Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Cin Yankan Ahlul Kitabi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Ko cin yanke-yanken Kiristoci a wannan zamani namu na yau yana halatta, duk kuwa da cewa hanyoyin yanka a wurinsu sun yawaita, watau kamar yin amfani da injuna, da kuma abubuwa masu daskarar da kwakwalwa a wurin yankan?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Cin yanke-yankensu yana halatta, matukar dai ba a san da cewa an yanka dabbar ne ta hanyar da ba ta dace da Shari'a ba, saboda asalin lamari shi ne halaccin cin sa, kamar dai yankan musulmi, saboda faɗin Maɗaukaki: Da abincin waɗannan da aka ba su littafi halal ne yake a gare ku, kuma abincin ku halal yake gare su)).

Sheik Uthaimeen ya ce cikin littafinsa Ash-Sharhul Mumtii 12/148:-

ﻓﺎﻟﺤﺎﺻﻞ : ﺍﻥ ﺍﻟﺬﻱ ﻋﻠﻴﻪ ﺟﻤﻬﻮﺭ ﺍﻫﻞ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﺍﻥ ﻣﻦ ﺗﺪﻳﻦ ﺑﺪﻳﻦ ﺍﻫﻞ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻧﺘﺴﺐ ﺍﻟﻴﻬﻢ ﻭﻟﻮ ﻛﺎﻥ ﻳﻘﻮﻝ ﺑﺎﻟﺘﺜﻠﻴﺚ ﻓﺎﻧﻪ ﺗﺤﻞ ﺫﺑﻴﺤﺘﻪ، ﻭﻳﺤﻞ ﻧﻜﺎﺣﻪ

Ma'ana: ((A takaice dai: Abin da majoratin masu ilmi suka ce shi ne duk wanda ya yi Addini da addinin Ahlul kitabi, ya kuma danganta kansa zuwa gare su koda kuwa yana cewa Allah uku ne, to lallai ne cin wannan yankan halal ne, kuma auren su halal ne)).

Sa'annan Al Imamul Dabarani, Abul Dar'da, wata an yi masa Fatawa akan cin Yankan Kirista, suka ce masa Kiristoti ne suka yanka Dabba daga Coci Suka kawo mana shin ya halatta mu ci? sai da ya girgiza kansa yace Allah yafe mana, sai ya tambaye su shin su ɗin ba Ahlul-Qitabbi bane? Sai suka ce ahlul-qitab ne,  sai yace ai Abincin su halal ne, sabida haka cewar ba'a San ya suka yanka ba a Ina suka yanka, duk wannan ba hujja bane na nuna Haramcin cin sa ba. Kawai in kana Bukata ka ci in ba ka Bukata ka bari, shikenan shin ba Allah ya halatta mana cin abin Yankan su ba? Mun yi bayanin Ayar jiya a Dayan Fatawar mu, sa'annan Duk Imanin ka duk Tsarkin ka duk Kyan-Kyamin ka, shin mun Kai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam ne? Duk Ayar da mutum zai karanta ko ya fassara ka tsaya ka dubi ya rayuwar Annabi yake?

Har kullum Ahlus Sunnah wal Jama'ah a duk inda suke suna gina Addinin su ne a kan abin da ya tabbata daga Alkur'ani Mai girma da kuma ingantattun hadithan Annabi mai tsira da amincin Allah masu daraja. Amma sabanin su, su kan gina Addinin su ne kawai a kan abin da ya dace da son zuciyar su.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Fb6qgYPXfEeHb8CD1SWAkK

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments