Ticker

6/recent/ticker-posts

Soye-Soyen Zamani a Abincin Hausawa (Masa, Fankasau, Gurasa, Alkubus, Sinasir)

Gabatarwa

A babi na goma sha uku an tattauna bayanai kan wasu nau’o’in abincin suya na gargajiya tare da misalan yadda ake gudanar da su. Idan aka lura da yadda ake gudanar da wasu nau’o’in abincin suya na gargajiya, akwai kamanceceniya matu ƙ a game da yadda ake sarrafa wasu nau’o’in abincin suyar na zamani. A bisa wannan  dalili, a wannan babi,ba za a maimaita bayanan da aka riga aka gudanar a baya ba. A maimakon haka, za a ta ƙ aitu kan kawo kayan ha ɗ in da ke ƙ ar ƙ ashin kowane kawai. Daga cikin nau’o’in abincin suyar gargajiya da ke kama da na zamani akwai:

1. Masar gero

Kayan haɗi:

a. Albasa

b. Fulawa

c. Gero

d. Kanwa

e. Kayan yaji

f. Mai

g. Ruwa

h. Yis ko Nono

2. Masar Masara

Kayan haɗi:

a. Bakin foda

b. Fulawa

c. Gishiri

d. Kanwa

e. Kayan yaji

f. Mai

g. Masara

h. Ruwa

i. Ɓ ula

j. Yis ko Nono

3. Soyayyen Dankali

Kayan haɗi:

i. Dankali

ii. Gishiri

iii.Mai

i v . Ruwa

v .Yaji

Masar Shinkafa

Kayan haɗi:

a. Albasa

b. Gishiri

c. Kanwa

d. Mai

e. Ruwa

f. Shinkafa

g. Suga

h. Yis ko Nono

Da farko za a jiƙa shinkafar a wanke  ta, sannan a kai markaɗe. Akan iya sanya yis kafin a kai markaɗe. Idan kuma ana buƙata, za a iya bari har sai an dawo daga markaɗen ƙullun kafin a sanya. A gefe guda kuma za a dafa shinkafa. Daga nan za a kwaɓa wannan  ƙullun da dafaffiyar shinkafar da aka tanada, sannan sai a yanka albasa  a kai tare da gishiri. Bayan gishiri, akan iya ƙara suga kaɗan a kai. Wanda ba ya buƙatar yis yana iya sanya nono. Akan sa kanwa yayin kwaɓa ta domin gudun tsami . Da zarar an kammala ƙwaɓa ƙullun sai a ajiye domin ya kumbura. Da zarar ƙullun ya tashi, sai batun soyawa cikin tanda.

Funkasau

Kayan haɗi:

a. Albasa

b. Alkama

c. Fulawa

d. Gishiri

e. Kanwa ko yis ko nono

f. Mai

g. Ruwa

Za a wanke  alkama a shanya ta bushe, sai a niƙo ta, ana so garin ya yi laushi luƙwai. Sai a samu fulawa a tankaɗe a saman alkama daidai yadda ake buƙata. A gefe guda sai a jiƙa yis da ruwan zafi  a saka gishiri ɗan kaɗan da kanwa ko nono mai tsami , sai a kwaɓa da ruwan yis. A lura, kada ya yi tauri da yawa, ko ya yi ruwa-ruwa. Bayan an ƙwaɓa, sai a rufe a aje cikin rana ko a cikin kicin ( ɗ akin dafa abinci) domin ya kumburo. Wasu kuma sai ƙullun ya tashi suke saka gishiri da kanwa da albasa . Za a ɗora mai a wuta  a riƙa ɗebo shi da hannu ana sanya shi saman marfin wani abu ko faranti a faɗaɗa shi. Daga nan za a riƙa sanya shi cikin mai domin soyawa. Ga masu buƙata, ana iya sanya kayan yaji domin ƙara masa ƙamshi.

Funkasau na Fulawa

Kayan haɗi:

i. Fulawa

ii. Garin waken suya

iii. Gishiri

iv. Ruwa

v. Yis

Za a tankaɗe fulawa, sai a ƙ ara tankaɗe waken suya a kanta, sai a zuba gishiri daidai yadda ake bu ƙ ata a cakuɗa su sosai. Za a yi amfani da damammen ruwan yis ɗ in da aka tanada yayin kwaɓa shi. Sannan kar a manta, ana amfani da ruwan ɗumi ne yayin kwaɓa yis ɗin. Za a yi ta juya shi sosai domin ya haɗe yadda ake bu ƙ ata. Daga nan za a ajiye domin ya kumbura. Shi ma ana amfani da faranti ko wani abu mai faɗi yayin suya, tamkar dai yadda aka yi bayanin fankasau.

Alkubus

Kayan haɗi:

i. Bakin foda

ii. Fulawa

iii. Gishri

iv. Ruwa

v. Suga

vi. Yis

Za a tankaɗe fulawa, sai a zuba bakin foda (baking powder) da gishiri da suga daidai gwargwado. Daga nan sai a jiƙa yis da ruwan zafi  sannan a kwaɓa wannan  fulawar da shi. Yawanci akan samu ƙananan kofuna na musamman wanda da su ne ake dafa wannan nau’i na abinci. Bayan an sanya sai a jera su cikin tukunyar da aka sa ruwa, sannan a ɗora bisa wuta . Yayin da ya dafu, za a ji ƙamshinsa na tashi sosai.

Sinasir

Kayan haɗi:

i. Albasa

ii. Bakin foda ko nono

iii. Man gyaɗa

iv. Ruwa

v. Shinkafa

vi. Suga

vii. Yis

Za a sami shinkafar tuwo  a wanke , sai a jiƙa, sannan a kai ta markaɗe. Bayan an dawo da ita, sai a kwaɓa tare da yis da bakin foda ko nono. Za a zuba gishiri daidai gwargwado sannan a ajiye domin ta kumbura. Da zarar ta kumbura, sai maganar suya. Ana soya sinasir ne ta hanyar amfani da firayin-fan (fraying-fan). Za a riƙa sanya mai daidai gwargwado sannan a zuba wannan  ƙullu na sinasir da cokali ko wani ƙaramin ludayi. Ana cin sinasir da miyar sos. Miyar  za ta iya kasancewa ta alayyafu ko dage-dage da dai makamantansu.

Gurasa

Kayan haɗi:

i. Bakin foda

ii. Fulawa

iii. Gishiri

iv. Ruwa

v. Suga

Fulawa da suga da bakin foda za a haɗe wuri ɗaya a gauraya su sosai. Sai a tona tsakiya a zuba ruwa a kwaɓa da ƙarfi-ƙarfi sannan a ajiye domin ta tashi. Daga nan, za a naɗa ta kamar ziro sai a saka yatsa a tsakiya a huda, amma hujin ya kasance mai faɗi. Daga nan sai a ɗora tukunya  a saman wuta . Za a riƙa sanya ƙullun gurasar ciki ba tare da an sa mai ba. Da zarar gefenta guda ya gasu, sai a juya ta zuwa ɗaya gefen.

Kammalawa

Kamar yadda bayani ya zo a sama, akwai ire-iren abincin soyawa da yawa da Hausawa  ke ta’ammuli da su. Ko bayan haka, a har kullum ana ƙ ara samun sab ab bin fasahohin samfuran kayan soye-soye a ƙ asar Hausa

Citation (Manazartar Littafin):  Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

Get a copy:
To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
+2348133529736

You can also write an email to:

Post a Comment

0 Comments