Ticker

6/recent/ticker-posts

Doya Da Miyar Kwai

 

Doya Da Miyar Kwai

Doya Da Miyar Kwai

Doya Da Miyar Kwai

Fitattun Kayan Haɗi

* Doya

* Kayan Miya

* Man Gyaɗa

* Albasa

* Kayan Ɗanɗano

* Kwai

* Thyme

* Curry

* Ginger And Garlic

* Ganyen Albasa

Lura: Waɗannan fitattu ne kawai daga cikin kayan haɗin. Ana iya samun sauye-sauye (daɗi ko ragi), wanda hakan ya danganta ga salo da ra'ayin mai girki.

1- Za ki fere doyarki ki yanka ki wanke ki dafa ta da gishiri daidai ta dahu dahuwa mai kyau kar ta faffashe sai ki ajiye a gefe.

2- ki ɗora tukunya a kan wuta ki saka manja/mangyaɗa, ki saka ginger and garlic da albasa har sai sun fara kamshi, ki kawo jajjagen tattasai da albasa da attarugu ki saka,ki saka magi daidai ba da yawa ba da thyme da curry, ki saka gishiri ɗan kaɗan. ki gauraya ki rufe su soyu, sai ki kawo ƙwai da kika fasa ki zuba a ciki ki rufe sai ya dahu sai ki gauraya shi sosai ya kama ko ina, ki saka ganyen albasa daidai ya yi laushi daidai shikenan.

A ci daɗi lafiya.

Daga:

Ummu Amatulqahhar Kitchen 
(Humaira'u)

Post a Comment

0 Comments