Ticker

6/recent/ticker-posts

Marigayiya Hajiya Rakiya Bagobira, Jakadiyar Marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji (Dr.) Shehu Idris

Marigayiya Hajiya Rakiya Bagobira
Marigayiya Hajiya Rakiya Bagobira, Jakadiyar Marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji (Dr.) Shehu Idris, Allah ya kyauta makwanci, amin. Ita ce wacce/wadda Makaɗa Sa'idu Ango Maidaji Sabon Birni ke ambata a cikin Waƙoƙin da yi yiwa Marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji (Dr.) Shehu Idris. Kasancewar ta Bagobira /Daga Tsatson Gobir/Gobirawa a Fadar Masarautar Zazzau kuma a lokacin mulkin Sarakunan Fulani ana iya cewa Tarihi ne ya maimaita kan sa domin ko a lokacin mulkin Amirul Muminina Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi ya yi Jakadiya Bagobira da ake kira Yar Gurma Fatima wadda/wacce ta zauna a Fadar Gobir a matsayin Jakadiya a lokacin mulkin Mai Martaba Sarkin Gobir Yunfa. Mai arziki ce matuƙa saboda ko a lokacin da take Jakadiyar Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ance ta mallaki Bayi 40. Allah ya jiƙan magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin. 

Daga Taskar:
Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

Post a Comment

0 Comments