Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Zan Iya Ce Masa Ina Son Sa?

TAMBAYA (61)

Aslm. Barka da dare. Zan yi tambaya. Idan naga namiji ina so zan iya fada masa?

AMSA

Waalaikumussalam, Warahmatullahi, Wabarakatuhum

Alhamdulillah. To yar uwa ba matsala bane ai mace ta ce tana son namiji saidai abin da ake so shi ne, son ya zamo don Allah ne ba don wata manufar ba

Saboda kyawawan halayen Annabi SAW ne ya sa Nana Khadija RA bint Khuwailid bint Asad bint Abdul-uzza, ta nemi shawarar qawarta Nafeesah, wadda a karshe dai ta zama silar auren Nana Khadija RA da Annabi SAW duk da cewar ta bashi shekaru 15 - a lokacin da take da shekaru 40 cif

(Duba littafin "Hazrat Sayyeda Khadija RA" (Tarihin Nana Khadija), wallafar Rashid Ahmad Chaudry), zaki ga bayanai daki-daki akan tarin miliyoyin kudinta bai sa ta ji kunyar neman auren Annabi SAW ba, kuma itace mace ta farko da ta fara musulunta (daga ita a cikin mata sai Lubabatu RA)

Don haka idan saurayin yayi miki kawai ki sanar dashi kai tsaye - kada ki biyewa rudin wawayen qawayennan da zasu dinga cewa ai zubar da aji ne hakan, sun manta da cewar duk jan ajin mace ta kama kafar kyakkyawar sahabiyar nan da ta auri mummunan sahabi Julaibeeb RA, saboda ta tabbata cewar Annabi SAW da yace ta aure shi bazai mata zabin tumun dare ba

(Siratun Naby)

Kuma kafin ki ce masa "I love you" yakamata ki fara addu'ar Istikhara domin bawa Allah SWT zabi, don gudun kada Allah yabarki da iyawarki

Wallahu ta'ala a'alam

Subhanakallahumma, wabi hamdika, ash-hadu anla'ilaha illa anta, astaghfiruka, wa'atubi ilayk

Amsawa;

Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ


Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments