Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Zubar Da Ciki

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Menene hukuncin ma’auratan da suka zubar da cikin da ya kai wata bakwai? Akwai kaffara a kansu?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

A asali bai halatta a dakatar da cigaban rayuwar jaririn da ke cikin ciki ba kome ƙanƙantansa kuwa, sai in akwai wata larura ƙaƙƙarfa. Kamar idan an samu tabbaci ko marinjayin zaton cewa haihuwar za ta saka rayuwar mahaifiyar ko na abin haihuwar ko kuma na su duka a cikin matsanancin hali.

Amma game da iyayen da suka haɗa baki suka kashe jariri a cikin da ya kai watanni huɗu ko fiye, wato a lokacin da ya zama an riga an busa masa rai, to sun yi laifi  a ƙaidar addini. Don haka wajibi ne gare su su tuba ga Allaah Maɗaukakin Sarki a kan wannan ƙazamin laifin da suka aikata, tuba ta gaskiya tare da sharuɗɗanta.

Bayan tuban ko akwai wani abu da shari’a ta ɗora musu? Manyan malamai (Rahimahumul Laah) sun sha bamban a kan haka. Dubi tattaunawa a kan mas’alar a cikin littafin Al-Mausuu’atul Fiqhiyyatul Muyassarah (6/256) na As-Shaikh Husayn Bn Audah Al-Awaayishah (Hafizahul Laah). Amma abin da fatawar Shaikhul-Islaam Ibn Taymiyah (Rahimahul Laah) ta nuna shi ne:

(i) Wajibi ne su bayar da cikakken bawa ko baiwa ko kuma farashinsa na ushurin (1/10) diyya ga sauran dangin wannan jaririn ban da su. Domin a ƙaida wanda ya kashe wani ba kuma zai ci gadonsa ba.

(ii) Ushurin diyya shi ne dinare hamsin idan cikakkiyar diyyar ita ce dinare ɗari biyar (500). Amma idan dinare dubu (1,000) ne kamar yadda hadisin Amr Bn Shu’aib ya nuna, ushurinsa zai zama dinare ɗari ɗaya (100) kenan a yau.

(iii) Sannan kuma a wurin yawancin malamai akwai kaffara a kansu na ’yanta bawa ko baiwa. Idan kuma ba su samu ba sai su yi azummin watanni biyu a jere. Idan kuma ba su iya yi ba sai su ciyar da miskinai guda sittin. (Majmuu’ul Fataawaa: 34/161).

Allaah ya ƙara mana fahimta.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Hukuncin Zubar Da Ciki

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Allah ya kara wa malam lafiya. Dan Allah malam na yi sati 7 ban ga al'ada ta ba, sai na je assibiti yau aka tabbatar min ina da ciki, to ina da yaro ɗan wata 13 ban daɗe da haihuwa ba, kuma na yi ta fama da matsalar rashin jini kafin in haihu, to yanzu ina jin tsoran barin cikin nan in gamu da wata matsalar wurin haihuwa, kuma mijina baya iya ciyar da mu, sai aka ce in ina so za a ba ni magani da zan rabu da shi, to yahalatta in yi haka?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salam. 'yar uwa asalin hukunci dangane da cikin mace shi ne ba ya halasta a zubar da shi a dukkan matakansa har sai idan akwai lallurar da Shari'a ta yarda da ita.

Idan ya kasance cikin yana halin ɗugon maniyyi ne, wato yana cikin kwana arba'in na farko ko qasa da haka, to ya halasta a zubar da shi idan har ya zama zubar da shi akwai wata maslaha ta Shari'a ko ya kasance da nufin kawar da wata cutuwa da aka hararo zai iya faɗa wa matar saboda cikin, to a wannan halin ya halasta a zubar da shi.

Amma tsoron wahalar tarbiyyar yara ba ya shiga cikin wannan halascin, ko rashin ikon ɗaukar nauyayyakinsu, ko nufin qayyade adadin 'ya'ya, da wasu uzurorin da ba na Shari'a ba, duk ba sa shiga qarqashin wannan halascin.

Har-ila-yau, haramun ne a zubar da cikin nan idan har ya qetare kwana arba'in, saboda bayan kwana arba'in sun shuɗe cikin yana zamowa gudan jini ne, kuma shi ne farkon halittar mutum, ba ya halasta a zubar da shi bayan kaiwarsa wannan mataki, har sai idan taron likitoci sun tabbatar da cewa cigaba da zaman wannan ciki haɗari ne ga rayuwar mace, suka ce akwai tsoron kada ta rasa ranta idan cikin nan ya ci gaba da zama tare da ita, to a nan ne ya halasta a zubar da shi.

Duba Fataawal Lajnatid Dá'ima (21/450).

Allah Ta'ala ne mafi sanin daidai.

Jamilu Ibrahim, Zaria.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734

Ga Masu Buqatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi Waɗannan Links...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇 https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8qu9GT

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments