Hukuncin Mijin Da Ya Kaurace Wa Matarsa A Wajen Saduwa

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum malam barka da yau Allah taimakeka don Allah malam mijine baya kusantar iyalinsa sai yayi sati shida ko biyar bai kusanci matar ba ko kuma idan tanaso ya kusanceta tayi masa magana akan hakki sai yaki kulata hartakai ga ranar tana cikin mugun sha'awa ta nuna buqatarta ya fita ya kyaleta ita kaɗai a matse shi ne ta matse  kafafunta ita kaɗai ta biyawa kanta buqata

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Walaikum sallam warahmatahi wabarkatahu

    Bai halatta haka kawai miji yakauracewa matarsa wajan kwanciya, indai bawai laifi tayi yakesan ladabtar da ita dahakan ba, idan laifi tayi yakesan ladabtar da ita da kaurace mata donta gyara halinta wannan ya halatta, amma shima iya saduwa ne haramun ne yace bazai bata kulawa ta magana da murmushi ko wasu abubuwa sama da kwana uku kamar yanda hadisi ingantacce ya haramta mutum musulmi ya kauracewa ɗan'uwansa sama da kwana uku.

    Indai saboda ladabtarwa ne ba haramun bane mutum ya kauracewa iyalinsa awajan saduwa kwanakin da yaga dama, saboda abubuwa guda biyu.

    Wajibine ga miji ya tausasawa matarsa yayi mata rangwame ya dunga saduwa da ita gwargwardon bukatarta gwargwadon ikonsa.

    An tambayi Shaikul Islam ibnu taimiyyah Alharrany Rahimahullah cewa: Dangane da miji idan zai iya hakuri da saduwa da iyalinsa wata guda ko wata biyu, shin yanada laifi ko bashi da laifi? shin miji zai iya neman hakan?

    Sai ya Amsa: Wajibi ne ga miji ya sadu da matarsa da kyautatawa, saduwa yana cikin mafi girman hakkinta akansa, yafi hakkin ciyar da ita dake kansa karfi, Saduwa wajibi ce, wasu sukace: wajibi ne acikin duk wata huɗu ya sadu da ita sau ɗaya, wasu sukace: A'a gwargwadon bukatarta da kuma ikonsa, kamar yanda zai ciyar da ita gwargwadon halinsa da ikonsa, wannan kuma shi ne mafi ingancin zantuka guda biyun.

    Majmu'u Fatawa(32/271).

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/CfDLSdXaGD00Wpxdfy2ofp

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.