Ticker

6/recent/ticker-posts

Wasa Da Namiji A Cikin Idda

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul Laah. Mace ce tana cikin iddan saki guda da mijinta ya yi mata shi ne ta yi wasa da namiji amma bai kai ga zina turmi da taɓarya ba! Shi ne take tambaya hukuncinta?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.

Abu ne sananne cewa wasan banza da maza haram ne ko mace tana da aure ko ba ta da aure. Haka ma idan auren ya mutu ta hanyar saki na ƙarshe wanda babu kome a cikinsa. Namiji ɗaya ne ya halatta mace ta saki jiki da shi su yi wasa ko da ma zai kai ga saduwa, shi ne: Mijin da aka ɗaura musu sahihin aure a ƙarƙashin dokokin Shari’ar Musulunci.

A bayan saki, ko shi mijin ma ba a yarda ta bari ya kusance ta ba a lokacin da take cikin iddar da ta ke akwai kome a cikinta, watau saki na-ɗaya ko na-biyu. Sai dai idan hakan da manufar yin kome ne, to wannan daidai ne, babu laifin komai. Yin hakan ma dalili ne a kan cewa ya dawo da ita, kamar yadda malamai suka faɗa.

Matar da take cikin iddar saki na-ɗaya ko na-biyu bai halatta wani ya nemi aurenta da kalmomin neman aure a fili ƙarara ba. Haka ma a ɓoye ta amfani da kalmomin jirwaye-da-kamar-wanka. Saboda akwai sauran haƙƙin mijinta a kanta, watau na yin kome a duk sadda ya ga dama.

Don haka bai halatta ba macen da take cikin irin wannan halin ta saki jiki har wani ya yi wasan jin daɗi da ita. Ko ba komai, idan da mijinta zai mutu a wannan lokacin to da kuwa iddar ta juye ta koma ta mutuwa, kuma da takaba ta hau kanta.

Wajibi ne ga macen da ta yi hakan ta tuba ga Allaah Ubangijin Halittu a kan hakan da sharuɗɗan da malamai suka shimfiɗa.

Amma idan a wannan halin saduwa ta auku a tsakaninta da abokin wasan da ba mijinta ba, ko da kuwa maniyyi bai fita wa ɗayansu ba, to ta lalata iddar tata kenan. Kuma sai ta faro ta daga farko bayan ta yi istibra’in da ya wajaba a saboda wannan saduwar. Waɗansu malaman su yarda wannan ce mafita gare ta a bayan tuba da istigfari.

Allaah ya ƙara mana shiriya. Ya sa mu iya kafewa a kan dokokinsa.

WALLAHU A'ALAM

Shiekh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments