Abubuwan Da Ke Ciki
Gabatarwa
A babi na goma an yi bayani dangane da nau’o’in abincin wasa -wasa na Hausawa a gargajiyance. Nau’o’in wasa-wasar da aka lissafo a ƙ ar ƙ ashin babi na goma, duk akan same su a zamanance. Bambancin da ke tsakani bai wuce na kayan ha ɗ i ba. Nau’o’in wasa-wasar gargajiya da ake samu a zamani sun ha ɗ a da:
i. Wasa-wasar dawa
ii. Wasa-wasar shinkafa
iii. Wasa-wasar gero
iv. Wasa-wasar dambu
v. Wasa-wasar burabusko
vi. Wasa-wasar wake
Wasa-Wasa r Kuskus
Kayan haɗin da za a tanada su ne:
i. Gishiri
ii. Kuskus
iii. Mai
iv. Ruwa
v. Yaji
Wannan nau’in
abinci kuwa, ruwa za a tafasa
daidai adadin sanwar da za a
yi. Za zuba kuskus a cikin ruwan
tare da gishiri. Da zarar ya yi, za a ga ya kumbura sannan ya yi wasar-wasar.
Sai a lura sosai, domin kada
a cika masa ruwa yadda zai cakuɗe.
Akan ci wannan
nau’in abinci da mai da yaji, wani lokaci har
ma da miya
.
Wasa-Wasa r Dambu
Kayan haɗin da za a tanada su ne:
a. Mai
b. Ɓarzazziyar
Masara ko Shinkafa
c. Ruwa
d. Yaji
Za dafa dambun
masara
ko na
shinkafa haka nan ba tare da an saka masa komai ba. Akan yi wannan
dafuwa ne ta hanyar turara shi a madanbaci.
Idan ya dafu,
sai a kwashe shi. Za a iya cin sa
da mai da gishiri da Barkono (tonka). Haka kuma, shi ma za a iya saka ganye a
yi kwaɗo
da shi tare da ƙuli. Haka kuma, za a iya saka masa miya
idan ana buƙata a ci da ita.
Wasa-Wasa r Taliya
Kayan haɗin da za a tanada su ne:
i. Gishiri
ii. Mai
iii. Ruwa
iv. Taliya
v. Yaji
Za a dafa
taliya da gishiri a tukunya
da farko.
Ana kula da adadin ruwan da
za a sanya domin kada ta cakuɗe.
Bayan ta nuna kuma ta tsane, ana cin ta da mai da yaji, ko kuma a sanya miya
.
Wasa-Wasar Makaroni
Kayan haɗin da za a tanada su ne:
i. Gishiri
ii. Mai
iii. Makaroni
iv. Ruwa
v. Yaji
Za a dafa makaroni da gishiri a tukunya
tamkar
yadda ake dafa taliya (wanda aka yi bayani a 24.1.3 a sama). Za a kula
da adadin ruwan da za a sanya domin kada ta cakuɗe.
Bayan ta nuna kuma ta tsane, ana cin ta da mai da yaji, ko kuma a sanya miya
.
Kammalawa
Abincin
wasa
-wasa, abinci ne mai sauƙin dafuwa ba tare da an
saka kayayakin lambu a wajen dafuwa ko cinsa ba. Duk da haka, akan samu waɗanda ke amfani da kayan lambun
yayin cin wasa-wasar. Mafi
yawanci abinci ne da ake cin sa da mai da yaji.
Wani
lokaci kuma akan sanya miya
, musamman a zamanin yau.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.