Faten Dankalin Turawa
i. Albasa mai ganye
ii. Dankalin Turawa
(Airish)
iii. Gishiri
iv. Kayan yaji
v. Magi
vi. Mai
vii. Ruwa
viii. Tarugu
ix. Tattasai
A fere dankali, a yanka shi, sannan a wanke a ajiye a zuba mai a tukunya a soya jajjagen tarugu da tattasai da albasa. Idan sun soyu, za a zuba kayan yaji a ciki a saka magi da gishiri da kori. Daga nan sanwa in ta tafasa, sai a zuba dankalin Turawa a ɗan ƙara ruwa a yanka albasa tare da lawashin albasa. Akan ba shi lokaci mai ɗan dama idan ya yi, sai sauƙewa.
Faten Doya
i. Albasa
ii. Doya
iii. Gishiri
iv. Kayan ciki
v. Kayan yaji
vi. Magi
vii. Mai
viii. Ruwa
ix. Tarugu
x. Tattasai
xi. Zogale
Za a fere doya kamar yadda aka fere dankali, sai a wanke a aje gefe guda. Sannan za a tafasa kayan ciki tare da albasa da É—an gishiri kaÉ—an, amma ba tare da an sanya ruwa ba. Daga nan za a jajjaga tarugu da albasa da
tattasai a saka mai a soya. Idan ya soyu, za a saka kayan yaji da magi da gishiri a yi sanwa. Idan
sanwa ta É—auki lokaci sosai za a É—auko doya a saka tare da wanke zogale da gishiri kafin a saka. Idan ta É—an jima,
za a É—auko muciya a É—an daddaga
sama-sama a warwatse doya sai a É—auko kayan ciki a saka a ciki. Idan ta
ɗan ƙara dafuwa za a sauke, sai rabo.
Faten Makani
i. Albasa
ii. Gishiri
iii. Kayan yaji
iv.
Magi
v.
Mai
vi. Makani(gwaza)
vii. Ruwa
viii. Tarugu
ix.
Tattasai
Za a fere makani a aje gefe guda, sai kuma a jajjaga kayan miya a soya su a saka magi da gishiri da kayan ƙamshi a yi sanwa. Idan ta tafasa, sai a zuba makani a saka muciya a farfasa
kamar yadda aka yi wa doya. Sai a sauke tukunya.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.