Ticker

6/recent/ticker-posts

Zo-Mu-Gaman Addini Da Siyasa; Kebantaccen Nazari Kan Sa-In-Sar Malaman Addini Na Zamfara Da Gwamnatin Zamfara

 Takardar ƙara wa juna sani da aka gabatar a ajin ALH 400: Seminars, a Sashen Nazarin Harsuna Da Aladu, Jamiar Tarayya Gusau, Nijeriya, (2022/2023 Academic Session).

Federal University Gusau (FUG) Nigeria

Zo-Mu-Gaman Addini Da Siyasa; Kebantaccen Nazari Kan Sa-In-Sar Malaman Addini Na Zamfara Da Gwamnatin Zamfara

NA

MUHAMMAD ABDULKADIR

LAMBAR RIJISTA: 1810104018

LAMBAR WAYA: 08109016443

KIBƊAU: laddongusau@gmail.com

Tsakure

Wannan aiki ya mayar da hankali ne a kan gano ayyukan malaman addinin Musulunci a majalisar malamai (Shura), da kuma a hukumomi da kwamitocin lamurran addinin na gwamnatin Jahar Zamfara; ya kuma bayar da matuƙar muhimmanci kan gano tare da bayyana yadda suke aiwatar da wasu daga cikin ayyukan nasu dangane da ma'aikatunsu da kwamitotansu.

1.0 Gabatarwa.

Tarihi ya nuna cewa, kafin aikowa da Annabawa, mutane na rayuwa ne irin ta dabbobi; zuciyar ɗan Adam ita ce gaba yana biye. Don canza wannan tsari ne, Alla maɗaukakin sarki Ya zaɓi ɗan Adam daga cikin sauran halittu, ya yi masa ni'imar hankali da tunani, ya aiko shi a matsayin manzo. Isowar saƙon Alla (S.W.A) ke da wuya, sai ɗan Adamu ya wayi gari cikin haske bisa haske; hasken hankali da hasken naƙali. Watsuwar hasken ayyukan manzanninsa faɗin duniya ke da wuya, sai ya samar da wani irin yanayi a bayan ƙasa, na aminci da adalci. Domin tabbatar da wannan aminci da adalci ne, daulolin musulunci, a tsawon tarihinsa, suka kakkafa waɗansu hukumomi da za su taimaka a kan haka. Wannan takarda ta kalli tarihin irin waɗannan hukumomi ne a taƙaice, a zamunnan da bayyana ma'anar Shari'a, manufofi da matuzganta da kuma dacewarta da kowane irin yanayi da lokaci da zamani, da wasu abubuwan da suke da alaƙa irin ta jini da tsoka da Shari'a. Daga bisani kuma ta nuna irin yadda aka samar da irinsu a jahar Zamfara bayan farfaɗo da sake aiki da tsarin shari'ar Musulunci a jahar, inda ta bayyana kafuwa da ayyukan kowace hukuma. Manufar hakan kuma ita ce, abin ya zama wani kundi na tarihi da nazari ga manazarta da sauran masu sha'awa.

1.1 Dubarun Bincike

Duba littattafan da hukumomin gwamnatin suka buga na ayyukansu da cigaban da suka samu.

Hira tare da wasu tsofaffin ma'aikatan waɗannan hukumomi da kwamitoci.

2.0 WAIWAYEN KALMAR MALAM

Kalmar 'Malam' na nufin, wanda yake da sani kan wani abu, sannan ya sanar ko ya koyar da wani ko wasu mutane wannan abu.

Kalmar 'Malamai' jam'i ne na kalmar malam.

 Malamai magada-annabawa, shi ne kirarin da al'umma ke yi wa malamai a lokacin da ya gabata, saboda tsoron Allah da suke da shi da kiyaye haƙƙoƙan Allah, da gudun duniya.

2.1 Ayyukan malamai a da;

1.      Jagorantar salla a masallaci

2.      Yin zanen suna, idan aka haihuwa

3.      Ɗaurin aure

4. Jagorantar sallar Jana'iza, da sauran abubuwan da suka shafi addini.

5. Yin wa'azi (musamman a Ramadana)

2.3 Malamai a yau;

Idan tsoho bai ji kunyar hawan jaki ba, jaki ba zai ji kunyar tutsu da shi ba.

Al'umma ba sa ganin girman malamai, sannan raini ya shiga tsakaninsu, har ta kai zagi da kalamai marasa daɗi na shiga tsakanin malamai da al'umma. Sakamakon sakin tsohuwar hanyar da aka san su (malamai) da ita, suka canza suka koma, goyon bayan ƙaryata ga fili, ƙwaɗayin abun duniya da babban abun da shi ne ya fi zubar musu da ƙima a idon al'umma, shi ne shiga harkokin siyasa da malaman wannan zamani suka yi.

3.0 MAJALISAR SHURA TA MALAMAI

 Yana da wuya matuƙa a samu wani littafi daga cikin littafan da ke magana a kan tsarin gwamnatin Musulunci, wanda bai nuna muhimmancin kafa Majalisar Shawara ba (shúrá). Samar da wannan majalisa ma, a wurin Malam Abul-a'alal maudúdí dole ne, kafin tsarin gwamnati ya karɓa sunan tsarin Muslunci (Mandudi: 1960:58).

Kamar yadda bayani ya tabbata Alla (S.W.A) Shi Ya umurci manzon Alla (S.A.W) da yin shawara da sahabbai (3/159). A kan wannan umarni ne, manzon Alla (S.A.W) ya kafa Majalisar shawara ta farko a tarihin Musulunci. Bayan "bai'atul aƙba" ta biyu, manzon ya hori mutanen Madina da cewa, su zaɓo manyan mutane guda goma sha biyu daga cikin ku, waɗanda za a riƙa yin shawara da su a kan duk abin da ya shafi jama'arsu, Ka'ab ɗan Malik ya ce: "Sai suka zaɓo mutum tara (9) daga cikin Hazraju, uku (3) kuma daga cikin Asusun." Bayan da kuma gwamnati ta zauna da gindinta a Madina, nan take sai Manzon Alla (S.A.W) ya yi wa waccan majalisa gyaran fuska, ta hanyar baje ta, da zaɓo magabata bakwai (7) daga cikin muhajirun. Waɗannan su ne suka zama 'yan majalisar shawara ga Manzon Alla (S.A.W) a wannan lokaci (Khálidi, 1984: 132-134).

