Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Ya Hallatta Mace Tayi Aikin Gwamnati?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Malam na ji wasu suna haramta aikin gwamnati ga mata, menene gaskiyar magana akan haka?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salam

To 'yar'uwa Allah Madaukakin sarki a cikin suratul Ahzaab ya umarci mace da ta zauna a gidanta, kar ta dinga yawan fita.

Malamai suna cewa bai halatta mace ta yi aiki a wajan gidanta sai da sharuda guda biyu

1. Aminta daga cakuduwa da maza, kasancewar mace tana da rauni, Kafada-da-kafada da maza yana iya kaita zuwa ga lalacewar tarbiyya.

2. Bukata zuwa ga aikin, kamar ya zama ta fito daga dangi matalauta ko kuma mijinta ya mutu tana bukatar abin da za ta tafiyar da bukatun marayunta, ko ya zama aikin likitanci ne a bangaren lalurorin mata.

Kissar Annabi Musa a cikin suratul Kasas lokacin ta ya je Madyana ta yi nuni zuwa ga sharudan da suka ygabata.

Idan ya zama dole sai mace musulma ta yi aikin gwamnati ya wajaba ta kula da abubuwa biyu

1. Sanya sutura mai rufe dukkan jiki.

2.Takaita magana da maza sai gwargwadon bukata.

Da yawa daga cikin matan da suke aikin gwamnati suna tozarta tarbiyyar yaransu, wasu kuma suna butsarewa mazajansu, saboda idonsu ya buɗe ta hanyar hira da abokan aiki.

Mutukar miji zai iya daukewa matarsa dukkan bukatunta na dole, to zamanta a gida ta kula da iyalanta da mijinta shi ne daidai, kamar yadda Allah ya umarce ku da hakan a aya ta (33) a suratul Ahzab.

وَقَرْنَ فِىْ بُيُوْتِكُنَّ وَلَا تَبَـرَّجْنَ تَبَرُّجَ الْجَاهِلِيَّةِ الْاُوْلٰى

Kuma ku tabbata a cikin gidãjenku, kuma kada ku yi fitar gãye-gãye irin fitar gãye-gãye ta jãhiliyyar farko.

Allah ne mafi sani

Dr. Jamilu Zarewa

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments