Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Auren Dan Shi'a

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

ina da 'yar'uwa sama da shekara goma tana soyayya da ɗan shi'a an yi an yi ta rabu dashi taqi, har ta shiga shi'ar, iyayenta sunqi aura mata shi, yanzu an samu wasu adangi 'yan bidi'a zasu daura musu aure, shin ya halatta muje bikin?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ

Idan Allah ya datar da Mutum ya shiryar dashi da bin hanyar Ahlussunnah wal-jama'a, to dole ya san abubuwan da zasu rabashi da abunda Ahulus-sunnah wal-jama'a suke akai don nesantar su, ya kuma san Abunda 'yan shi'a suke akai na aqidu mugwaye da tafarki.

Asalai da 'yan shi'a suka saɓawa ahulus-sunnah akansu suna da yawa daka cikinsu akwai:-

'yan shi'a suna qudurce jirkitar alqur'ani badai-dai yake ba, suna qudurce limamansu basa Saɓo, sun kafirta sahabbai baki ɗaya sai 'yan kaɗan da suka bari ba su kafirta ba, suna girmama Qabur-bura, da raya su, suna neman agajin mamacin dake cikin qabari da roqonsa biyan wata buqata, a mai-makon Allah, duk Wannan ya samo asali saboda baqar qiyayya da hassada da suke da ita akan ahlusunnah Wal-jama'a, da kafirta su da sukayi, ta yaya zaka Aurar da 'yarka ga wanda wannan shi ne aqidarsa, ta yaya kake tunani zai samu nasara arayuwa tareda tattaruwar wannan tufka da War-wara da yake da ita acikin addini? ta yaya zai tarbiyanci 'ya'ya?, akan tauhudi zai rainesu ko akan shirka da bata da maguzanci? shin kanajin Zai koya musu son sahabbai, ko qinsu zai koya musu?, shin zai koya musu Tsarkakuwar limamansu goma sha biyu, ko zai koyar dasu mantuwa da kus-kure yana iya faruwa dasu?, da sauran Abubuwa masu yawa na tufka da War-wara.

Indai Mutum ɗan shi'a ne ko an daura masa Aure da yarinya wannan auren ɓataccene, bai halatta Mace ta Aureshi ba, domin Waɗannan aqidun suna kishiyantar addinin musulunci ne, Allah madaukakin Sarki yace

وَلَا تَنكِحُوا الْمُشْرِكَاتِ حَتَّىٰ يُؤْمِنَّ وَلَأَمَةٌ مُّؤْمِنَةٌ خَيْرٌ مِّن مُّشْرِكَةٍ وَلَوْ أَعْجَبَتْكُمْ وَلَا تُنكِحُوا الْمُشْرِكِينَ حَتَّىٰ يُؤْمِنُوا وَلَعَبْدٌ مُّؤْمِنٌ خَيْرٌ مِّن مُّشْرِكٍ وَلَوْ أَعْجَبَكُمْ أُولَٰئِكَ يَدْعُونَ إِلَى النَّارِ وَاللَّهُ يَدْعُو إِلَى الْجَنَّةِ وَالْمَغْفِرَةِ بِإِذْنِهِ وَيُبَيِّنُ آيَاتِهِ لِلنَّاسِ لَعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ 

Kuma kada ku auri mata mushirikai sai sun yi imani: Kuma lalle ne baiwa muminaita ce mafi alhẽri daga ɗiya kafira, kuma ko da ta ba ku sha'awa. Kuma kada ku aurar wa maza mushirikai sai sun yi imani, kuma lalle ne bawa mumini shi ne mafi alhẽri daga da mushiriki, kuma ko da ya ba ku sha'awa, waɗannan suna kira ne zuwa ga wuta kuma Allah Yana kira zuwa ga Aljanna da gafara da izninsa. Kuma Yana bayyana ayoyinsa ga mutane; tsammaninsu suna tunawa. (Suratul Bakara aya 221)

An tambayi Shaikul Islam ibnu taimiyyah akan shin ya halatta mace ta auri ɗan shi'a ko na miji ya Auri 'yar shi'a?.

Ya Amsa da: 'yan shi'a masoya son zuciyane da bidi'a da ɓata, bai kamata musulmi ya Aurar da 'yarsa ko wacce yake da walicci akanta ga ɗan shi'a ba.

Idan itama 'yar shi'ace, aure yayi, idan ana fatan zata tuba, idan ita macen ce 'yar shi'a namijin ba ɗan shi'a bane, kuma ba'a tsammanin zata tuba, barin Aurenta shi ne yafi, don kada ta ɓata masa 'ya'yansa. Maj-mu'u fatawa (32/61).

Kaga Anan shaikul islam ya hana auren 'yar shi'a, duk da Aure yana sanya miji yayi tasiri akan matarsa, ya halatta auren 'yar shi'a idan ana fatan tuban ta..

idan Mutum yaga aurenta zaisa ya tsayar da ita akan hanyar gaskiya.

Amma Idan Macece Ɗan shi'a ya nemi Aurenta kai tsaye haramunne a daura musu aure, idan An daura auren baiyi ba.

Ta kowacce hali babu wata hujja da uba zai qyale wasu tsoffi 'yan bidi'a yanaji yana gani su aurar wa da ɗan shi'a 'yarsa, wannan ya nuna shikansa bai san me yake yi ba, ranar qiyama kai uba kai Allah zaiwa tambaya dangane da kiwon 'ya'yanka da Allah ya baka.

ba dai-dai bane iyaye maza sudunga qyale Al'amarin auren 'ya'yansu a hannun kakanninsu ko iyayensu koda kuwa su ba su aminta da aqida ko halaye na wannan da yake neman 'ya'yansu ba.

Uba shike da haqqin Aurar da 'yarsa ga mutumin daya aminta da halayyarsa da Addininsa da Aqidarsa.

Wajibine akan Uba ya tashi tsaye yayi bincke mai qarfi akan duk wanda yazo neman Auren 'yarsa.

Idan ya tabbatar bashi da aqida ko halayya mai kyau, to shi ne yake da cikakken iko da hurumin Auren da 'yarsa, in yaga mutum bashi da aqida mai kyau, to karya sake wasu tsoffi suyi masa dole, ya tsaya tsayin daka ko sama da Qasa zata haɗe karya Aurar da 'yarsa ga mutumin banza mushiriki.

Yanzu ba Maganar zuwa Daurin Aure ba, ko an daura ma Auren baiyi ba.

Dolene Akan uban wannan yarinya ya tsaya yaga 'yarsa bata Auri wannan zindiqin ba, duk irin rikicin da za'ayi saidai ayi 'yarkace kai Allah zai tambaya akan Amanarta daya damqa ahannunka.

Kada Ku sake ayi wannan Auren iskanci da fasadi mai yawa dake cikinsa.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments