Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wanda Ya Auri Mace Saboda Kyanta

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam, akwai wani hadisi da yake magana kan cewa wanda ya auri mace kawai dan kyanta Allah zai hana masa jin-daɗin kyan, ko don kuɗinta kawai Allah zai hana masa jin-daɗin kuɗin, shin wannan hadisin akwai shi kuma ya inganta?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Ga yadda aka faɗi hadisin duk wanda ya auri mace saboda kuɗinta, Allah zai kara masa talauci, duk wanda ya auri mace saboda kyawunta Allah zai kara masa muni, a cikin maruwaitan hadisin akwai Abdussalam bn Abdulkuddus wanda yake rawaito hadisan karya, don haka hadisin bai inganta ba, kuma ba za'a kafa hujja da shi ba.

Allah ne mafi sani.

Amsa daga Dr. Jamilu Yusuf Zarewa.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments