Idan Mace Ta Kashe Namiji

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu Alaikum. Wani malami ne ya ce wai idan mace ta kashe namiji za a kashe ta, amma idan shi ya kashe ta ba za a kashe shi ba. Yaya abin ya ke?

    𝐀𝐌��𝐀❗️

    Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

    Shi da ya faɗi maganar ce za a nemi bayani da hujja daga gare shi. Allaah Ta’aala ya ce

     قُلۡ هَاتُوا۟ بُرۡهَـٰنَكُمۡ إِن كُنتُمۡ صَـٰدِقِینَ

    Ka ce: Ku kawo hujjojinku in kun kasance masu gaskiya. (Surah Al-Baqarah: 111; Surah An-Naml: 64)

    Kisan kai dai kowa ya san haram ne, saboda maganar Allaah Ta’aala

    وَمَن یَقۡتُلۡ مُؤۡمِنࣰا مُّتَعَمِّدࣰا فَجَزَاۤؤُهُۥ جَهَنَّمُ خَـٰلِدࣰا فِیهَا وَغَضِبَ ٱللَّهُ عَلَیۡهِ وَلَعَنَهُۥ وَأَعَدَّ لَهُۥ عَذَابًا عَظِیمࣰا

    Kuma duk wanda ya kashe mumini da gangar, to sakamakonsa Wutar Jahannama ce, yana madawwami a cikinta, kuma Allaah ya yi fushi da shi, kuma ya la’ance shi, kuma ya yi masa tattalin azaba mai girma. (Surah An-Nisaa’i: 93).

    Kuma Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

    « كُلُّ الْمُسْلِمِ عَلَى الْمُسْلِمِ حَرَامٌ دَمُهُ وَمَالُهُ وَعِرْضُهُ »

    Kowane musulmi a kan musulmi haram ne: Jininsa da dukiyarsa da mutuncinsa. (Sahih Muslim: 6706).

    Sannan kuma ya ƙara cewa

    « لَزَوَالُ الدُّنْيَا أَهْوَنُ عَلَى اللَّهِ مِنْ قَتْلِ رَجُلٍ مُسْلِمٍ »

    Wallahi, gushewar duniya shi ya fi sauƙi a wurin Allaah fiye da kashe wani mutum musulmi. (At-Tirmiziy: 1455).

    Don haka, ba a samun musulmi da wannan laifin sai dai a bisa kuskure

     وَمَا كَانَ لِمُؤۡمِنٍ أَن یَقۡتُلَ مُؤۡمِنًا إِلَّا خَطَـࣰٔاۚ

    Kuma bai kamaci mumini ya kashe wani mumini ba sai dai a bisa kuskure. (Surah An-Nisaa’i: 92).

    Shiyasa malamai suka yi saɓani a kan tuban mai wannan laifin, kamar yadda Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

    « كُلُّ ذَنْبٍ عَسَى اللَّهُ أَنْ يَغْفِرَهُ إِلاَّ مَنْ مَاتَ مُشْرِكًا أَوْ مُؤْمِنٌ قَتَلَ مُؤْمِنًا مُتَعَمِّدًا »

    Kowane zunubi ana fatar Allaah ya gafarta masa sai dai wanda ya mutu a halin yana mushiriki, ko muminin da ya kashe wani mumini da gangar. (Abu-Daawud: 4272).

    Hukuncin mai kisan kai da gangar a asali shi ne: Qisas, watau wanda ya yi kisan shi ma a kamo shi a kashe shi, kamar yadda Ubangiji Ta’aala ya ce

     یَـٰۤأَیُّهَا ٱلَّذِینَ ءَامَنُوا۟ كُتِبَ عَلَیۡكُمُ ٱلۡقِصَاصُ فِی ٱلۡقَتۡلَىۖ ٱلۡحُرُّ بِٱلۡحُرِّ وَٱلۡعَبۡدُ بِٱلۡعَبۡدِ وَٱلۡأُنثَىٰ بِٱلۡأُنثَىٰۚ فَمَنۡ عُفِیَ لَهُۥ مِنۡ أَخِیهِ شَیۡءࣱ فَٱتِّبَاعُۢ بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَأَدَاۤءٌ إِلَیۡهِ بِإِحۡسَـٰنࣲۗ ذَ ٰلِكَ تَخۡفِیفࣱ مِّن رَّبِّكُمۡ وَرَحۡمَةࣱۗ فَمَنِ ٱعۡتَدَىٰ بَعۡدَ ذَ ٰلِكَ فَلَهُۥ عَذَابٌ أَلِیمࣱ

    Ya ku waɗanda suka yi Imani! An wajabta muku yin Qisasi a kan kisan kai: Ɗa domin ɗa, kuma bawa domin bawa, kuma mace domin mace. (Surah Al-Baqarah: 178).

    Sharɗɗan zartar da qisas, in ji malamai su ne

    1. Mai kisan ya zama mukallafi. Domin an ɗauke alƙami a kan wanda ba mukallafi ba, kamar yaro ko mahaukaci.

    2. Ya zama da gangar ya yi kisan. In da kuskure ne to babu qisas sai dai diyya kawai.

    3. Ya zama ya kashe wanda bai halatta a kashe shi ba. Amma idan ya kashe ridadde ko mazinacin da ya taɓa aure, ko ɗan fashi ko ɗan tawayen da jininsa ya halatta, a nan babu diyya, babu qisasi.

    4. Kar ya zama wanda ya yi kisan mahaifi ne ga wanda aka kashe. Saboda

    « لاَ يُقْتَلُ بِالْوَلَدِ الْوَالِدُ »

    Ba a kashe uba domin ya kashe ɗa. (Ibn Maajah: 2763).

    5. Ya zama dukkansu musulmi ne. Domin kamar yadda Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya faɗa

    « وَلاَ يُقْتَلُ مُسْلِمٌ بِكَافِرٍ »

    Ba a kashe musulmi domin ya kashe kafiri. (Sahih Al-Bukhaariy: 111)

    6. Haɗuwar waliyyan mamacin a kan qisasin. Domin in aka samu ko da mutum ɗaya bai amince da qisas ba, to ba za a tsayar masa da shi ba.

    7. Wannan shi ne abin da na sani daga bayanan malamai a kan wannan mas’alar. Watau Babu bambanci a tsakanin mace da namiji a nan

    Ana kashe mace don ta kashe namiji, haka kuma ana kashe namiji don ya kashe mace.

    WALLAHU A'ALAM

    Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

    08021117734

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.