Fitattun Kayan Haɗi
* Taliya
* Dankali
* Kayan Miya
* Man Gyaɗa
* Albasa
* Kayan Ɗanɗano
* Kayan Ƙamshi
* Ganyen Albasa
Lura: Waɗannan fitattu ne kawai daga cikin kayan haɗin. Ana iya samun sauye-sauye (daɗi ko ragi), wanda hakan ya danganta ga salo da ra'ayin mai girki.
Yadda ake yi
Da farko za ki ɗora tukunyarki a kan wuta, ki saka manja ko mangyaɗa duk wanda kike so, sai ki saka cittanki da tafarnuwa da albasar da kika yanka daidai. bayan ya fara ƙamshi sai ki saka ruwa daidai yadda zai dafa miki abincin, ki saka su maginki da gishiri da kayan kamshinki, ki rufe ki barshi ya dahu sosai ruwan, sai ki bude ki zuba dankalinki da taliya da jajjagen tattasai da attarugu (in kina so za ki iya saka kayan miyan tin a farko, amma za su dahu sosai hakan sun fi daɗi gaskiya). ki gauraya taliyar kar ta haɗe, sai ki rufe ki barshi ya dahu, in zai yi minti bakwai ne, to tin yana minti shida sai ki buɗe ki saka ganyen albasa da kika yanka da albasa da tattasai da kika yanka su, sai ki rufe su dahu tare shikenan.
A ci daɗi lafiya.
Daga:
Ummu Amatulqahhar Kitchen
(Humaira'u)
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.