Ticker

6/recent/ticker-posts

Tsotsan Al'aura Tsakanin Ma'aurata

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin Ko Ya halatta ga Miji ya tsotsi gaban Matarsa ko ita Mace ta tsotsi gaban Mijinta ko ko kuma ta sha Maniyyinsa?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

​Asali dai a ​Shari'ance​ Ya halatta Mace da Miji su yi abin da ake ƙira da suna ​(Al-Istimta'u)​ wato ​Jindaɗī tsakanin Ma'aurata,​ dan haka Ya halatta su ji daɗi da junansu yadda  suka ga dama, Sai dai abin da ​Shari'a ta keɓance ta yi hani a kansa,​ kamar a ce ​Miji​ ya sadu da ​Matarsa​ a lokacin da take cikin ​Jinin al-ada ko jinin Bīƙi,​ ko kuma ​Miji​ ya sadu da ​Matarsa​ ta ​duburarta​ ko Saduwa da'ita lokacin da take yin ​Azumin-Farilla,​ dan haka ke nan idan ​Miji ya tsotsi Farjin-Matarsa​ ko ita ​Mace ta tsotsi azzakarin Mijinta​ Malamai suka ce duk Ya halatta, saboda hakan zai iya shiga ne cikin ​Ƙarƙashin​ hukuncin ​(Al-Istimta'u)​ wato Jindaɗī tsakanin ​Ma'aurata,​ Saboda ​Faɗin Aʟʟaн()​ cewa:​

نِسَاؤُكُمْ حَرْثٌ لَّكُمْ فَأْتُوا حَرْثَكُمْ أَنَّىٰ شِئْتُمْ  

​​MA'ANA:​​

​​Matanku Gonakanku ne, dan haka ku zo wa Gonakanku ta inda duk kuka ga dama:​​ (Suratul Bakara Aya ta 223)

​A cikin wata ​ayar​ kuma ​Aʟʟaн()​ Yace:​

هُنَّ لِبَاسٌ لَكُمْ وَأَنْتُمْ لِبَاسٌ للَهُنَ

​​MA'ANA:​​

​​(Matanku) tufafi ne a gareku, haka ku ma (Mazajensu) tufafi ne a gagaresu. (Suratul Bakara Aya ta 187)

​Amma idan ya kasance ana da tabbas ko zato mafi rinjaye game da cewa yin hakan zai iya haifarwa wani daga cikinsu wata cuta, ko kuma  ya kasance babu wata cuta da hakan zai haifar sai dai kawai ​ɗaya daga cikin Ma'auratan​ ba ya son a yi masa hakan to ​Malamai​ suka ce bai halatta su yi hakan ba dan gudun kada acutar da wanda ba ya so ɗin, Said ai wasu daga cikin ​Malamai suna ganin duk dacewa yin hakan ba haramun bane to amma barinsa shiyafi alkhairi,​

​Amma dangane da ​Magana​ akan hukuncin cewa idan ​Mace tana tsotsar azzakarin Mijinta​ haryakai ga yin ​Inzali (fitar maniyyi)​ a cikin bakinta, Shin ya halatta ta haɗiye wannan ruwan ​Maniyyin​ ko bai halattaba? ​Alal-Haƙiƙa anan Malamai sunyi Saɓani​ akan wannan ​Mas'ala,​ kuma ​Saɓanin​ nasu ya ginune akan Mas'alar cewa ​Shin Maniyyi najasane​ ko ba najasa bane? ​Malaman​ da suka tafi akan fahimtar cewa ​Maniyyi najasa ne​ suka ce Haramun ne Mace ta sha, domin ba ya halatta ga ​Mutum Musulmi​ ya ci ko ya sha dukkan abin da ya kasance jasa ne,​

​Saidai ​Magana​ mafi Inganci kamar yadda wasu daga cikin ​Malamai suka rinjayar itace,​ cewa ​Maniyyi​ ba najasa bane, to amma Saidai ​Malamai​ suka ce duk da kasancewar Maniyyi abune ​Mai-tsarki ba najasaba,​ suka ce bai kamata ace ​Mutum​ yasha ​Maniyyiba,​ domin yin hakan yana daga cikin ​ƙazanta,​ kamar yadda bai kamataba aga ​Mutum​ yana shan ​Majina ba,​ duk dacewa ​Majina​ ba najasa bace amma ko shakka babu cewa shanta ɗin ​ƙazantane,​​

​​шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'α'αʟαм

              ​​AMSAWA

           ​Mυѕтαρнα Uѕмαn​

              ​08032531505​

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBqfaiPwf28l

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa 

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments