Shin Mala'iku Na Tsinewa Mijin Da Ya Qi Amsa Buqatar Matarsa?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu Alaikum, malam dan Allah ina da tambaya, na kasance ina da sha'awa sosai kuma ba ni kaɗai ba ce gurin mijina, kuma duk sanda na nuna ina bukatarsa ba ya yadda, duk yadda nabi se yace bacci, kullum se dai in shi ne yake da bukata, kuma in na ki se na tuna da malaikun rahma za su kwana suna tsine min, shin dan Allah malam shi mala'iku ba sa tsine masa ne?? kuma wallahi yana jefani cikin wani hali duk idan na nuna ina da bukata ze kawo hujja mare karfi ya fada min.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salam, Lallai ƴar'uwa ya tabbata a hadisi ingantacce cewa duk matar da mijinta ya neme ta ta qi amsawa za ta kwana Mala'iku na tsine mata har zuwa safe. Amma ba a sami hadisin da ya nuna shi ma namiji idan matarsa ta neme shi ya qi amsawa cewa shi ma zai kwana Mala'iku na tsine masa ba. Kuma malamai ba sa qiyasta wannan hadisin a kan mijin da ya qi amsa kiran matarsa ba.

    Amma malamai sun tabbatar cewa duk wanda ya qi amsa kiran mayarsa don manufar cutar da ita, ko quntata mata, to wannan ya saɓa wa umurnin Allah a zamantakewar aure, saboda Allah Maɗaukakin Sarki ya ba da umurnin a mu'amalanci mata ɗa kyautatawa a Suratun Nisá'i, aya ta: 19

    يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا يَحِلُّ لَكُمْ أَن تَرِثُوا النِّسَاءَ كَرْهًا وَلَا تَعْضُلُوهُنَّ لِتَذْهَبُوا بِبَعْضِ مَا آتَيْتُمُوهُنَّ إِلَّا أَن يَأْتِينَ بِفَاحِشَةٍ مُّبَيِّنَةٍ وَعَاشِرُوهُنَّ بِالْمَعْرُوفِ فَإِن كَرِهْتُمُوهُنَّ فَعَسَىٰ أَن تَكْرَهُوا شَيْئًا وَيَجْعَلَ اللَّهُ فِيهِ خَيْرًا كَثِيرًا  

    Ku waɗanda suka yi imani! Ba ya halatta a gare ku, ku gaji mata a kan tilas kuma kadaku hana su aure domin ku tafi da sashen abin da kuka ba su, face idan suka zo da wata alfasha bayya nanniya kuma ku yi zamantakẽwa da su da alhẽri sa'an nan idan kun ƙi su, to akwai tsammanin ku ƙi wani abu alhali kuwa Allah Ya sanya wani alhẽri mai yawaa cikinsa. (Suratul Nisa'I aya 19)

    Kuma Allah Maɗaukakin Sarki a wata ayar ya bayyana cewa mata suna da haqqi kwatankwacin wanda yake kansu, a suratul Baqara, aya ta: 228

    وَلَهُنَّ مِثْلُ الَّذِي عَلَيْهِنَّ بِالْمَعْرُوفِ وَلِلرِّجَالِ عَلَيْهِنَّ دَرَجَةٌ وَاللَّهُ عَزِيزٌ حَكِيمٌ 

    Kuma su matan suna da kamar abin da yake a kansu, yadda aka sani. Kuma maza suna da wata daraja a kansu (su matan). Kuma Allah Mabuwayi ne, Mai hikima. (Suratul Bakara aya 228)

    Saboda haka wajibi ne a kan maza su riqa qoqarin  biya wa iyalansu haqqoqinsu na aure saboda taimaka masu wajen kaucewa faɗawa ga saɓa wa Allah S.W.T. Allah ya shiryar da mu.

    Allah ne mafi sani.

     Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.🏻

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.