ShimfiÉ—a
A babi na tara, an kawo bayanai a kan dafa-duka amma a gargajiyance. Zamani ya zo da sauye-sauye daban-daban a wannan nau’in abinci na dafa-duka. Wasu daga cikin sauye-sauyen sun shafi kayan haÉ—in abincin ne kawai. A nan, ana nufin nau’ukan kayayyakin sarrafa dafa-duka, misali kayan É—anÉ—ano da na Æ™amshi. A É“angare guda kuwa, akwai sababbin nau’o’in dafa duka na zamani da suka zo wa Bahaushe. Ya same su ne daga baÆ™in al’ummu da ya yi cuÉ—anya da su. Wannan babi na ashirin da uku zai bibiyi waÉ—annan nau’o’in abincin na dafa-duka da ke Æ™unshe da tasirin zamani.
Dafa-Dukan Shinkafa da Taliya
i. Albasa
ii. Gishiri
iii. Kayan yaji
iv. Magi
v. Mai
vi. Nama
vii. Ruwa
viii. Shinkafa
ix. Taliya
x. Tarugu
xi. Tattasai
xii. Tumatur
Dafa-dukan shinkafa da taliya ita ma haka za a yi ta kamar wadda ta gabata. Sai dai za a tafasa nama da albasa kafin a saka shi a cikin sanwa. Haka ma, idan za a saka taliya sai an zuba dafaffiyar shinkafa daga baya a saka taliya.
Dafa-Dukan Shinkafa da Ganye
i. Alayyafu
ii. Albasa
iii. Ganda
iv. Gishiri
v. Kayan yaji
vi. Magi
vii. Mai
viii. Ruwa
ix. Shinkafa
x. Tarugu
xi. Tattasai
xii. Tumatur
xiii. Zogale
Wannan dafa-duka ita ma kamar yadda
aka yi ta wake haka za a yi ta. Sai dai a wurin ganda za a
tafasa ta da gishiri da albasa sosai kafin a saka ta bayan an yi sanwa. Shi
kuma zogale za a murje shi sosai a saka cikin sanwa saboda
ya nuna sosai. Daga nan,
sai a saka shinkafa. Idan alayyafu ne,
sai an saka shinkafa sannan a saka alayyafu.
Dafa-Duka Shinkafa da Doya
i. Albasa
ii. Doya
iii. Gishiri
iv. Kayan yaji
v. Kukumba
vi. Magi
vii. Mai
viii. Ruwa
ix. Shinkafa
x. Tarugu
xi. Tattasai
xii. Tumatur
Ita ma dafa-dukan shinkafa da doya
akan yi ta ne kamar sauran da aka yi bayani a sama. Bayan nan, ita ma doyar za a fere ta a ajiye gefe. Sai dai idan za a saka shinkafa tare za a
saka su. Idan ana buƙata za a iya yayyanka kukumba a saka a ciki.
NaÉ—ewa
Dafa-duka abinci ce da ta tara abubuwa da yawa, kamar dai
yadda aka ga bayanin a sama. Akwai wasu nau’o’in dafa-duka da za a iya samu a Æ™asar Hausa bayan waÉ—annan, musamman da yake kullum sababbin ilimomi na Æ™ara zuwa ga al’umma a fannonin rayuwa daban-daban, ciki
har da yadda suke samar da abincinsu na yau-da-kullum.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.