𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Malam musulmi zai iya auren ahlul
kitab tana addininta yana musuluncinsa?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
To dan'uwa Allah madaukaki ya
halatta auren kamammu daga cikin ahlul-kitabi, wato Yahudu ko Nasara, kamar
yadda ya yi bayanin hakan a cikin suratul Ma'ida a aya mai lamba ta: (5)
الْيَوْمَ أُحِلَّ لَكُمُ الطَّيِّبَاتُ ۖ وَطَعَامُ الَّذِينَ
أُوتُوا الْكِتَابَ حِلٌّ لَكُمْ وَطَعَامُكُمْ حِلٌّ لَهُمْ ۖ وَالْمُحْصَنَاتُ مِنَ الْمُؤْمِنَاتِ
وَالْمُحْصَنَاتُ مِنَ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ مِنْ قَبْلِكُمْ إِذَا آتَيْتُمُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ مُحْصِنِينَ غَيْرَ مُسَافِحِينَ وَلَا مُتَّخِذِي أَخْدَانٍ ۗ وَمَنْ يَكْفُرْ
بِالْإِيمَانِ فَقَدْ حَبِطَ عَمَلُهُ وَهُوَ فِي الْآخِرَةِ مِنَ الْخَاسِرِينَ
A yau an halatta muku abũbuwa
mãsu dãɗi kuma
abincin waɗanda aka
bai wa Littãfi halal ne a gare ku, kuma abincinku halal ne a gare su, da mãtã
mãsu kãmun kai daga muminai da mãtã ´yã´ya daga waɗanda aka bai wa Littãfi a gabãninku idan kun
je musu da sadãkõkinsu, kuna mãsu yin aure, ba masu yin zina ba, kuma bã mãsu
riƙon
abõkai ba. Kuma wanda
ya kãfirta da ĩmãni to, lalle ne aikinsa yã ɓãci,
kuma shĩ, a cikin Lãhira, yanã daga mãsu hasãra. (suratul Ma'ida a aya ta 5)
kuma an samu wasu daga cikin
sahabai, sun aure su kamar Usman dan Affan - halifa na uku a musulunci- ya auri
Banasariya, haka Dalhatu dan Ubaidillah ya auri Banasariya, sannan Shi ma
Huzaifa masanin sirrin Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya auri Bayahudiya,
Allah ya kara musu yarda. Duba: Ahkamu-ahlizzimah 2\794.
Saidai malaman wannan zamanin
suna cewa, abin da ya fi shi ne rashin auren Ahlul-kitab a halin yanzu, saboda
yadda zamani ya canza, domin da yawa idan mijinsu musulmi ya mutu yaran suna
zama cirister, kai wani lokacin ko da sakinta ya yi za ta iya guduwa da yaran,
sannan zai yi wuya ka samu kamammu wadanda ba su taba zina ba a cikinsu.
Wasu kasashen kuma idan za ka
auri cirister daga cikinsu dole zai ka yarda da dokokin kasarsu, a lokuta da
yawa kuma za ka samu dokokin sun saɓawa
ka'idojin musulunci.
Allah ne mafi sani.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBqfaiPwf28l
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.