,

            Sai nic ce mashi ga ni Hamidu,

            Tashi ka samo min abin daka,

Yara: Sai yac ce mini Bage Ɗansala,

            In ka samo zo ka ‘yam mana,

            A ci dai ba don a ƙoshi ba,

            Garin kwaki ya yi taimaka.

 

Jagora: Lale-lale Bage Ɗansala,

Yara: Baban Talle ɗan ƙanen Kulu,

            A ci dai ba don a ƙoshi ba,

            Garin kwaki ya yi taimaka.

 

Jagora: Ran nan birnin Diggi niz zaka,

            Su ko ringo mawa ni ishe,

            Sai nic ce mi shi Manu,

            Tashi ka samo min abin daka,

Yara: Sai yac ce mini Bage Ɗansala,

            Yaushe rabonmu da ganin dawo,

            A ci dai ba don a ƙoshi ba,

            Garin kwaki ya yi taimaka.

 

Jagora: Ran nan birnin Diggi niz zaka,

            Su ko kingomawa ni ishe,

            Sai nic ce mishi,

            Tashi ka samo min abin daka,

            Arne yas sadda kai sama,

            Na aza ni ko ba ni za shi yi,

 

Yara: Sai yac ce mani ba shi,

            In ka komo Diggi ka mutu.

 

Waƙar Muɗa: Gwamma Maibege Iyaka

 

Jagora: Ya bismillahi Rabbana na hwara,

Yara: Son ganin ka mukai Usmanu.

 

Jagora: Ya bismillahi Rabbana na hwara,

Hwara wa nikai da sunan Allah,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Komi za ka yi ka ambaci Allahi,

            Sannan harakka kai maka kyawo,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora:Malam Abdu assalamu alaikum,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Abdun an ka biɗe ni ka same ni,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Ni Gwamma ba bara ba,

            Sai wani aiki,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Ka shaida a kwai ɗumi ga ‘yar wazi,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Abdu an ni ta ar rabin dame ‘yar igge,

            Akwai ɗumi akwai labari,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Dido im munka tai gidan Usumanu,

            Ba kwana ba ba barin kwana ba,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Taru dai ba kwana ba,

            Ba barin kwana ba,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Allah taimakanni za ni kalami,

            Yunwar Muɗa marar albarka,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Ni Gwamma,

            Yunwam Muɗa ɗiyab banza ta,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Ta sa dibat tahwasa dibal laho,

            Ɗibar maguraza ɗibar rogo,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Dibo lokacin muɗa la’ananna,

            Diba tahwasa ɗibar lalo,

            Har ɗibar maguraza, ɗibar rogo,

            Ɗan rukuɓun dud da ya hito an ɗebe,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

Jagora: Ni Gwamma an saɓa ga rogon daji,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Samsamin rogo sun yi ɗiyansu,

            Dum mun ɗebe.

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Rogo na ta lillibo gun gona,

            Duk am bi kunnuwa an ɗebe,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Dibo yunwa Muɗa da taz za ka Abdu,

            Dibo yammam ag garinsu garinsu,

            Can inda jalla yat talitto ta,

            Gadara ag garinsu tak komo nan,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Muɗa gandara ag garinsu,

            Tak hauro nan,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Sai tad dangano da nata yali,

            Gtari duk tana kiran ya Allah,

            In ta tai gari, tambaya taka yi,

            Allah yo ina gidan zakaranu?

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Wani mai tcince da kwarmato,

            Yac ce mata sa gabanci dibo gabas,

            Kamat tsayin mutum na salla,

            Falale garin tudu in kiz zo,

            Don nan kama tambaya,

            Don Allah na san kina ganin ‘yar Igge.

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Falalen Tudu tak kama tambaya don Allah,

            Allah yo ina gidan zakaramu.

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Wani mai tcince da kwarmato,

            Yac ce mata Gwamma Iyaka at tungassu,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Wada tag gangaro da dutcin talla,

            Dan nan tak kama tambaya,

            Allah yo ina gidan zakaranu?

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Wani yac ce ta sa gaba gabas,

            Don Allah in kit tai ki tambayi malamai,

            Ke san gidansu na gwa da sheda,

            Iccen ceɗiya yana garkassu,

            Makaranta tana ga bakin zaure,

            Akwai maƙera irin ta ƙirar ƙarhe,

            In kit tambaya kina isko ta,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Abdu ina ɗaka zamne nai kaɗi na kwashe,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Ni Gwamma sai ni yi assalamu alaikum,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Ni ɗiya Ige ni ga ni nan da murnab baƙi,

            Nik kwashe zabgiya bisa ƙofa,

            Mai sallama shigo ga ɗaki,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Tac ce mani huta da zabgiya ‘yar Igge,

            Ni ba ni ta mutum ba,

            Ni ta yunwa,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Tac ce duba uwar bara ‘yar Igge,

            Ni ta niyy yi sallama ki amsa,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Sai nic ce mata zakka shigo marar albarka,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Tac ce tsaya ki ji ni yau waziri,

            Ni ta Muɗa marar albarka,

            ‘Yar baya hwanhwararar Allah,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Dibo yunwam Muɗa da ba ta da kunya,

            Nit tashi niy yi ƙuryaɗɗaki,

            Sai nid dibo sunguminmu na shibka,

            Nij jajiɓo shi niw wurge ta,

            Nir rimbiɗe ta hat tah hwaɗai,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Taz zabura tat tashi tab bi bakin ƙofa,

            Tac ce tsaya ɗiyar waziri,

            Mai rai komi shi kai shikan yi jawabi,

            Komi ya kai yakan yi jawabi,

            ‘Yak kande ba ni cin kazakki,

            ‘Yak kande ba ni cin jakkanku,

            ‘Yak kande ba ni cin zannunku,

            Amma ina kashin aurenki,

            Auren ko ke da Jaji da Bawa,

            Zama ba su koma yo maki ɗiba.

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Zakkah nir rimbiɗe ta har ta hwaɗi,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Tac ce dakaknta uwab bara yar Igge,

            To ke ga na cire kaya,

            Amma za ni na gidan Madibbo.

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Tat tai ɗaka ta iske malami na harda,

            Shi na kurɗaba gami da iziyya,

            Tad damƙe wuyansa sai ta jin ƙe,

            Tak kame tagguwa tam murɗe,

            Tac ce tsaya haba modibbo,

            Ni ta Muɗa marar albarka,

            Ka san ba ni yi da sunan Allah,

            Ka san hwarau-hwarau aka ba ni,

            Malam ko a ba ni guntun rogo.

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: To kuma malam koko a ba ni guntun hoce,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Tac ce sha hura ka gane baƙinka,

            Ba ka sha hura ba labari,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Tac ce kuma malam ci tuwo ka gane baƙinka,

            In ba a ci tuwo ba da labari,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: To mai shi ka cin tuwo ke maida,

            Mai shi, ka shan hura ke maida,

            Duw wanda bai da bai da dubara,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Ta iske wanda bai da dame,

            Ba gwallo ga rai ba,

            Baya da kuɗɗi,

            Sai maƙwar gwago taj jimƙe,

            Ta jujuwa shi nan tar rabke,

            Wau lammalin sun ɓace ga bakin malam,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Kuma al-hamza ta ɓace,

            Ga bakin malam,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Dibo tay yi kar kara ga garin kowa,

            Ba garinmu ɗai Gwamma ba,

            Tay yi rantsuwa da ikon Allah,

            Tac ce gabas da yamma mu gane,

            Sai ta yamutce mu dum mun watce,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Amma Zanhwaranmu na da hatcinsu,

            Da dama-dama ‘yar Waziri,

            Nan Hausa ta aje kayanta,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora:Dac can kassuwa ta Sakkwato,

            Can tas sawo tsuma bulala,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Tac ce ina maza manoma gero?

            Ina maza manoma dawa?

            ƙaƙa-ƙara-ƙaƙa kun ji?

            Kun ga tsuma bulala?

            In rimbiɗe ku in rabke ku,

            In lalabo ku in korro ku,

            In gargaɗo ku duk ku yi Bauchi,

            Ita ta Muɗa marar albarka.

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Ta sa ɗibat tahwasa ɗibal lalo,

            Hakin dud da ba a ci an canye,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Dibo Abdu korar Muɗa la’ananna,

            Ta sa maza sakin matansu,

            Ta sa maza su tud da ɗiyansu,

            In ƙarya ni kai mutane ku toge,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: ‘Yar baya Muɗa ita ce marar albarka,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Da tag gargaɗo maza suka watce,

            Malam waɗansu na nan zugu,

            Dibo waɗansu na Gada zamne,

            Waɗansu ga su gayaw zamne,

            Dibo waɗansu sun kai Maga,

            Dibo waɗansu na nan Zuru,

            Dibo waɗansu na Tadurga,

            Dibo waɗansu Wasagu,

            Dibo waɗansu sun kai Kanya,

            Wasu na Magajiya sun zauna,

            Wasu na cikin Rijau sun zauna,

            Dibo waɗansu Dirin daji,

            Dibo waɗansu na Badi zamne,

            Korenta na marar albarka,

            Ta ce Alhamdulillahi Allah,

            Shukran Hamdan, shukran Allah,

            Ta yamutce maza sun watse,

            Ta ce ta yi rantsuwa da ikon Allah,

            Wani sai lahira da shi da gidansu.

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Ta ce wani sai lahira da shi da gidansu,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Kuma in ƙarya ta nikai,

            Mutane ku toge,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Ni Gwamma rabin dami ‘yar Igge,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: In hwaɗa maka yunwan Muɗa marar albarka,

            Ta sa maza sakin matansu,

            Ta sa maza su tud da ɗiyansu.

Yara: Son ganinka mukai Usmanu.

 

Jagora: Abdu an wani ɗa sai lahira ya gane gidansu,

Yara: Son ganinka mukai Usmanu. 

The book “Cimakar Bahaushe” (Diets of the Hausa People) is a collection of 293 traditional and modern diets of the Hausa people. Detailed explanations of the recipes and ingredients are provided. Comments are provided on the areas of the Hausa land where specific diets are mostly found, the age categories of people that usually use it, as well as the scientific impact of some of the diets to human biology. Data is collected from interviews with different categories of people including: i.          Food sellers within the Hausa land: Mainly to have an idea of recipes on the diets. ii.         People of older age: Mainly to have insights on traditional diets of the Hausas. iii.        Hausa scholars: Mainly to verify and justify the validity of the information obtained as well as provide further expert explanations on the diets. Moreover, over two hundred (200) pieces of literature were reviewed to have better insight on the topic in question as well as get scientific and professional clarifications on some key concepts relevant to the research. The pieces of literature cover major relevant phenomena such as diet and hunger. Others are on the Hausa land and the Hausas. The book contains thirty-three (33) chapters. Chapter one is the main introduction in which a concise explanation is provided on the Hausas, their history, their land, social life, and transformations due to globalization, acculturation, and modernity. Chapter two detailly discusses the concepts of diet and food from the Hausa point of view. That includes the meaning and the usage of diets in some Hausa works of literature both verbal and written (i.e. prose, poetry, proverbs, etc.). Chapters three and four discuss the sources of Hausa diets and their forms accordingly. Chapters five to seventeen discuss some traditional Hausa diets including hard and soft ones. Chapter eighteen concentrates on the influence of modernity and globalization on Hausa diets. It has been discovered that there have been some significant changes in the Hausa diets ranging from recipes to kitchenettes. Chapters nineteen to thirty-two discuss modern Hausa diets. Some traditional diets are still retained with little modifications, while on the other hand, there are a lot of new ones. Chapter thirty-three discusses “hunger” from the Hausa point of view. The relationship between hunger and food is examined. Additionally, the use of hunger in various Hausa literary works is studied. It is concluded that hunger is like a disease whereby its cure is food. 7th November 2022
Citation (Manazartar Littafin): Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

Get a copy:
To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
+2348133529736

You can also write an email to:

Post a Comment

0 Comments