Ticker

6/recent/ticker-posts

Kosan Rogo

Kosan Rogo

Fitattun Kayan Haɗi

Kosan rogo

Ingredients
1- Garin rogo (alabo)
2- Albasa
3- gishiri
4- ruwa
5- magi
6- tattasai+Attarugu

Lura: Waɗannan fitattu ne kawai daga cikin kayan haɗin. Ana iya samun sauye-sauye (daɗi ko ragi), wanda hakan ya danganta ga salo da ra'ayin mai girki.


Za a niqa rogo a tankaɗe (garin alabo ke nan) sannan a kwaɓa da ruwan dumi (kwabin a yi mai kauri yadda za a iya mulmula shi) sai a saka gishiri daidai da magi, a jajjaga attarugu da tattasai da albasa a saka a ciki a dama sosai. Sai a dinga gutsura ana mulmula shi mai faɗi kamar kosai ana soyawa. Ana ci da yaji.

A ci daɗi lafiya.

Daga:

Ummu Amatulqahhar Kitchen 
(Humaira'u)

Post a Comment

0 Comments