Ticker

6/recent/ticker-posts

Matar Auren Da Take Waya Da Besty

TAMBAYA (60)

Assalamu Alaikum. Ina yini malam. Dan Allah Malam ina da tambaya mene hukuncin matar auran datayi Besty Kuma Suna waya kuma sunayin chat. Kuma ba ɗan uwan tah bane ba muharramin tabane

AMSA

Bai halatta ta dinga kebewa da wani Besty har ma su dinga waya ko chatting, saboda ba halayya ce ta Mar'atus Saliha ba saboda wannan zai zama silar budewa shaidan kofa wanda karshen al'amarin shine da na sani (wato zina)

Allah SWT yace;

( وَلَا تَقْرَبُوا الزِّنَا ۖ إِنَّهُ كَانَ فَاحِشَةً وَسَاءَ سَبِيلًا )

الإسراء (32) Al-Israa

Kuma kada ku kusanci zina. Lalle ne ita ta kasance alfãsha ce kuma tã mũnãna ga zama hanya.

Wannan wayar da suke hanyace da take bayyana kusantuwa zuwa ga aikata zina kuma a dabi'ance sannan a al'adance ma bai dace ba ballantana kuma a addinance

Tabbas duk ranar da asirinta ya tonu, indai har mijinta yana da kishi to bazai ji dadin hakan ba, to indai har mijin ta bazai so ba ina kuma ga wanda ya haramta hakan

Ya kamata mata su gane cewar shi fa aure ba abune na wasa ba, kuma duk ana samun irin wannan matsalar ne tun daga hanyoyin da ake bi wajen neman auren har zuwa lokacin da mutum zai je makarantar koyon zaman auratayya

Mun tsinci kanmu a wani zamani wanda idan da zaka jera mataye da mazajen aure 10 to da kyar ka samu 3 wadanda zasu nuna maka shaida wato certificate din da suka samu na zuwa makarantar koyon zamantakewar aure

Wannan qalubale ne a garemu baki daya

Akan wannan gaba ya dace na ja hankalin gwauro da gwauruwa da sauran ma'aurata cewar ya zama wajibi mu dinga karanta littattafan addinin musulunci musamman wadanda suke da alaqa da rayuwar auratayya

Domin sanin mu'amalar auratayya a addinance sai a karanta ko a koyi littafin "Guidelines To Intimacy In Islam" (Tafarkin rayuwar auratayya a musulunci), wallafar Muhammad Shoiab Ibn Ibrahim Adam (Kamar yanda Mufti Muhammad Ibn Adam Alkhawthary ya fitar a littafinsa), wanda littafi ne da ya tattaro bayanai da hujjoji daga Qur'ani da Hadisai akan yanda ake rayuwar mu'amalar aure, kamar yanda Annabi SAW ya yi ga iyalansa su Nana Aisha RA da sauransu

Sai kuma aje a koyi wani littafi wanda Imam Ibn al-Qayyim al-Jauziyya (Rahimahullah) ya rubuta mai suna; "Newborn Baby Guide" {Tuhfatul Maudud bi ahkam al-Maulud} (Shiriya ga jariri), a ciki yayi bayani daki-daki akan hanyoyin da ake bi don samun da nagari har zuwa abin da za'ayi bayan an haifeshi, ya rubuta littafin ne a matsayin kyauta ga yar uwarsa wadda talauci ya sa bai iya siyan tsaraba ga jaririn da ta haifa ba, sai ya rubuta littafin a matsayin tsaraba ga yan uwa musulmi baki daya

Haka kuma ya kamata a koyi littafin: "Natural Blood of Women" (Hukunce-hukuncen jinin mata) wallafar Shaykh Muhammed Ibn Saleh al-Uthaymeen (Rahimahullah), wanda abin kunya da takaice sun kare ga macen da ta yi aure amman daga ita har mijinta ba su san menene banbanci tsakanin jinin Istihadah da jinin Nifass ba

Sannan kuma dai akwai wani littafi da maza yakamata su karanta mai suna: "Men Around The Messenger, SAW" {Rijalu Haulal Rasul} (Maza A Kewaye Da Ma'aiki SAW), wallafar Khalid Muhammad Khalid, su kuma mata sai su karanta: "Women Around The Messenger, SAW" {Nisa'u Haulal Rasul} (Yanda Mata Suke Koyi Da Ma'aiki, SAW), wallafar Muhammad Ali Khutb

Sannan kuma uwa uba shine mu koyi sallah kamar yanda Annabi SAW ya koyar, da fadinsa SAW "Sallu kama ra'ayta muni usalli" bi ma'ana "Kuyi sallah kamar yanda kuka ga ina yi", domin kuwa duk wanda yake sallah to dayan abu biyu ne; in ma dai a a'adance yake yi (wato ya gani ana yi ne shima yake kwaikwayo) ko kuma a sunnance ta hanyar karanta littafin "Sifatu Salatin Naby" {The Description of the Prophet's Prayer} (Suffar yanda Annabi SAW yake sallah) wallafar Shaikh Muhaddith, Mujaddid Muhammad Ibn Nuhu Nasiriddin Albany (Rahimahullah). Ya kawo yanda Annabi SAW ya koyar da sallah da hujjoji a cikin sahihan hadisai

Don hakan wadannan sune a taqaice shawararin da zan baki tare da sauran gwauraye. Muna roqon Allah ya bamu abokan zama nagari wadanda zamu zauna tun anan duniya har zuwa gidan Aljannah

Wallahu ta'ala a'alam

Amsawa;

Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments