Ticker

6/recent/ticker-posts

Idan Na Kara Saduwa Da Ke, Kamar Nayi Da Mahaifiyata Ne

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam Dan Allah tanbayace Dani akwai kawatace takecemun namata tanbaya itada mijintane tunsunada sati uku nabikinsu sabani yashiga tsakaninsu saishi mijin yarantse akancewa inyakara saduwa da ita tokamar ya yida mahaifiyar sa ne to itakuma saitabashi hakuri haryahakura to alokacin yasamu wani malami yamasa bayani saiyacemasa fiddakai zaiyi saiyacire mudu uku shikenan gashi harsun haifiyara biyar to yanzu sai takejin ance idanhaka tafaru saika ciyarda miskini 60 saitagaya mishi to fa shine take tanbiya ya auren su yake dakuma yaranda suka haifa nagode sainaji amsa.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikis Salaam:- Tabbas ya yi Kuskure harda shi malamin da ya basu Fatawar, Kuma ba haka ya kamata ya yi ba. Abinda aka gaya masa daga baya shine zai yi. Ma'ana zai ciyar da Miskinai 60.

 Sannan zai yi hakan ne kafin ya sadu da matar sa. Sai ya gama ciyarwa zai fara kusantar matar sa da Jima'i. Matukar Bai bayar ba babu Jima'i a tsakanin Su.

Sabida haka kenan ya Kaddara Cewa a baya ya yi Amfani da Fatawar Wani Jahilin Malami wanda bai san me yake yi ba.

 Sabida haka a yanzu zai dakatar da Saduwa da matar sa, har sai ya gama ciyarwar tukuna, Sannan ne kuma zai fara saduwa da Matar sa,  Sa'annan Auren su yana Nan babu abunda ya same shi.

Allah shine Masani.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments