Ticker

6/recent/ticker-posts

Maziyyi Yana Karya Alwala?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum warahmatullah malam ina yi maka fatan alkhairi mal. Tambayata anan itace mutum ne yayi alwala yayi komai sai da yaje masallaci ya tayar da sallah sai maziyyi ya fito masa shin malam mutum zai sallame sallar ne ko zai karasa ta kuma yaya hukuncin sallar tasa idan ya karasa? Allah ya karawa malam lafiya da wadatar zuciya na gode

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikum assalam, ya wajaba ka yanke sallah, ka saké Alwala, an rawaito daga Aliyu (R.A) ya ce: "Na kasance mutum mai yawan maziyyi sai na umarci Mikdad ya tambayar min Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam sai ya ce maşa: Idan ya fito ka sake alwala, ka wanke azzakarinka, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 266" 

Allah ne mafi sani

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfqds

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments