Ticker

6/recent/ticker-posts

Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Abubakar III Ne Sanadiyyar Kiran Alhaji Salihu Mai Buhu Gummi Da Wannan Alkunya/Laƙabi Na "Mai Buhu".

Ga yadda abun ya faru. Wani lokaci ne a cikin 1970s, En'a ta Sakkwato (Sakkwato Native Authority, NA) ta buga Tanda(Tender) ta wasu ayyukan kwangiloli, yan kwangila da dama suka yanki wannan Tanda ciki kuwa har da wannan bawan Allah da muke magana akai.

Bayan an fitar da sunayen yan kwangilar da suka samu nasara sai wannan bawan Allah ya tafi ya duba ko sunansa ya fito. Aka yi sa'a kuwa ya ga suna "Salihu Gummi" a cikin tsarin sunayen yan kwangilar da Allah SWT ya baiwa nasara.

Sai kuma aka yi rashin sa'a su biyu ne masu wannan suna na Salihu Gummi suka zo daga Gummi domin duba sunayensu su kuma karɓi takardar kama aiki.

Tandan Tandan Tandan!!! Idan aka kira Salihu Gummi sai duka su biyun su karɓa. A cikin hikimarsa da ya saba sakawa cikin lamurran mulki sai Mai Alfarma Sarkin Musulmi Abubakar III, Allah ya kyauta makwanci, amin ya ce wa wancan Salihu Gummi (wanda  ya fi wannan Salihu Gummin da muke magana akai yawan shekaru a duniya) "Kai mi as sana'ak ka, ka kau cika wagga Tanda? Ya amsa masa cewa " Allah shi baka nasara sana'ag goro nikai, kuma tabbas na yanki Tanda ".

Ya juya akan wannan Salihu Gummi da muke magana akai ya ce " Kai Samari wace sana'a ka kayi, ka kau yanki Tandag ga? Ya ce masa " Saye da sayar da hatci ni kayi, kuma na yanki Tandaw wanga aiki, Allah ya taimake ka".

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Abubakar III ya dube su, ya ce tau zan kashe wagga gardama. Kai Salihu da ad da shekaru da yawa an baka wanga aiki, daga yau kuma sunan ka Salihu Mai Goro Gummi. Ya juya wajen Salihu Gummin da muke magana akai ya ce "Kai kuma in Allah yaso zan samo maka naka aikin kuma daga yau sunan ka Salihu Mai Buhu Gummi".

Haka kuwa aka yi, domin ya samo masa aikin ginin Makarantar Furamare ta garin Illelar Awwal dake cikin gundumar Gummi. Daga lokacin ne kuma ya ci gaba da ansa wannan alkunya/laƙabi na "Mai Buhu" a cikin sunansa.

Wannan shi ne Alhaji Salihu Mai Buhu Sarkin Yaƙin Gummi, Ajiyan Zamfara, Ɗan Kasuwa, Ɗan Kwangila kuma Ɗan Siyasa. Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana mai albarka, amin.

Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara, Nijeriya.

08149388452, 08027484815.

birninbagaji4040@gmail.com

Talata, 30/01/2024.

12:54 Na Rana.

Post a Comment

0 Comments