Ticker

6/recent/ticker-posts

Jakadiya Hajiya Fadimatu Binta

Jakadiya Hajiya Fadimatu Binta

"Jakadiya zauna bari kuka Aminu dai/ne na nan bai kau ba" 
Inji Dr. Mamman Shata Katsina a faifansa na Marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dr. Shehu Idris mai amshi 'Alhaji Sarkin Zazzau Shehu'. 
Wannan ita ce Jakadiya Hajiya Fadimatu Binta, Jakadiyar Marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Muhammadu Aminu wadda Dr. Mamman Shata Katsina ya yiwa wannan kalamin. Ta na nan a raye, Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana mai albarka, ya jiƙan magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.
Daga Taskar:
Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

Post a Comment

0 Comments