Ticker

6/recent/ticker-posts

Mafarkin Tashin Alqiyama

TAMBAYA (66)

Assalamu Alaikum warahamatullah. Malam Allah ya saka da Alkhairi da fada karwa ameen.

Malam kwana 2 ina yawan mafarkin Tashim Alqiyama. Malam maye fassara mafarkina? Na gode sosai Allah ya saka da Alkhairi Ameen

Ataimka dan Allah

AMSA

Alhamdulillah

Ganin ranar lahira a mafarki na nufin gargadi na musamman ga mai aikata sabo, ko kuma gargadi ga wanda yake da kokwanto akan girma ko kankantar saqo

Ganin ranar lahira a mafarki na nufin gaskiya. Idan ka ganka kai kadai a filin tashin alqiyama na nufin mutuwarka. Mafarkin jiran ayi maka hisabi na nufin zaka yi tafiya. Idan kayi mafarkin an tashe ka ranar lahira daga kai sai matarka, hakan na nufin baka mata adalci

Idan aka tashi mayaqi shi kadai ranar lahira hakan na nufin zai nasar akan abokin hamayyarsa. Sautin busar kahon ranar lahira na nufin tsira ga masu taqwa

SHARHI

A karkashin haka, saika dage da yawan aikata ayyukan alkhairi ka nesanci na sharri, a shawarce idan ka samu kudi (ta hanyar halal) saika fanshi littafin al-Qur'ani mai girma, ka bawa committee din masallachi mafi kusa ko kuma Islamiyya/Tahfeez  a matsayin sadatul jariya saboda idan Allah SWT ya karbi rayuwarka to ladanka zai ci gaba da zuwan maka alhalin kana kabari la'akari da duk wanda ya karanta harafi daya yanada lada 10. To ya kake tunani idan wani ya karanta shafi 5 ko 10, ko kuma a samu wani ya karanta Izu 1 ko 10. Kuma duk harafi daya lada 10 zai samu kuma kaima zaka samu lada 10 din ba tare da an tauye masa nashi ba kamar yanda Annabi SAW yazo a cikin Sahihul Bukhari da Muslim. Lada kan lada kenan

Wallahu ta'ala a'alam

Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta, astaghfiruka wa'atubi ilayk

Amsawa;

Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments