Hukuncin Matar Da Ta Ki Yarda Mijinta Ya Sadu Da Ita

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Menene hukuncin Matar da zata nemi Mijinta yabata wasu Kuɗaɗe idan kuma bai bata ba sai takama fushi dashi harma taki yarda yana saduwa da'ita??

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Dafarko dai musani cewa Shari'ar-Muslunci ta wajabtawa Miji yaciyar da Matarsa tareda ƙananan 'Ya'yansa, sannan kuma dolene akansa ya nema musu muhallin da zasu zauna, to ammafa kowanne Miji zaiyi hakanne iyakar daidai gwargwadon samunsane, saboda faɗin Aʟʟαн( ) acikin Sūratuɗ-Ɗalaƙ aya ta-7 inda yake cewa

    " ﻟِﻴُﻨْﻔِﻖْ ﺫُﻭ ﺳَﻌَﺔٍ ﻣِﻦْ ﺳَﻌَﺘِﻪِ ﻭَﻣَﻦْ ﻗُﺪِﺭَ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﺭِﺯْﻗُﻪُ ﻓَﻠْﻴُﻨْﻔِﻖْ ﻣِﻤَّﺎ ﺁَﺗَﺎﻩُ ﺍﻟﻠَّﻪُ "

    MA'ANA

    Ma'bocin wadata yaciyar da iyalinsa daga cikin wadatarsa, amma wanda aka ƙuntata masa (yanayin arziƙinsa) sai yaciyar daga ɗan abinda Aʟʟαн( ) ya horemasa

    Danhaka abune maikyau ga wanda Aʟʟαн( ) ya ba shi wadata shima ya yalwatawa iyalinsa daidai gwargwado, idan ya yi haka ya saukewa kansa nauyin da Aʟʟαн( ) yaɗora masa akan kiwon da Aʟʟαн( ) ya ba shi na iyalinsa,

    Sannan kuma babu laifi akan Miji idan yaɗauki Kuɗi ko wata kadara yabawa Matarsa domin hakan na daga cikin kyautatawa, Saidai yin hakan ba wajibi bane akansa, domin baya cikin abinda Shari'a ta wajabta masa, danhaka idan bai bayarba to babu komai akansa indai yasauke nauyin da Shari'a ta ɗōra masa gwargwadon samunsa

    Danhaka anan baya halatta ga Mace ta ɗōrawa Mijinta nauyin cewa sai yabata adadin wasu Kuɗaɗe, kokuma tace dole sai ya saya mata wata kadara dadai sauransu waɗanda kwata-kwata basa cikin ciyarwar da Aʟʟαн( ) Ya wajabta masa, to idan Mace tayi haka ko Shakka babu tayi zalunci, kuma sai Aʟʟαн( ) Ya kamata da wannan laifin, sannan tayiyu wani Mijin idan an tambayeshi yaƙi bayarwa, wani Mijin kuma tayiwu yabayar amma bawai dan aransa yanason bayarwarba, saidan kawai azauna lafiya domin wataƙila yasan idan bai bayarba to fitinar da Matar za ta yi masa adalilin hakan ba ƙaramabace, wata Matar ma adalilin hakan zata riƙa fushi da Mijin harma ta dena yarda yana saduwa da'ita, sannan wasu Matan kuma sukan ribaci daidai lokacin da sukaga Mijinsu yanason saduwa dasu sai su bijiro masa da wata bukatarsu alokacin, danhaka kusani dukkan Mutumin da yaɗauki haƙƙinsa yabawa wani badon yanasoba sai dan kawai an tilasta masane kokuma don saboda yanajin kunyar Mutumin tasa ya ba shi amma ba ason ransaba, ko yabayarne kawai dan yakuɓuta daga Sharrinsa ko Masifarsa, kokuma yabayarne kawai dan saboda yanajin tsoransa, dadai sauran wasu hanyoyi makamantan waɗannan, tofa ya tabbatar dacewa yaci haramun, domin Mαиzoи Aʟʟαн( Sallallahu alaihi Wasallam) Yace

    " ﻻ ﻳﺤﻞ ﻣﺎﻝ ﺍﻣﺮﺉ ﻣﺴﻠﻢ ﺇﻻ ﻋﻦ ﻃﻴﺐ ﻧﻔﺲ ﻣﻨﻪ "

    MA'ANA

    Baya halatta aci dukiyar wani Mutum Musulmi sai in da son ransa

    Danhaka sai ayi hattara, sannan baya halatta ga Mace tahanawa Mijinta kanta ya yi jima'i da'ita kawai don saboda yaƙi biyamata waɗansu buƙatunta na duniya, danhaka kusani cewa dukkan Matar da Mijinta ya nemeta da jima'i amma taƙi yarda to tana cikin tsinuwar Aʟʟαн( ) da Mala'ikunsa, saidai in wata larurace ta hanata to anan sai ayimata uzuri

    шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ

    AMSAWA

    Mυѕтαρнα Uѕмαи

    08032531505

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/Cnf26Q8MPqz9yUYU1nxqRq

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.