Gaba Da Mutanen Gida

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    As-Salaam Alaikum. Mun komo zama a family house ne sai ya zama ba ma jituwa da wadansu matan gidan har abin ya kai ga a yanzu ba na magana da mata biyar domin ba sa so na da alheri. Na san gaba ba kyau, amma kuma magana da su ma babu alheri, shi ne nake tambaya ko za a kara min haske?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

    Yar uwa daga dukkan alamu matsalar daga gare ki ne, kafin a kalli sauran jama’ar gidan. Domin abu ne mawuyaci mutane biyar duk su haɗu a kan gaba da ke amma a ce ke kanki ba ki da wani laifi. Hausawa sun ce: Hanu ɗaya ba ya yin tafi. Don haka ki binciki al’amarinki, lallai akwai wani abin da kike yi musu ke ma. Domin ai ruwa ba ya tsami banza.

    Amma da yake tun dayake Karin haske kike nema, to ga nasiha dai

     

    Al-Imaam Muslim (Rahimahul Laah) ya riwaito hadisi da isnadinsa sahihi har zuwa ga Sahabi Abu-Hurairah (Radiyal Laahu Anhu), cewa: Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

    « تُفْتَحُ أَبْوَابُ الْجَنَّةِ يَوْمَ الاِثْنَيْنِ وَيَوْمَ الْخَمِيسِ، فَيُغْفَرُ لِكُلِّ عَبْدٍ لاَ يُشْرِكُ بِاللَّهِ شَيْئًا، إِلاَّ رَجُلاً كَانَتْ بَيْنَهُ وَبَيْنَ أَخِيهِ شَحْنَاءُ، فَيُقَالُ أَنْظِرُوا هَذَيْنِ حَتَّى يَصْطَلِحَا، أَنْظِرُوا هَذَيْنِ حَتَّى يَصْطَلِحَا، أَنْظِرُوا هَذَيْنِ حَتَّى يَصْطَلِحَا »

    Ana buɗe ƙofofin Aljannah a kowace ranar Litini da ranar Alhamis, sai kuma a gafarta wa dukkan bawan da ba ya haɗa komai da Allaah. Sai dai mutumin da ya ke akwai gaba a tsakaninsa da ɗan’uwansa. Sai a ce: Ku dakatar da waɗannan biyun har sai sun yi sulhu! Ku dakatar da waɗannan biyun har sai sun yi sulhu!! Ku dakatar da waɗannan biyun har sai sun yi sulhu!!! (Sahih Muslim: 6709).

    Abubuwan Lura

    (1) Haram ne musulmi ya yi gaba har ya ƙaurace wa ɗan’uwansa musulmi, musamman saboda wani dalili daga cikin al’amuran samun abin duniya.

    (2) ’Yar uwa musulma mai imani! Ba kya shirka ko tsafi, ba kya cikin ƙungiyar matsafa masu shan jini, masu taammali da bokaye. To, ta yaya za ki bari wannan garaɓasa ya riƙa wuce ki a kowane mako?

    (3) Domin wata mace ta yi miki wulaƙanci, ko ta zage ki, ko kun yi sa-in-sa da ita, sai ki bari hakan ya janyo miki wannan mummunar asarar?

    (4) Kina ji kina gani a kowane mako Allaah Maɗaukakin Sarki ya gafarta wa kowane musulmi har sau biyu, amma ke ban da ke?! 

    (5) Kai! Ko dambe kuka yi, kuka yi jina-jina da ita kya bari hakan ya kai ga rasa wannan gafarar mai matuƙar muhimmanci da girma a wurin kowane musulmi?!

    (6) Yanzu idan a cikin hakan ajalinki na rayuwa ya cika a tsakanin ranar Litinin zuwa ranar Alhamis, ko a tsakanin ranar Alhamis zuwa ranar Litinin ɗin fa, yaya kenan? Me za ki ce?!

    (7) ’Yar uwa! In tambaye ki mana: Yanzu idan kika yi dambe da wata kafira arniya, kuma har ya kai ga ta keta miki rigar mutunci a idon jama’a, kuma kafin ki rama sai aka shiga tsakani, aka raba ku.

    (8) Washegari kika yi sammako da ƙaƙƙarfar niyya ta ɗaukar fansa, amma kuma sai kawai aka ce miki ai tun jiya bayan kun rabu ta musulunta. Kuma ma har tana neman ki ku sasanta.

    (9) Tambaya a nan: Don Allaah! Za ki cigaba da wannan shirin da niyyar ta ɗaukar fansa a kanta, ko kuwa ba za ki cigaba ba? Kawo amsa ta gaskiya tsakaninki da Allaah.

    (10) Idan kika ce: Sam! Babu sasantawa, ba za ki yafe mata ba. Dole sai kin yi ramuwar gayya a kan ta kawai! To, ina cikar imaninki da musulunci kenan?!

    (11) Idan kuwa kika ce: Tabbas! Za ki manta da abin da ya wakana a tsakaninku, za ki je ki haɗu da ita ku yi musafaha cikin ƙauna da soyayya, wannan shi ne abin da ya kamaci dukkan musulmi mai imani.

    (12) To amma idan har za ki iya yin wannan ga wannan sabuwar musulunta, me ya sa ba ki iya yin hakan ga wacce kika san ta yi shekaru a matsayin ’yar uwarki musulma a cikin addinin ba? Me ya sa?!

    (13) Don haka idan dai har za ki iya daidaitawa da wacce ta musulunta a yau, to babu dalilin cigaba da zaman gaba da wata mace musulma da ta daɗe a cikin musulunci.

    (14) Tun da dai har dabbobi ma Allaah Maɗaukakin Sarki zai yi musu hisabi a Lahira, to ina kuma ga waɗanda suka musulma da kika cutar da ita da wani aiki ko wata kalma a tsawon zamanki da ita?

    (15) A ƙarshe: Idan har ba ki iya yin haƙurin zama da mutanen da kuke da mabambantan raayoyi da su ba, to da wanene kike jin za ki iya zama? Tumaki da akwaki, ko kuwa kyankyasai da beraye?

    Allaah ya kiyaye. Allaah ya shiryar da mu.

    WALLAHU A'ALAM

    Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafi

    Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.