Waɗannan 'yan majalisa, gaba ɗayansu mutane ne masu ilimi mai zurfi na addinin musulunci da godewa a fagen rayuwa. Makusanta ne na ƙud-da-ƙud ga Manzon Alla (S.A.W) kuma zaɓaɓɓu daga cikin almajiran makarantarsa. Gudunmawar da suka bayar ga cigaban addini, ta sa gaba ɗayan musulmi (Sahabbai) ke matuƙar son su da girmama su, ta yadda da za a gudanar da zaɓe don fitar da 'yan majalisar manzon Alla (S.A.W) to, babu shakka su za a zaɓo. Dr. Abdulƙadir ya kawo jerin sunayen wasu daga cikin waɗannan mutane da suka haɗa da:

a. Abubakar Siddiƙ (R.A)

b. Umar ɗan Khaɗɗabi (R.A)

c. Usman ɗan Affanu (R.A)

d. Aliyu ɗan Abu Ɗalib (R.A)

e. Sa'ad ɗan Ubadata (R.A)

f. Sa'ad ɗan Mu'azu (R.A)

g. Abdurrahman ɗan Aufi (R.A)

h. Zubairu ɗan Auwam (R.A)

i. Zaidu ɗan Harisata (R.A)

j. Usamata ɗan Zaidu (R.A)

Wannan majalisa ita ce ta ci gaba da zama makomar Halifofi a Madina bayan rasuwar manzon Alla (S.A.W) a cikin duk abin daɗi ya shafi rayuwar al'umma, har da wadda ta keɓance su da iyalinsu (Al-Farusi; 1984:114).

 Kamar yadda tsarin shari'ar Muslunci ya al'adanta na barin ƙofa buɗe, ga al'amurran siyasarsa su tafi gwargwadon yadda zamani ke tafiya, ta fuskar gudanarwa, da tabbata a kan turbar ingantattar aƙida, babu wata takamaimar siffa da tsarin da ya daddale don gudanar da majalisar sahwara ko da kuwa ta fuskar addini 'yan majalisa ne, zaɓen su da dabarun aiki. Muhimmin abu dai shi ne samar da 'yan majalisar, su kuma yi aiki don tabbatar da haƙƙoƙan Alla da na bayinsa ta hanyar bayar da shawara (Farisa, 1984:108,109). Amma duk da haka, a dunƙule malamai sun keɓe wasu ɓangarora guda biyu da majalisar shawara ke da haƙƙin tsoma baki kamar haka

i. Hukunce-Hukuncen Ijtihadi:

Duk al'amurran da babu takamammen nassi wanda ke nuna hukuncinsu ƙarara, ko nassosan da ke iya ɗaukar fahimta fiye da ɗaya, ko aka bayar da zaɓi a cikinsu, ko malamai suka yi hidima mai yawa a cikinsu, majalisa na da damar tsoma baki a cikin irin waɗannan, haka kuma;

i. Hukunce-Hukuncen Ijtihadi:

Duk al'amurran da babu takamammen nassi wanda ke nuna hukuncinsu ƙarara, ko nassosan da ke iya ɗaukar fahimta fiye da ɗaya, ko aka bayar da zaɓi a cikinsu, ko malamai suka yi hidima mai yawa a cikinsu, majalisa na da damar tsoma baki a cikin irin waɗannan, haka kuma;

ii. Al'amurra Siyasa:

Kamar ɗauka yaƙi, irin na neman zaɓe, da ƙulla amana ko yanke alaƙa, da sarrafa dukiyar gwamnati, da duk wani abu da aiki da ra'ayin mutum ɗaya a cikinsa, na iya jefa al'umma a cikin fitina da ruɗani ko ya zubar da mutuncin wani shugaba. Irin waɗannan abubuwa duk sai majalisa ta zauna. (Mubarak, 1989:35).

 Haka irin wannan tsarin na samar da majalisun shawara ya ci gaba da wanzuwa a gwamnatocin da aka yi na Musulunci a faɗin duniya.

 A nan bay-baya kuma, daular Usmaniyya ta Sakkwato, majalisar shawara ta sarkin musulmi Muhammad Bello (1817-1838) ta haɗa manyan mutane masu ilimi da ƙwazo da jaruntaka, waɗanda suka haɗa da

Galadima Digiri

Abubakar ɗan Jada

Ubandoma Muhammad.

Aliyu Jedu (Shagari/Boyd, 1978:51)

Sambo ɗan Ashafa (Gusau 1984:50).

 Kafin zuwan Turawan Mulki a ƙasar nan, irin wannan majalisar ce ta ke gudanar da duk irin abubuwan da majalisar dokoki da ta dattijai ke gudanarwa a yau. Zaman samar da irin wannan majalisa wajibi, ga gwamnatin da ke tafiya da a kan tsarin Musulunci ya sa gwamnan Jahar Zamfara Alh. Ahmad Sani ya kafa majalisar shawara ta malamai tun lokacin da ya ƙaddamar da shari'a a jahar, wadda dokar gwamnatin jaha mai lamba 16, wadda ta fara aiki ranar 28th ga watan Juli 2003 ta ƙarfafa ta kuma inganta. Daga cikin abubuwan da wannan doka ta tanada akwai cewa

- Kada Mambobin wannan majalisa su ƙasa 17 ko su wuce 31. Kuma dole su zama daga cikin gogaggin malaman Fiƙihun musulunci da rayuwar yau da kullum. Haka kuma lallai ne kada a kasa zaɓo malamai goma (10) daga cikin Jaha, 5 kuma daga wajenta.

- Duk abinda waɗannan mambobin za su zartar a majalisar, lallai ne ya alamta fahimtar gaba ɗaya ƙungiyoyin addinin da ke jahar, da sauransu.

 3.1 Ayyukan da gwamnati ta ɗora wa wannan majalisa kuma, sun haɗa da

i. Zaunawa taro alal'aƙalla sau ɗaya a kowane wata, don karɓa tambayoyi daga gwamnati ko kotuna ko ma'aikatu ko wasu mutane, a kan abin da ya shafi dokokin musulunci, Fiƙhu, ko don tattauna wasu matsaloli.

ii. Sa ido tare da auna yadda aiwatar da Shari'ar Muslunci ke gudana a jaha, tare da bayar da shawarwari a kan matakan da ya kamata gwamnati ta ɗauka don kyautata al'amurran.

iii. Harhaɗa sakamakon bincike-binciken ƙere-ƙeren zamani da sauran al'amurran rayuwa, tare da dubon su da tabaran musulunci.

iv. Ba gwamnan jaha shawara a kan dacewa ko rashin ta a idon Shari'a, a kan duk wata doka da majalisar dokokin jaha ke son tabbatarwa.

v. Yin duk wani aiki da zai bijiro wa majalisa.

Wannan majalisa ba ta da wani iko wanda ya wuce na bayar da shawara a cikin gaba ɗaya waɗannan ayyuka da aka ɗora mata. Kafin gwamnatin jahar Zamfara ta naɗa mace, a karo na farko a matsayin 'yar majalisar zartarwa a shekarar 2003, sai da ta nemi shawarar majalisar (Hira: A.U. Kanoma, 2006). Babu laifi a tsarin Musulunci mace ta zama 'yar majalisar zartarwa. Hasali ma yin haka ya kamata matuƙa, don ta wakilci 'yan uwanta mata a wurin (Khálidi, 1984:135).

Bayan waɗannan hukumomi da kwamitoci kuma, gwamnatin jahar Zamfara a ƙarƙashin wannan tsari, ta kafa waɗansu hukumomin don bunƙasa rayuwar al'umma

4.0 Hukumomin gwamnatin da wasu ayyukan yyukan malamai a Hukumomin.

4.1 Ma'aikatar Lamurran Addini

An kafa wannan ma'aikata ne sakamakon dawowa da aiwatar da tsarin shari'ar Musulunci. Babban maƙasudin samar da ita kuwa shi ne, domin ta kula da ganin an aiwatar da tanade-tanaden wannan tsari kamar yadda ya dace ya kuma kamata; da kuma sauran duk waɗansu al'amurra da suke da alaƙa da addinin a jahar. A daidai lokacin da aka kafa ta, ma'aikatar lamurran addini, an samar mata da sasanni da rassa da suka haɗa da

v  Sashen Mulki

1)      Sashen kuɗi da saye-saye,

2)      Sashen Wa'azi da Da'awa

3)      Sashen Al'amurran Addini,

4)      Reshen inganta karatun Alƙur'an,

5)      Reshen karɓar Zakka da;

6)      Reshen hardar Alƙur'ani.

Ayyukan kuma da wannan Ma'aikata take gudanarwa daga lokacin da aka kafa ta zuwa yau, sun haɗa da:

·      Shirya wa'azin Mako-mako,

·      Gina masallatai da makarantun islamiyya,

·      Bayar da gudunmawar kuɗi ko kayan aiki domin kammala wasu masallatai da makarantun islamiyya,

·      Samar da abincin buɗe baki ga malamai da almajirai da sauran mabuƙata a cikin watan Ramalana,

·      Ɗaukar nauyin malamai masu gudanar da tafsiri a lokacin azumin Ramalana,

·      Shirya wa tare da ɗaukar nauyin gudanar da sallar tahajjud a masallatai daban-daban na faɗin jaha a lokacin azumin watan Ramalana.

·      Samar da shanun jajibiri ga malamai da almajirai da sauran jama'ar gari a lokacin babbar salla.

·      Tallafa wa malamai da mabuƙata da ragon layya a lokacin babbar salla.

·      Tallafa wa makarantu da cibiyoyin addinin Musulunci domin shirya tarukan gargaɗi da faɗakarwa a faɗin jaha,

·      Samar da littafan addinin musulunci da sauran fannoninsa na ilimi da wayewa, tare da rarraba su ga ɗalibai da sauran masu sha'awar karance-karance a faɗin jaha.

4.2. Hukumar Hana Cin Hanci Da Rashawa,

An kafa wannan Hukuma ne a ƙarƙashin dokar hana cin hanci da rashawa ta jaha, wadda ta fara aiki a ranar 28th July, 2003. Taken hukumar kuwa shi ne "Ba wanda ya fi wani a gaban Shari'a"

Maƙasudin kafa wannan Hukuma shi ne yaƙar cin hanci da karɓar rashawa a cikin al'umma da ma'aikatun gwamnati ta hanyar sa ido a kan yadda ake shiryawa da aiwatar da kwangiloli, kula da ɗa'a da tarbiyar jami'an gwamnati ta fuskar tsare aiki, gaskiya da riƙon amana da makamantansu. Haka kuma aikin hukumar ne shiga tsakanin talakawa da gwamnatin ƙananan hukumomi, da sarakunan gargajiya da ma'aikatar Shari'a, da 'yansanda, da ƙungiyoyi masu zaman kansu.

Wannan hukuma na gudanar da aikinta, ta hanyar kwato wa mai ɗan karfi haƙƙinsa daga ɗayan waɗannan wurare da aka ambata a sama. Wasu lokutan ma takan yi tsaye ta ga gwamnati ta hukunta azzalumin, ko da hakan za ta raba shi da aikinsa, don a tsarkake al'umma. Haka kuma idan wani ya zalunci ɗaya daga cikin hukumomin, wannan hukuma kan tsaya kai da fata ta ƙwato wa hukumar haƙƙinta.

Duk irin waɗannan matsaloli, aikin wannan hukuma ne ta magance su. Allah (S.W.A) na cewa: "Lalle ne Allah yana umurnin ku, ku bayar da amanoni ga masu su..." (4:58)

4.3 Hukumar Zakka Da Waƙafi

 Zakka ita ce abu na biyu da Allah (S.W.A) Ya wajabta wa musulmi, daga cikin tsarin shikashikan musulunci guda biyar. Allah (S.W.A) na cewa: "Kuma ku tsayar da sallah, kuma ku bayar da Zakka, kuma abin da kuka gabatar domin kanku daga alheri (waƙafi) za ku same shi a wurin Allah." (2:10).

A tsarin shari'ar Muslunci, gwamnati ce ke da haƙƙin karɓo Zakka daga hannun mawadata da nufin tsarkake su, tare da rarraba ta ga talakawansu, da nufin cike giɓin da ke tsakaninsu na tattalin arziƙi, don kawar da ƙyashi a tsakaninsu. A kan haka ne Allah (S.W.A) Ya ce wa Manzon rahama (S.A.W) "Ka karɓi sadaka (Zakka) daga dukiyoyinsu, ka tsarkake su. Kuma ka tabbatar da kirkinsu...." (9:103).

A kan wannan umurni ne, shi kuma Manzon Allah (S.A.W) ya gaya wa Mu'azu ɗan Jabalu, a lokacin da ya tura shi Yaman, cewa: "Ka sanar da su cewa kuma, haƙiƙa Allah Ya farlanta sadaƙa (Zakka) a kansu za a karɓe ta daga mawadatansu a ba talakawansu" (Buhari da Muslim/ Kardhawi, 1985-241). Malam Mawardi Bashafi'e ya ce: "Sadaka na nufin Zakka, Zakka kuma na nufin sadaka, abu ɗaya ne aka ambata da sunaye daban-daban." (Kardhawi, 2001:40). Saboda muhimmanci da Zakka ke da shi ne, a tsarin gwamnatin Musulunci, Gwamnatin jahar Zamfara ta kafa wannan hukuma ta karɓar Zakka da Waƙafi, a ƙarƙashin dokar gwamnatin jaha mai lamba 13, ta ɗora mata nauyin karɓo waɗannan haƙƙoƙa daga wurarensu tare da rarraba su a inda suka dace.

 Don tabbatar da wannan guri ne, Gwamnatin ta zaɓo amintattu daga cikin ma'aikatan gwamnati da 'yankasuwa da malaman addinin Musulunci, a matsayin mambobin hukumar. Wannan hukuma nada sassa guda biyar kamar haka:

·         Sashen Ƙarɓowa

·         Sashen Rarrabawa

·         Sashen Waƙafi

·         Sashen Mulki, da;

1.      Sashen Kuɗi

Har wa yau kuma hukumar ta rarraba ma'aikatanta zuwa wasu ƙananan kwamitota kamar haka

1.0  Kwamitin Fatawa

2.0  Kwamitin Bincike

3.0  Kwamitin Kasuwa

1)      Kwamitin Tallafin Gaggawa

·         Kwamitin Ma'aikata

4.4 Hukumar Kula Da Wa'azi Da Kafa Masallatan Juma'a Da Na Idi:

Gina masallatai da tsare alfarmarsu, tare da gudanar da ayyukan ibada, da wa'azi da karantarwa a cikinsu abu ne da ke da asali a shari'ar Muslunci. Allah (S.W.A) na cewa

 "Kuma wane ne mafi zalunci daga wanda ya hana masallatan Allah, domin kada a ambaci sunansa a cikinsu, sai kuma ya yi aiki ga rushe su?..." (2/114).

Shi kuwa Manzon Allah (S.A.W) cewa ya yi:

"Ku yi kira zuwa ga hanyar Ubangijinku da hikima da wa'azi mai kyau..." (16/125).

Manzon Allah (S.A.W) kuma ya ce:

"Duk wanda ya ga abin ƙi daga cikinku, to, ya canza shi da hannunsa, idan bai da iko to, da harshensa..." (Muslim).

Waɗannan ayoyin da hadissai, na nuna halaccin gina Masallaci da yin wa'azi da gargaɗi ga duk wanda ke da iko daga cikin Musulmi. To, amma, tattare da haka, kasancewar waɗannan abubuwa sun shafi tsintsar rayuwar addini ta jama'a, tsarin shari'ar Muslunci ya sanya wannan aiki ƙarƙashin kulawar gwamnatin Musulunci. Masallatai a idon tsarin musulunci kashi biyu ne

a) Manyan Masallatai (na Juma'a da na Idi)

 b) Ƙananan Masallatai (na Salloli biyar na yini)

 Malam Ibn Khaldun na cewa: "Kulawa da manyan Masallatai na hannun shugaban Musulmi ko wanda ya wakilta. Shi ke da alhakin naɗa limamansu don gudanar da salloli biyar, da na juma'a da na Idi, da na kisfewar rana da na roƙon ruwa... Amma, ƙananan masallatai; na kan hanya da na unguwanni, haƙƙin kulawa da su, na hannun mutanen unguwa da maƙwabtan masallatan." A kan abinda ya shafi gudanar da wa'azi a cikin masallatan kuma, sai ya ci gaba da cewa: "Wajibi ne a kan Shugaban Musulmi ya ɗauki nauyin zaɓar amintattun Malamai kuma ƙwararru don gabatar da wa'azi da fatawa ga mutane tare kuma da hana gudanar da su a cikin manyan masallatai, sai da izininsa, don kada waɗanda ba su cancanci ayyukan ba, su ɓatar da jama'a" (Ibn Khaldun, 889:214).

Sahabban Manzon Allah (S.A.W) sun ɗauki masallaci da matuƙar muhimmanci. Sun yi ƙoƙarin gina shi da kyautata shi da tsare alfarmarsu, da yin amfani da shi kamar yadda suka ga Manzon Allah (S.A.W) ya yi, ta hanyar gudanar da salla da itikafi da wuridi da zikiri da tafarkin da ta'adib a cikinsa (Maijega, 1990:5,10). Shekaru kamar talatin (30) da suka wuce kuma, kula da kafa masallatan Juma'a da na Idi da gudanar da wa'azi a cikinsu da sauran wurare, na hannun Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alh. Sir. Abubakar (III) (1938-1988) ne. Shi ke bayar da takardar izinin gaba ɗayan waɗannan abubuwa a ƙasar nan baki ɗaya (Boyd/Maishanu.1991:69). Saboda muhimmancin waɗannan abubuwa a rayuwar jama'ar musulmi ne, gwamnatin wannan jaha ta Zamfara ta kafa wannan hukuma, ta kuma ɗora mata nauyin

o   Bayar da izinin kafa masallatan Juma'a da na Idi.

o   Tantance Limamai da malaman Tafsiri a masallatan Juma'a da na Idi.

o   Biyan albashi/alawus g limamai da Na'ibbai da Ladannai na masallatan Juma'a da na Idi.

o   Tsoma baki a cikin duk abin da ya shafi waɗannan wurare.

Daga lokacin da aka kafa wannan hukuma zuwa shekarar 2005, ta tantance

1.      Masallatan Juma'a 1,442

2.      Masallatan Idi 1,332

3.      Limamman Masallatan Juma'a 1,442

4.      Na'ibbansu 1,442

5.      Ladannansu 1,442

Haka kuma tana biyan su kuɗaɗen alawus- alawus duk wata kamar haka

1.      Limammai 10,000.00

2.      Na'ibbai 6,000.00

3.      Ladannai 2,000.00

A ɓangaren gudanarwa kuwa wannan hukuma na da shugaba (Chairman) da Kwamishinonan dindindin guda biyar (5), tana kuma da sassa guda huɗu, kamar haka

·         Sashen Kula da Masallatan Juma'a

·         Sashen Kula da Wa'azi

·         Sashen Mulki

·         Sashen Kuɗi

4.5 Hukumar Kula Da Jin Daɗin Makarantun Allo

A tarihin Musulunci, makarantun allo su ne wuri na farko da 'ya'yan musulmi ke koyon rubutu da karatu, don sanin abun da zai banbanta su da dabbobi, wato ilimi. Da iya rubutu da karatu ne mutum ke iya kyakkyawan tunani. Shi kuma kyakkyawan tunani da shi ne, ake gane Allah (S.W.A) a kuma iya ƙirƙiro nagartattun hanyoyi da dabaru don kyautata rayuwar duniya da lahira

(IbnKhaldun, 799:412).

Neman ilimi wajibi ne a idon Musulunci, don Allah (S.W.A) cewa Ya yi: "Ka yi karatu da sunan Ubangijinka wanda ya yi halitta." (96/1). Shi kuma Manzon Allah (S.A.W) ya ce "Neman ilimi farilla ne a kan kowane Musulmi" (Ɗabrani).

 Kula da makarantu da fitar da al'umma daga cikin duhun jahilci aikin gwamnati ne a tsarin Musulunci. Manzon Allah (S.A.W) shi ne farkon wanda ya tabbatar da haka, ta hanyar amfani da fursunonin yaƙin Badar su karantar da 'ya'yan musulmi rubutu da karatu, don su fursunonin su fanshi kansu." (Kardhawi, 1997:212). Haka Sahabbai da tabi'ai suka ci gaba da kula da wannan aiki, ta hanyar samar da malamai da masallatai, a matsayin Makarantu na farko a musulunci.

A cikin watan August,2001 ne, gwamnatin Zamfara ta kafa wannan hukuma a ƙarƙashin kulawar ma'aikatar kula da bunƙasa rayuwar al'umma. A ƙarƙashin wannan hukuma ne, gwamnatin ke kula da jin daɗin makarantun allo a jahar, ta hanyar ba su isasshen abinci. Hukumar na ɗaukar nauyin ciyar da almajirai 17,400 daga makarantun allo 337, daga sassan jahar daban-daban. Babban maƙasudin wannan aiki shi ne sauƙaƙa wa almajirai hanyar samun abinci da rage yawan barace-barace a jaha.

4.6 Hukumar Hisbah

 Aikin hisba, aiki ne na gwamnati a tsarin Musulunci, ta hanyar horon jama'a da aikata alheri da hana su aikata ɓarna, asalin aikin kuwa shi ne faɗar Allah (S.W.A) da Ya ce:

"Waɗanda suke idan muka ba su iko a cikin ƙasa,sai su tsayar da salla, su kuma bayar da Zakka kuma su yi umurni da alheri, su kuma yi hani da abin ƙi..." (22/41).

Shi kuwa Manzon Allah (S.A.W) cewa ya yi: "Ko dai ku dage a kan horo da alheri da hani daga abin ƙi, ko Allah Ya ɗora miyagun mutane a kanku, har akai idan na ƙwarai daga cikinku suka yi addu'a ba za a karɓar ba." Khalifa Umar ɗan Khaɗɗabi shi ne farkon wanda ya fara aiki irin na 'yan hisba da kansa. An ruwaito cewa yakan kai duka ga wanda ya lafta wa raƙuminsa kayan da ya fi ƙarfinsa ya kuma ƙara da tambayarsa cewa: "Don me za ka ɗora masa kayan da ba ya iya ɗauka?" Amma, ba a fara amfani da lafazin "Hisba" a matsayin tsarin gwamnati ba, sai lokacin mulkin Abbasiyawa (158-169). Kafin wannan lokaci aikin hisba, wanda ya keɓanci ɗaukar mataki a kan matsalolin da, ba su buƙatar dogon bincike na hukunce-hukuncen Shari'a,. Yana hannun wanda aka naɗa alƙali ne. A wannan lokaci ne anka ƙirƙiro ofishin hisba na farko a tarihin musulunci, anka ɗora masa ayyukan kamar haka

i.        Horo da kowane irin alheri da hani da kowane irin sharri.

ii.      Kula da ganin an aiwatar da hukunce-hukuncen Shari'a a cikin

- Kasuwa (kada a yi algussu)

- Gine-gine (kada a canye hanya)

- Bashi (Kada a ƙi biya)

- Maƙwabtaka (kada a yi zalunci)

Ta fuskar maƙwabtaka, aikin ya haɗa har da hana wani yin dogon bene ta yadda zai iya hangen cikin gidan maƙwabcinsa (Hassan, 1996:398). A wajen Ibn Khaldun, aikin hisba ya haɗa har da:

1.      Tilasta duk mai ruɓaɓɓen gini rushe shi, don kada ya faɗa wa masu wucewa.

2.      Hana malamai tsanantawa wurin yi wa ɗalibai ladabi ta hanyar duka. Ba kuma Shugaban hisba zai jira sai kawo masa koke ba. A'a, ko labari ya ji to, ya je" (Ibn Khaldun 779:219).

Ta haka ne, tare da ƙoƙari ijtihádin shugabannin musulmi, tsarin aikin hisba ya ci gaba da faɗaɗa yana bunƙasa a matsayin aiki mai zaman kansa, har kuma ya shiga cikin kusan gaba ɗayan ayyukan da ma'aikatun gwamnatocin zamani suka keɓanta da su, kamar kula da lafiya, da tsaro da walwalar jama'a, da ƙa'idojin tuƙi da makamantansu (Khardawi, 1990:178).

4.6.1 Matakan Aikin Hisba

Kamar yadda aka bayyana a baya cewa, aikin hisba aiki ne da ya shafi horo da hani ƙarƙashin kulawa da ikon gwamnati. A kan haka malam Abdullahi Ɗanfodiyo ya kawo wasu matakai guda tara (9) waɗanda biyar su dai-dai ke wajaba don cin nasarar wannan aiki. Matakan na farawa daga gargaɗi zuwa yaƙar maɓarnaci idan ta kama. Ga su kamar haka:

1.      Sa'ido: Wato mayar da hankali sosai a kan yadda jama'a ke kaiwa da komowa don sanin halin da suke ciki, ta hanyar hikima da basira; ba da nufin leƙen asiri ko tozartawa ba.

2.      Faɗakarewa: Idan wanda aka sa ido a kansa, ta bayyana cewa, mugun aikin da yake yi, yana yin sa ne a kan rashin sani, to sai a gargaɗe shi a nuna masa haramcin ko rashin kyansa a shari'ance.

3.      Nasiha: Idan ya ci gaba da ɓarnar, sai hisba ta yi masa nasiha tare da tsoratar da shi azabar Allah da hushinsa.

4.      Mugunyar magana: A lokacin da nasiha ba ta yi amfani ba, to sai a gaya masa miyagun maganganu, ta hanyar gaya masa cewa, to daga yau fa sunansa a wurin doka shi ne, 'fasiƙi' ko 'wawa' ko 'jahili.'

5.      Matakin Soja: wato hana shi ɓarnar da ƙarfin tuwo, ta hanyar kashe gangunansa, ko fitar da shi daga cikin gidan ƙwace da makamantansu.

6.      Bushara da Duka: Idan hakan ba ta sa ya bar mugun aikin ba, to sai a yi masa bushara da cewa, to yanzu kan jikinsa zai gaya masa.

7.      Duka: Idan kunne ya ƙyanƙyashe, sai a mammangare shi a ɗan shusshure shi gwargwadon yadda za a hana shi ɓarnar.

8.      Fitar da Makami: Idan kuwa har ya ci gaba da taurin kai, da ƙoƙarin fito-na-fito, to sai a nuna masa makami, a ce ko ya bar ɓarna ko ya gane kurensa. Idan kuwa har ya kuskura ya yi biris da maganar, to, ya halatta a yi amfani da makamin a kansa.

9.      Shata Daga: Idan hakan ta sa ya yo gayyar yaƙi, to sai hisba ta ɗebi dakaru, idan ta kama babu laifi a sháya daga.

Amma kuma wanibi ne kafin mutum ya shiga aikin hisba, ya tabbatar ba wata cutarwa da za ta sami wani daga cikin danginsa saboda shi. (Ɗanfofiyo: Dhiya'u Ahlul-Hisbah). Ƙaddamar da sake aiki da tsarin shari'ar Muslunci a jahar Zamfara ke da wuya, sai gwamnati ta fahimci lalle akwai buƙatar samar da wata hukuma da za ta kula da tabbatar ganin ana aiwatar da dokokin Shari'ar kamar yadda ya dace. A kan haka ne ta kafa wannan hukuma, amma da sunan: Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Kula Da Aiwatar Da Shari'a. Daga baya kuma ta sake mata suna zuwa: Hukumar Kula da Aiwatar da Shari'a. A ranar 28th July, 2003 ne, dokar gwamnatin jaha ta sake tabbatar da wannan hukuma da sunan: Hukumar Hisba, ta kuma samar masu da motocin gudanar da aiki, a lokuta daban-daban kamar haka

·         Toyota Bus 5

·         Nissan Bus 5

·         Nissan Urban 3

·         Nissan Gas 2

·         Toyota 2y 3

·         Isuzu Tiger 6 da

·         Babur Kanchen

4.6.2 Ayyukan wannan hukuma su ne:

1.      Tabbatar da ganin an aiwatar da dokokin Shari'ar Muslunci a matakin jaha da ƙananan hukumomi.

2.      Tabbatar da ganin ma'aikata na gudanar da ayyukansu a kan tsarin shari'a a ma'aikatun gwamnati da masu zaman kansu.

3.      Halartar kotunan Shari'ar Muslunci, don tabbatar da ganin an gudanar da shari'o'i bisa ƙa'idojin musulunci, tare da kawo rahoton duk wani abu da ka iya hana adalci tabbata a kotunan.

4.      Haɗa hannu da hukumomi makusantan hursunonin da ke jiran hukuncin haddi.

5.      Biyar duk hanyoyin da suka dace don ganin an tsarkake al'umma daga duk wani abu da Shari'a ta hana.

6.      Tabbatar da ganin harkokin gudanarwa da na siyasa, a matakin jaha da ƙananan hukumomi sun tafi dai-dai da tsarin shari'a.

7.      Tabbatar da ganin ana gudanar da bukukuwa a faɗin jaha a kan tafarki da koyarwar Shari'a.

8.      Wayar da kan jama'a a kan tsare-tsaren aiwatar da Shari'a.

9.      Bayar da shawara ga gwamnatin jaha da ƙananan hukumomi a kan ma'aikatu a kan abinda ya shafi shari'a.

10.  Bayar da gudummawa ga duk wata hukuma a kan al'amurran Shari'a a duk lokacin da suka buƙata.

11.  Karɓa kiran gwamnati a kan kowace irin buƙata.

 A duk lokacin da wannan hukuma ta hisba ta ci karo da wata matsala mai matuƙar rikici, kamar ta aure, takan tura ta kotu ne. Wannan hukuma ta hisba ta jahar Zamfara na da jami'an gudanarwa kamar haka:

·         Shugaba (E.C)

·         Kwamishinonan dindindin guda shida (6)

·         Mambobin wuccin gadi guda 32

·         Sakatare

 Haka kuma tana da ƙananan ofisosa (rassa) a ƙananan hukumomi.

4.7 KWAMITIN KULA DA LOKUTTAN SALLA

Salla ita ce ibada ɗaya a cikin Musulunci, wadda musulmi ke gudanarwa sau biyar a kowace rana, a cikin wani ɗan taƙaitaccen lokaci, don ganawa da Ubangiji, ta hanyar nutso a cikin gulbin tunani da kaiwa da komawa, tare da yin zikiri da du'a'i bayan karatun Alƙur'ani. Salla wata gaɓa ce da mutum kan katse hidimominsa na rayuwar duniya, ya fuskanci mahaliccinsa yana mai ƙanƙan da kai da miƙa wuya zuwa gare shi (Mubarak, 1974:178).

 Salla babban al'amari ce addinin Musulunci, hasali ma ita ce abin da ke bambanta musulmi da wanda ba shi ba. Manzon Allah (S.A.W) na cewa "Da zarar mutum ya bar salla, to ya zama kuskuri kuma kafiri." (Musulim). A wani wurin kuma ya ƙara da cewa: "Duk wanda ya kiyaye salla za ta zamar masa wani haske da dalilin samun tsira gobe ƙiyama. Duk kuma wanda bai kiyaye ta ba, ba zai sami wani haske da dalilin samun tsira ba. Za a tayar da shi gobe ƙiyama tare da Ƙaruna da Fir'auna da Hamana da Ubayyu ɗan Halarci." (Ahmad). Wannan babbar ibada ta salla, naɗa keɓantattun lokuta da Shari'a ta yi umurni da gudanar da ita a cikinsu. Haka kuma musulunci ya ƙyamaci mutum ya gudanar da salla shi kaɗai, sai dai ya yi ta tare da jama'a (Jam'i) ina ma da hali, a masallaci (Kardhawi,1985:222). Allah (S.W.A) na cewa: "Ku tsare lokutan a kan salloli da kuma ku tsayu kuna masu ƙanƙan da kai ga Alla (2/238). A wata ayar kuma Maɗaukakin sarki ya ce: "Lalle ne, salla ta kasance a kan mumini farilla mai ƙayyadaddun lokuta." (4/103).

 Saboda muhimmancin tsare yin salloli a cikin lokacinsu, Alla (S.W.A) bai bar was manzon Alla (S.A.W) nauyin yi wa Sahabbai bayanin waccan aya ba. A maimakon haka sai ya aiko mala'ika Jibrilu ya koya wa Manzon Allah yin salla a cikin lokaci, ta hanyar tahowa dai-dai lokacin kowace salla. Abu Mus'ab, Ba'ansari, (R.A) ya ce:

"Wata rana na shiga wurin Mugirata ɗan shu'ubata, sai na taras ya yi salla bayan lokacinta ya wuce. A lokacin kuma yana zaune a Iraƙi. Sai na ce masa: Ya aka yi haka ne ya kai Mugirata? Ba ka da labarin cewa Mala'ika Jibrilu (R.A) ya sauka ya yi salla, Manzon Allah (S.A.W) kuma ya yi " (bayansa"...ya maimaita haka har sau uku a ƙarshe Manzon Allah ya ce: "Da haka aka umurce Ni?" (Bukhari:521).

Bayan wannan koyarwa da Jibrilu (R.A) ya yi wa Manzon Allah (S.A.W) ne, shi kuma ya sheda wa Sahabbai, a wani Hadisi da Abdullahi ɗan Umar ya ruwaito cewa Manzon Allah (S.A.W) ya ce:

"Lokacin sallar Azzahar idan rana ta karkata; lokacin da inuwar mutum ta yi tsawonsa, matuƙar La'asar ba ta yi ba. Lokacin La'asar kuwa matuƙar rana ba ta yi fatsi-fatsi ba. Lokacin sallar Magriba kuwa, matuƙar shafaƙi bai faku ba. Lokacin sallar Isha'i kuwa, har zuwa rabin dare na tsakiya. Lokacin sallar Subahin kuwa, daga hudowar alfijir, matuƙar rana ta hudo to, ku kame daga salla, don ita (rana) tana ɓullowa ne tsakanin ƙahonin sheɗan (Muslim:173/612).

Zaƙaƙuran malamai a fagen ilimin Fiƙhun ibada, sun yi fashin baƙin wannan Hadisi, suka fitar da lokacin kowace salla, daga cikin sallolin yini da dare guda biyar, ta hanyar tantance zaɓaɓɓen lokacin kowace, mukhtári, da lalurinta.

Ga bayanin a cikin jadawalin.

 

Sallar Azzahar

Daga karkatawar rana daga tsakiyar sama, zuwa ƙarshen kamu ɗaya na tsawon inuwar mutum

Daga farkon mukhtárin La'asar zuwa gab da fatsi-fatsin rana

La'asar

Daga ƙarshen mukhtárin Azahar, zuwa ƙarshen lalurinta

Daga tsakanin jajan rana zuwa faɗuwarta

Magariba

Daga farkon lalurin la'asar zuwa ƙarshensa

Daga ƙare-sallar zuwa ketowar al-fijir

Isha'i

Daga ɓacewar ja-jan rana har zuwa sulusin farko(1/3)

Daga ƙarshen sulusin (1/3) zuwa ƙarshen lalurin Magriba

Subahin

Daga hudowar al-fijir zuwa wayewar gari (jijjihi)

Daga wayewar safiya zuwa ɓullowar rana.

 

 

 

 

Waɗannan lokuta su ne ƙayyadaddun lokutan da aka sharɗanta yin ibadar salla a cikinsu, wato i) Lokaci Mukhtari (Zaɓaɓɓe) da ii)Lokaci laluri (Bisa Lalura) (Gusau, 1994: 29-30).

 Bincike a tarihin Musulunci ya nuna cewa, kulawa da ganin an yi sallolin farilla a cikin lokacinsu, aikin hukuma ne, koda kuwa hakan za ta kai ga hukunta masu kunnuwan ƙashi, hukunci mai tsanani. Bukhari da Muslim sun ruwaito cewa, Manzon Allah (S.A.W) ya taɓa cewa

"Haƙiƙa na yi nufin in yi umurni da a tayar da salla, ina kuma wakilta wani ya yi Limancin, sannan ina ɗebi wasu mazaje, su ɗauki bakunan wuta mu iske waɗanda ba su halarta salla (a cikin lokaci da jama'a) in ƙone ɗakunansu." A wani hadisin kuma Abu Zarri na cewa "Wata rana Manzo Allah (S.A.W) ya ce mani: "Ya za ka yi idan ka wayi gari shugabanninka na jinkirta salla ko yin ta kafin kafin lokacinta?" Sai na ce: Duk abin da ka hore ni da shi, shi zan yi. Sai ya ce: Da zarar lokacin salla ya yi ka yi ta. Idan kuma sun tayar da tasu, kana kusa ka bi su ta zama nafila gare ka" (Muslim: 238/648).

Haka Sahabbai da tabi'ai da sauran shugabanni a tarihin musulunci, suka dage a kan gudanar da sallolinsu a kan lokuta na Shari'a, kuma a masallaci, kai! Hatta sallar Asham (Alkareji) Mai jega, 1993:10).

 A ranar 6th Yuli 2001 ne, gwamnatin Jaha ta ƙaddamar da wannan kwamiti, ta kuma ɗora masa nauyin kulawa da tantance lokacin kowace salla, tare da wayar da kan jama'a. Kwamitin na ƙarƙashin sashen Da'awa ne, na Ma'aikatar lamurran addini ta jaha.

4.7.1 Dabarun Aiki

 Wannan kwamiti ya fara aikinsa, da shirya ziyara ta musamman zuwa ga manyan malamai, waɗanda ke cikin garin Gusau, musamman malaman zaure. Maƙasudin ziyarar, shi ne malaman su san da kwamitin, ya kuma nemi shawarwari daga gare su. Waɗanda ziyarce-ziyarcen sun yi nasara, don malaman sun yi arƙawarin bayar da gudummawa ga kwamitin a duk lokacin da buƙatar hakan ta samu.

 Tun daga wannan lokaci ne, kwamitin ya ci gaba da samar da jadawalin kowace salla a ƙarshen kowane wata. Hanyoyin da kwamitin kan bi don samar da wannan jadawali sun haɗa da

·         Alƙur'ani Maigirma: shi ne makoma ta farko da kwamitin kan dogara a kai don samun bayanai a kan gaba ɗayan abun da jadawalin zai ƙunsa.

·         Hadisi: Daga nan kuma sai kwamitin ya duba abubuwan da suka taho a cikin hadisai, a matsayin bayanin waɗancan ayoyi na Alƙur'ani.

·         Fiƙhu: Kwamitin kan leƙa zantukan malaman Fiƙhun fuskokin nazari. Babbar madogarar kwamitin a wannan hanya ita ce littafin: Bidayatul-Mujtahid Wa Nihayatul-Muhtasid na malam Ibn Rushid.

·         Ilimin Taurari: Kwamitin kan yi amfani da bayanan masana taurari, tare da suna maganganunsu da Alƙur'ani da Hadisi da Fiƙhu, a inda sukan fifita su a kan ilimin taurarin a duk lokacin da ya yi ban hannun makaho da su.

 A ƙarshe, kwamitin kan rarraba wannan jadawali a cikin faɗin jahar Zamfara; birni da ƙauye. Wasu garuruwa na jihohin maƙwabta ma kan amfana da wannan aiki.

8.KWAMITIN KULA DA GANIN WATA

 Azumi ibada ce, wadda Alla (S.W.A) ya farlanta a kan bayinsa. Ana yin sa ta hanyar ƙaurace wa ci da sha da jima'i tun daga fitowar alfijir har zuwa faɗuwar rana kullum, tsawon kwana ashirin da tara (29), ko talatin (30), na watan Ramalana. Ka ga kenan, ashe azumi tuɓe rigar bukatun jiki ne gaba ɗaya, da nufin samun kusanta ga Ubangiji da hasken ruhi da ɗaukakarsa (Mubarak, 1984: 180).

 A cikin shekara ta biyu ne, bayan hijirar Manzon Allah (S.A.W), Allah (S.W.A) Ya farlanta wa musulmi ibadar azumi, don su ƙara tsoronsa. Allah (S.W.A) na cewa

"Ya ku waɗanda suka yi imani! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan waɗanda suke gabaninku, tsammaninku, za ku yi taƙawa" (2/183).

Watan Ramadana shi ne lokacin da Shari'a ta keɓe don gudanar da wannan ibada ta azumi. Da zarar watan ya fita, Azumi ya kama; ƙarewarsa, kuwa ita ce ƙarewar ibadar a wannan shekara. Manzon Alla (S.A.W) ya gaya mana yadda ake tabbatar da ganin wannan wata mai alfarma. Abu Hurairata ya ruwaito cewa:

"Ku ɗauki Azumi idan an ga wata; ku kuma aje idan an gan shi. Idan kun kasa ganin sa, to ku kammala kwanakin watan Sh'abana su kai talatin" (Bukhari da Muslim).

Wannan Hadisi ba ya nufin cewa dole ne ga kowane musulmi; namiji ko mace, sai ya ga wata da ƙwayar idonsa, kafin ya ɗauki Azumi. Hain kansu a cikin wannan ibada shi ne abin so (Jinjina,2001:149), ta hanyar azumtar kwanakin watan baki ɗaya ba tare da koda rana ɗaya ta kuɓuce masu daga cikinsa; ko su azumci wata rana daga wajensa ba. Wato kamar su yi Azumin ranar ƙarshen watan Sha'abana ko ranar farkon watan shauwal (Ƙardhawi, 1990: 145). Manufar wannan Hadisi kuwa na tabbata ne kawai, ta hanyar biyar diddigin ƙarewar watan Sha'aban, da sauran watannin shekara Musulunci baki ɗaya, don dukansu, na da alaƙa da juna, ta fuskar farawa da ƙarewa. Wannan aiki kuwa wajibi ne a kan al'ummar musulmi baki ɗaya (Ƙardhawi, 2003:25).

 Fitar watan Azumi na tabbata ne a shari'ar Musulunci, tabbata irin wadda ke wajabta wa kowane musulmi ɗaukar Azumi, idan mutum ɗaya ko biyu adilai, ko taron jama'a suka bayar da shedar ganin watan gwargwadon yanayi da ganin nasu. Wannan hanya ta jiran wata ya fito da kansa kafin a ɗauki Azumi (ar-ru'uyah) ita ce hanyar da musulmi suka dogara a kanta, can farkon zamani, saboda a zamanin Manzon Alla (S.A.W) mafi yawan al'ummar Larabawa ba su da ilimin rubutu da lissafi. Manzon Alla (S.A.W) na cewa:

"Mu al'umma ce bagidada ba mu iya rubutu ko lissafi ba..." (Bukhari: 1913). Amma wasu malamai sun tafi a kan cewa, a duk lokacin da kwalliyar koyarwa da Manzon Alla (S.A.W) ya yi ta biya kuɗin sabulu; aka wayi garin al'ummar Muhammadu ta yi ilimi, aka samu masana ƙwararru a kowane fanni har da na taurari, kamar irin yau, to babu laifi a nemi tabbatar watan Azumi ta hanyar lissafi, alal-aƙalla ko da ta fuskar tabbatar da rashin yiwuwar bayyanarsa a daidai wani lokaci. (Ƙardhawi, 1992: 171, 178).

Bayar da sanarwar an ga watan Ramadana da yin umurni da ɗaukar Azumi aikin shugaba ne a tsarin Musulunci. Ibn Umar ya ce: "Mutane sun dubi wata, sai na gaya wa Manzon Alla (S.A.W) cewa lalle Ni na gan shi, sai ya ɗauki Azumi ya kuma umurci mutane da su ɗauka." (Abu Dawuda). Haka wannan al'amari ya ci gaba da gudana sai bayan wucewar Manzon Alla (S.A.W) ne, aka fara samun bambanci kwana ɗaya ko biyu tsakanin Musulmi a cikin ɗaukar Azumi, kamar yadda abin ke faruwa a kwanukanmu na yau. Hakan kuwa na tabbatar da cewa lalle, akwai waɗanda rana ɗaya ta watan Ramadana ke kucce wa, a duk lokacin da irin haka ta faru. Don ƙoƙarin kauce wa irin wannan haɗari ne, shugabannin musulmi suka haɗu a kan cewa, a duk lokacin da shugaban Musulmi ya bayar da sanarwar an ga watan Ramadana ya kuma yi umarni da tashi da Azumi, ta hanyar wata hukuma ko ma'aikata,to, wajibi ne kowa ya tashi da shi, don tabbatar da haɗin kan musulmi a cikin ibadodinsu wajibi ne (Ƙardhawi, 2003:32-33) Da zarar gwamnati ta karɓar sunan Gwamnati, to, yi mata ɗa'a wajibi ne, saɓa wa umurninta kuwa tawaye ne, Alla (S.W.A) na cewa:

"Ya ku waɗanda suka yi imani ku yi ɗa'a ga Alla, kuma ku yi ɗa'a ga manzonsa, da ma'abuta al'amari daga cikinku." (4/58)

Shi kuwa manzon Alla (S.A.W) cewa ya yi:

"Duk wanda ya yi Mani ɗa'a haƙiƙa ya yi ɗa'a ga Alla, Wanda kuma ya saɓa Mani yaƙi ƙara ya saɓa wa Alla. Haka duk wanda ya saɓa wa shugaba haƙiƙa ya yi ɗa'a gare ni, wanda kuwa duk ya saɓa wa shugaba haƙiƙa ya saɓa mani." (Muslim).

 A ƙoƙarin sayyidina Umar (R.A) na bayyana irin muhimmancin da ɗa'a keda shi a addinin Musulunci cewa ya yi: "Babu musulunci idan babu jama'a, babu jama'a idan babu shugaba, babu shugaba idan babu ɗa'a." (Abu Farisa, 1984:67).

A kan abin da ya shafi kulawa da ganin al'ummar musulmi sun ɗauki Azumi sun aje lokaci ɗaya kuwa, gwamnatin Jahar Arewa a ƙarƙashin jagorancin Sardaunan Sokoto Sir, Ahmadu Bello KBE (1909-1966) ce ta fara kafa kwamiti na musamman a ƙarƙashin jagorancin Wazirin Sakkwato Dr. Junaidu (1909-1997) don bayar da shawara ga JNI. Sardaunan ya ƙaddamar da kwamitin ne a ranar 23rd August, 1963. Ayyukan wannan kwamiti sun haɗa da, duba yadda za a shawo kan matsalar ɗauka da aje Azumi. A cikin jawabin da Sardaunan ya yi a ranar ne yake cewa:

"...haka ya ke kuma Azumi da sallolin Idi. Sanin ku ne abin da ake ciki a wannan lokaci ana yin su daban-daban a wurare, alhali kuwa ƙasa ɗaya muke, wannan yana damun jama'a ainun. Kowane musulmi ana ɗauƙar sa adali, sai ina ya bayyana akasin haka." (Alƙali,2002:108,111).

An ci gaba da irin wannan aiki ne, don haɗa kan musulmi, gwamnatin jahar Zamfara, a ƙarƙashin jagorancin Sardaunan Zamfara Dr. Ahmad Sani, ta kafa wannan kwamiti na kula da ganin wata. An ƙaddamar da wannan kwamiti a ranar 11th Shawwal 1422A.H/ 4th Okutoba, 2001. Shi ma wannan kwamiti yana ƙarƙashin sashen Da'awa ne na ma'aikatar lamurran Addini ta jaha. Mambobin kwamitin kuma sun haɗa 'ya'yan

i) Ƙungiyar Ƙadiriyya.

ii) Ƙungiyar Tijjaniyya

iii) Ƙungiyar Izala (Jos/Kaduna)

iv) Ƙungiyar Islahuddin, da;

v) Wakilan gwamnati

4.7.2 Ayyukan da aka ɗora wa kwamitin kuma sun haɗa da:-

1.      Tabbatar da ranar da kowane wata ya kama, tsawon shekara.

2.      Bayar da sanarwar kamawar a kafafen watsa labarai.

3.      Sa ido a kan ranakun Idi da sauran bukukuwan musulunci.

4.      Haɗa kan al'ummar Musulunci a kan kalandar da kwamitin zai riƙa fitarwa wata-wata. Musamman watannin Ramadana da Shawwal da Zul-Hajji.

5.      Gudanar da aiki

Wannan kwamiti ya gudanar da waɗannan ayyuka da aka ɗora masa ta hanyar:

a. Kafa ƙananan kwamitota a ƙasashen Uwayen ƙasa a faɗin jaha.

b. Haɗuwa da sakatarorin waɗancan kwamitota, tare da;

c. Fita don dubon wata, a ƙarshen kowane wata.

d. Tattaunawa da wasu kwamitota irinsa na wasu jahohin ƙasa, da;

e. Buga kalandar fitar kowane wata tare da bayanan Burujai da Manziloli, tare da fitar da muhimman ranakun shekarar musulunci.

5.0 ABUNDA BINCIKE YA GANO

Bayar da shawara ga gwamnatin jaha shi ne babban aikin malamai da su ke a wannan majalisa.

Tunatarwa ga Sauran jama'a, tare da tirsasawa ga waɗanda kunnuwansu na ƙyanƙyashe ga aikata haƙƙoƙan Shari'a.

5.1 KAMMALAWA

Kamar yadda bayanai suka gabata wannan muƙalla ta yi tozali ne kacokam kan ayyana ayyukan malamai da ke a majalisar malamai (Shura) ta jahar zamfara, tare da ayyana wasu daga cikin ayyukan da suka shafi sauran hukumomin addinin na gwamnatin jahar. Haka ma ta bayyana wasu daga cikin kwamitotan da malamai ke aiwatar da wasu ayyuka na Hukumomin.

Post a Comment

0 Comments